💖💫RUDANI💖💫 82

56 24 79
                                    


Fita yayi dan amsa kiran, shi ya rasa mey ke damun Teemerh "Ke Teemerh bakida hankali ne zaki kirani da sassafen safiya?" Ya fara mata bala'i "Kayi haquri Ahmad, na kirane naji ya Ilhaam take" sake duba wayan yayi yaga eh dagaske Teemerh ne kawae yayi wani venomous smile "Teemerh kar ki bani dariya mana. Ilhaam ne kikeso kiji ya take?" Ya sake tambaya dan tabbatar da abunda kunnen sa yaji "Bana kira danna tausaya mata bane, so nakeyi na rokeka" dan shiru yayi, jin tayi shiru itama yace "Ki fada ina jinki" tace "Banaso Ilhaam ta dawo, saboda dawowanta ba alkhairi ah ciki, inda hali ka aureta kafin ka dawo da ita, Anwaar is not concentrating kan komai fa" dan murmushi yayi kafin yace "Ki kwantar da hankalin ki Teemerh, Ilhaam zata dawo amma sai bayan ta aureni yanda ba wanda zai kwace ta daga gareni, har Anwaar" wani farin ciki taji mara misaltuwa, finally Ilhaam is leaving her life forever, fatan ta Anwaar ya dawo gareta itama "Nagode Ahmad ni zan kashe" yace "Wait, sun san yanda nake kuwa?" Teemerh tace "Aa I don't think so, amma Aameer yace dole zaka karbi hukunci mey tsanani" dariya ya fara dan yasan kafin ya karbin hukunci Ilhaam sai ta fara karba musu nasu "Zan tabbatar na ba Aameer mamaki Teemerh, and how has your husband been?" Ya tambaya dan ya fara farin ciki da rushewan Anwaar "I can't read his mind, amma bayi fita aiki, kullum yana tare dasu Aameer, I've given him a new name, Barrister Anwaar" he can hear the bitterness in her tone saying this, Anwaar is blindly in love with this Ilhaam, amma da yardan Allah ya rasa ta har abada kenan

