💖💫RUDANI💖💫 8

286 56 18
                                    



FLASH BACK, SOME YEARS AGO.

___JUSTICE MUHAMMADU ALBAAZ shine cikekken sunan Baa, cikekken dan Maiduguri neh amma aiki Abuja ya kaishi wanda anan suke rayuwarsu, Allah ya mishi tarin dukiya kaman ba gobe, bayan yayi retire ne ya joining politics wanda Allah ya bashi sa'a wajen cimma burinshi, ya rike makamai da yawa a siyasa wanda ya bawa arzikinshi daman kara habaka, Allah ya azurtashi da mata kwalli daya wanda akafi sani da HAJIA RAKIYYA, yanada yara guda uku Babban danshi shine ALHAJI ABDULLAH ALBAAZ na biyu kuwa sunanshi ALHAJI ISMA'IL ALBAAZ wanda na uku sunanshi ALHAJI YUSUF ALBAAZ, dukkan nin su basu damu da shiga siyasa irin na mahaifisu ba business nasu suka sa a gaba wanda in za'a irga masu kudi a kasan namu sunan ne list in farko, daga bayane Baa yaja ra'ayin Alhaji Isma'il zuwa siyasa, saboda hadin kai da suke ma junansu da suka tashi yin gida sai sukayi compound kowa da side nashi wanda mahaifinsu da matarshi kuma gidansu daman,

Alhaji Abdullah Albaaz yanada Mata daya (Hajia Hafsat, Mami) da yara guda uku Mahfouz, Humainah, da Aameer

Alhaji Isma'il yanada Mata daya (Hajia Nadia, Aunty) da yara guda uku Aliyu(Abutturab), Sabeerah da Al'ameen(Aameen)

Alhaji Yusuf yanada Mata daya( Hajia Hajarah, Ummi) da yara uku shima Omar(Farouq), Ateekah, da Anwaar

(Just by seeing how these characters are set of three, 3 people will convince you more that this is a fictional story😂) so enjoy please, Xo 😘

Haka a kullum suke rayuwansu cikin farin ciki, sam basu nuna ma yaransu banbanci shiyasa in ka gansu baza'a ka gane waya haifi wani ba a cikin su, sun zaci baza su sake haihuwa ba saboda Aameer, Anwaar da Aameen sunada 7yrs kenan sai kwatsam Allah ya azurta Hajia Hajarah Ummi, da yarinya mai kyau wato Ashphert, tayi murna sosai wanda ada ta zaci namiji zata haifa sai Allah ya cika mata burin ta na samun diya mace, Hajia Hafsat itama mace ta samu wato Zeenert aww su Aameer anyi qanwa, sai Hajia Nadia da Ilhaam, kusan tare tare aka haifesu, domin Xeenerh aka fara haifa wanda tanada kwana biyu a dunia aka haifi Ashphert, Hajia Nadia itace ta haifi Ilhaam karshe wanda su Ashphert sunada sati biyu a dunia aka haifeta, come see that level of happiness daga family'n Albaaz, ana dawowa daga asibiti akazo ganin Baby Anwaar yana ganinta yace "Ohh Aunty she's cute I love her" Sabeerah ce ta kwashe da dariya tace "Kuji bakin Anwaar kaman he loves her in nan" Ateekah ma darian tayi banda Humainah dake danna waya, Aunty tace "Don't worry my son the baby is yours" Smiling yayi yana shafa kan Ilhaam, shidai sunada Ashphert a gidansu amma shi Ilhaam ta fi mishi kyaune fa, Aameer ne ya shigo sanye da uniform da gani na Haddah ne yazo ya shafa kan Ilhaam, ae koh Ilhaam kaman tasan abunda akeyi harda smiling "Aunty she just smiled" ya fada very excited "Ohh yes she does" Humainah dake danna wayane ta dago kai da kalli Anwaar dako shirin canza kaya zuwa na Haddah baiyi ba "Aww lalle Anwaar inna tashi I will beat you blue black kake cewa koh?"
"What have I done wrong Yaa Humainah?"
"Kasa uniform driver zai saukeni gidansu Mariam kusa da schl naku, ina Aameen yake?"
"Yana daki" cewar Sabeerah, kafin ta gama rufe baki sai gashi ya fito da uniform yana cuna baki da aka tambayeshi dalili kuwa wai yanzu Aunty zata bar sanshi zata koma san baby shi koh daukan tama bazai yiba, dariya sukayi sosai banda Anwaar da yace shi bazaije schl ba zai zauna da baby ne, Ateekah da kyar ta kaishi part nasu ta shiryashi tace in ya dawo baby na nan ba inda zataje.

A hanyan dawowan Alhaji Abdallah, Alhaji Isma'il da Alhaji Yusuf da kuma mahaifiyarsu Hajiya Rakiyyah daga Umrah ne kasancewar anyi suna basu nan, anan ne aka samu plane crash suka rasu, bayan shekara biyu kuma Allah ya dauki Hajia Nadia mahaifiyarsu Ilhaam inda Ilhaam ta koma wajen Ummi, Aameen wajen Mami, shiyasa Yaa Abu yake matukar san Ilhaam, na farko batasan dadin mahaifi ba ga na biyu kuma a kankanin shekaru data fi bukar mahaifiyarta sai Allah ya dauketa, Anwaar ma duk da rashin magana irin nashi yana kula Ilhaam sosai, suyi fada suyi dadi.

( Dear Readers I'm a lazy writer, dan Allah kuyi hakuri in kunga ina summarizing wani abun, I know some people might be thinking cewa ina sa yawan rasuwa yayi yawa so I've to, duk da haka kuna ga characters in sunada yawa and kowa da kuka gani akwae main role nashi da yake playing, so cooperate) Thanks 💖

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now