ABUJA

"TOH Maa Laure ta fada mana in detail yanda abun ya faru koh? Aliyu bani iya bacci tun b'ace wan yarinyan nan" Maāmaa ta fada a dame, gashi bata iya damuwa ba dan har Maiduguri ta kira ta fadawa Mummy koh zataji sassauci, ita har blaming kanta take, data barta ta zauna gidan da akwae securities da hakan hala bai faru ba, amma haka Allah yasa "Bayani a fili yake Maāmaa, Ahmad ne ya sace ta, the guy you trust a few days ago" Yesmin tasa baki "Keep your mouth shut Yesmin and let your elders speak" Aliyu ya mata warning, shiru tayi bata sake cewan komai ba "Toh ae ni Ahmad ya cuceni, dan yazo rimi-rimi yasa na dauki yarda na basa ashe ya kasa dauketa chan gidan saboda securities shiyasa yayi hakan dan ta dawo nan ya dauketa" Yaa Abu yace "Mey Ahmad yace Maāmaa?" Har zata fara bayani Anwaar ya tsareta "Yaa Abu yanzu ba wannan ne abunda ya dace ayi a wannan lokacin ba, kamata yayi muyi focusing wajen nemo Ilhaam" Anwaar ya kawo wani topic "Toh wai ni how on earth ace policemen sun kasa nemo Ahmad?" Aameen ya tambayi Aameer "Abunda na gani kenan, gabadaya basu san abunda sukeyi ba, da zaran an nemo sa, I will make sure I sue him to court" ya fada and the factness in his voice is clear "No you guys wait, Ahmad ba abokin ku bane?" Mahfouz ya tambaya "Yea he was" suka amsa in chorus, Aameer making the was clear and audible "Ya kamata ace kunsan wani hide point nasa hakan zai taimaka sosai" duk shiru sukayi suna dan tunanin kafin sukace "Borno" Aameen da Aameer suka sake amsawa in chorus "Maiduguri?" Aliyu ya tambaya yana mamaki "Eh I remember when we were in school when he told me akwae hide point nasa a Maiduguri but bansan wajen ba" Aameen ya amsa "Yanzu zamu koma police station din muji ya ake ciki koh Mahfouz?" Farouq ya tambayi Mahfouz, kallon sa Mahfouz yayi ganin yana maganan amma bayi kallon kowa cikin su sai waya, toh ba dole idon mutum yayi ciwo ba "Eh sai muje daga nan kuma ya kamata mu wuce Maiduguri ayi filling case chan ma koh Allah zaisa a dace", "Basai kun d'aga hankali ba, Najeeb is in Maiduguri kuma recently akayi promoting nasa zuwa DCP (Deputy Comissioner of Police) kunga komai zai zo da sauki, da kam fa yau zasu shigo amma sai nace su daga" Maāmaa ta musu bayani, Billy suppose to do some events in her wedding amma saboda wannan abun daurin aure kawae akayi, ita Maāmaa tashin hankali ma koh tara jama'a batayi ba "Ya kamata koh zasu zo shi ya haqura, we will need him there, Ahmad must be cunning to set such trap" Aameer ya fada yana girgiza kai, Allah ne kadai yasan irin hukuncin da zai yima Ahmad bayan an kamo sa "Zamuje Maiduguri, Yaa sai ku kula danan" Anwaar yayi maganan ah hankali, kansa yana ciwo sosai dan shima koh bacci bai iyawa "Zanje" Yesmin tayi saurin amsawa "Da izinin wa?" Maāmaa ta tambaya hakan yasa tayi shiru, ita mantawa takeyi fa, shiru tayi ta tashi zuwa wajen su Xeenerh, shima Anwaar tashi yayi ya bita, gani yake kaman in yaje wajen su zai ga Ilhaam, shi dama zai ganta koh zaiyi magana bazata amsa ba mana "Yaa Anwaar please be brave, Ilhaam will be back home safe and sound In Shaa Allah" Xeenerh ta fada ganin ya shigo yayi shiru, yakai 2 hours zaune wajen baiyi musu magana ba, daga yayi waya da wannan sai yayi da wannan har su Aameer suka masa sallama Aameer ya tafi aiki "Xeenerh bana tunanin zan yafewa kaina idan har wani abu ya samu Ilhaam" ya fada dan ya dauki blame in "Yaa Anwaar ina mey tabbatar maka Allah zai kareta, ka kwantar da hankalin ka-" bata gama rufe baki ba taga Aameer ya dawo, samun waje yayi ya zauna kawae yayi shiru, he is in a great dilemma "Aameer what's wrong?" Xeenerh tabar magana wa Anwaar ta koma wajen Aameer ganin yanayin sa, shima Anwaar karasowa yayi jin miye "Why do things seem to be so complicated?" Ya tambaya kaman sun sani "Aameer kayi haquri Ilhaam zata dawo da yardan Allah" Xeenerh ta fada dan duk tunaninta Ilhaam ne, batasan wannan yayi x5 na Ilhaam in sunji ba "I pray so Xeenerh, amma can you imagine yau Lami (housemaid na Mami) tayi magana?" Girgiza kai Xeenerh ta fara ganin how funny Aameer sound, toh ae abun farin ciki ne "Finally ta revealing komai kenan, Barrister right?" Anwaar ya tambaya, dakai ya amsa kawae "Then why the tears?" Xeenerh ta tambaya "Aameer bazai taba iya magana ba Xeenerh saboda answer da Maa Lami ta bayar yayi tsauri sosai" Ashphert ta fada tana kuka "Ta fadi wanda tasa tayiwa Mami abunda tayi?" Anwaar ya tambaya sounding curious "Guys abar maganan nan, saboda yana bukatan bincike mey kyau" Aameen ya dakatar da Ashphert "No please, can you make this drama short?" Xeenerh tace ga Ashphert "Anwaar I can't believe cewa wanda ta haifeni itace behind all this pain" Ashphert ta sanar musu "Ashphert can you amplify it? Dan ban gane mey kike cewa ba" Anwaar ya sanar da Ashphert "In short, matar da ka dauka matsayin uwa wato Ummi itace ta bada umarnin a sawa Mami poison-" Ae bata rufe baki ba Anwaar ya dauketa da mari to avoid the nonsense coming out of her mouth, da badan cikinta ya girma ba da confirm ya zube, da sauri Xeenerh ta mike tare da rufe kunne dan kunne ta baza su iya dauka ba, Yesmin na gefe tana girgiza kai kaman dai bataji da kyau ba, Al'ameen dake kusa da Ashphert ne yayi saurin tare ta "Kana ganin condition nata still ka daketa?" Ya tambaya yanaso Anwaar ya koma cikin hankalin sa, suma duk ba yarda sukayi ba amma shi sam Ummi bata laifi wajensa, the best gift Allah gave Ummi is Anwaar "Abunda ya kamata tayi tunani kenan, baka jin irin maganan batanci da Ashphert takeyi akan Ummi?" Ya tambaya hanun sa cikin kansa "Anwaar koh kaki koh kaso that's the truth, ya kamata ka gane cewa Ummi ba mutuniyar kirki bace ba" Ashphert ta maimaita, wani gigitaccen tsawa Aameer ya daka mata hakan yasata yin shiru "Isn't Ummi our Mother? Koh kin fara shan wani abu ne da yake juya miki tunani. Get out of my side" Aameer ya sanar da ita "Ba yanda zanje Aameer, magana akeyi akan wanda ta haifeni, I've every single right to be among" tana fada ta zauna ma dan ta tabbatar masa ba yanda zata "Doctor, Lami is damn serious about what she's saying, tace dalilin da yasa tun farko taqi magana kenan" Aameen yayi interjecting "How can I disagree to this?" Xeenerh ta tambaya "Halin Ummi gabadaya ya chanza ah shekarun nan, ba itace muka sani ah da ba. Amma still my heart is telling me otherwise, my heart is still telling me Ummi bazata aikata hakan ba, beside mey Mami ta tsare mata? Karyane kawaeeee" Xeenerh ta fada kukanta na kara tsananta "Wai dagaske Lami ne tace hakan?" Anwaar ya kara tambaya dan ya tabbatar wa kunnensa, saboda shi duk ya dauka maganan Ashphert ne saboda yanda bata son Ummi a ranta yanzu "Haka ta fada, yanzu ko zamuyi kokarin rufe case court ba yarda zasuyi ba, saboda sun aika takardan" Hanu Anwaar ya sake sawa cikin kansa ya baza gashin, ya yarda Ummi tayi abubuwa da yawa ciki kuwa harda raba sa da Ilhaam, amma to kill somebody? Ummi can never do that "I hope peace will reign in the house" Aameen ya fada sannan ya wuce "It has to be regained first" Ashphert ta fada sannan ta bisa "Anwaar calm down, komai zai zo da sauki, nasan ta dawo 2days ago and currently sick dansu Mlm Abdallah sun fara mata maganin, but don't worry komai zai zo da sauki tunda Maa Sahla na wajen. Yanzu mu fara shirin zuwa Borno koh?" Aameer ya tambayesa, dakai ya amsa kafin suka fita, leaving Xeenerh and Yesmin, haquri Yesmin taba Xeenerh kafin ta kira Rafeeq yazo ya dauketa dan ita in abubuwa sun faru bawani karfi takeji ba, ba driving in da zata iya.
*^*


💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now