💖💫RUDANI💖💫 28

172 32 21
                                    





9:31 pm sai ga Aameer yazo, dakin Ilhaam direct ya wuce, ya bude kofa ya shiga abunsa, bata ciki, hakan yasa yayi tunanin tana bathroom ya zauna jiranta. Fitowa tayi towel daure akanta da alamu wanke kai tayi, ta d'an razana ganin mutum har zata koma saita ga Aameer ne, rike kirji tayi ta koma gefe tana maida numfashi "Aameer sau nawa zance kana yimun sallama?" Tayi maganan tana b'ata rai "C'mon Babe ke kinada matsala, and by the way wanke kai cikin dare lafiya koh?" Ya tambaya harda yamutsa fuska "Bazan iya bacci ba in ban wanke ba" ta bashi amsa "Kije beauty salon su wanke miki mana, gashi ne ma yafiye yawa kaman na aljanu" ya fada yana mey cigaba da yamutsa fuska "Toh ae aljanan ce" Tayi maganan trying to make a ghost face, dariya ma ta basa "Ke koh, yawwa zuwa nayi na nuna miki abu yanzu na wuce abuna kinga dare ya fara" tace "Menene?" Ta tambaya tana drying kanta "Wait" ya fad'a, tsayawan kuwa tayi ya karaso ya karbi dryer ya fara drying mata gashin "Kai ka iyane?" Mamaki duk ya kamata "See you, Ashphert takance na mata sometimes tun ban iya ba yanzu harna iya" tace "Aww see love gashi ta taimakeni yau ae" sai kuma ta fara dariya jin yanda yayi maganan "Naga dama dai, yanzu saina bar miki abunki "No sorry" ta fada tana dariya, kallonsa tayi ta vanity sai tunawa tayi the very first time Aameer said he loves her, saurin daina tunanin tayi, shi kuwa drying mata kan yayi tsaf harda sa ribbons "Toh wancan abincin na waye Ilhaam?"..."Kanaso kaci ne?" Itama ta tambayesa "No kinaso inna koma gida muyi fad'a da Ashphert kenan innace banijin yunwa" Ilhaam tace "Wai ban isa na hada fada ba kuwa" yace "Da ya fi miki kam" yayi maganan da dariya "So baki fada mun na waye ba?..."Nawane banci bane" ta bashi amsa "Dama ance mun baki cin abinci yanzu"..."Munnirah koh? Toh ni ae banijin yunwa ne shiyasa"..."Toh ni kuma in bakici abinci ba yau bazan tafi ba"..."So kakeyi Ashphert ta fito cikin dare kenan" Dariya sukayi ah tare kuma "Yawwa barinyi abunda ya kawoni" waya ya ciro ya nuna mata motoci, ya nuna mata wanda Ashphert ta zaba "In saya miki irin na Ashphert in? Koh baki san irin nata?" ya tambayeta dan yasan tsaf Ilhaam ba lalle abun ya burgeta ba, batason abun irin na kowa "In sunji lbr zasuyi fada fa koh ka manta sun kwace nawa?"..."Toh yanzu Ilhaam ah ina zasuji labari? Saidai ke zaki fada musu kuma, koh baki san irin nata?" Ya sake tambaya dan kara tabbatar wa "No irin natan ma yayi Aameer, AMG ce fa" yace "You sure?"..."Eh 100% kuwa" abincin yasata taci saida ya tabbatar ta koshi kafin ya tafi.

***
Washegari Sameerah tazo, sannan sabowan motan ta ta iso, ana kawowa ta karbi key tayi Fashion Parlor, daga nan tayi gidan Xeenerh suka sha tadi bata dawo gida ba sai bayan isha, tana shiga d'aki daga mutum ah zaune na kallon ball, koh ba'a fada ba tasan waye saboda kamshin turaren sa, daurewa tayi ta karasa, jin shigowan mutum yasa Anwaar jiyowa, tana ganin shine ta saki ajiyan zuciya saidai yaushe ya dawo? Har zata gaishe sa saita tuna abunda Ahmad ya fada mata "Anwaar zai tura gidansu Teemerh" kawae tasa kai ta wuce "Wait!" Ya tsaida ita "Zo!" Ba musu ta koma wajenshi "Ba mutum kika gani bako?" Ya fada yana wani bata rai "Statue na gani tunda danayi sallama ba'a amsa ba" ta fada kasa-kasa yanda ita kadai zataji, saidai ya jita "Ilhaam when on earth zaki bar masifa?" Tsaya wa tayi tana kallonshi dan batasan yaji abunda ta fada ba, shima kare wa cuteness nata kallo yakeyi chan tayi pouting mouth ta bubbuga kafa ta wuce abunta, girgiza kai kawae yayi, bayan ya gama kallon shi ya tashi ya yabar side in saboda bayiso ya kwana ah main house daga shi sai Ilhaam, Ilhaam tunda ta shiga bata fito ba, da asuba tana tashi tayi sallah ta sake maida bacci, ba ita ta fito ba saida gari ya waye, brush kawae ta tashi tayi koh sleeping dress nata bata cire ba ta sauko kasa, ta gama mantawa da Anwaar ya dawo saida ta ganshi ah kan dinning yana breakfast, kaman zata koma sai kuma ta sauko tayi kitchen, tambayan Munnirah tayi abincin ta nan tace ae shi ta bawa Anwaar ganin bata tashi ba, wani kallon banza ta bita dashi sannan ta fita "Kyaji da masifanki dai" Munnirah ta fada bayan da Ilhaam tabar kitchen in, tana fitowa saiga Teemerh "Hi Ilhaam" sai anan ya juya dan ganin waye, yana ganin Teemerh ya juya ya kalli Ilhaam, dauke kai tayi kaman batasan abunda ke faruwa ba "Morning Anwaar jiya bansamu nazo ba shine nace bari nazo yau" tayi maganin tana k'arasawa wajensa "You're welcome" kadai yace da ita "Ilhaam bakiga nazo bane koh sannu da zuwa?" Wai fa duk ganin Anwaar wajen taje wannan rawan kan "Oh Teemerh ashe kece, ni sai ji nayi kaman nasan muryan ashe dai ke in ce" tayi maganan kaman wanda kace dole saita amsa Teemerh "Yes, Ilhaam ya gida?"..."Lafiya" kadai tace ta haura sama "Anwaar bata mun magana bafa" ta fad'a tana kallon sa "Nima batamun ba" ya bata amsa ya takaici, wani dad'i Teemerh taji jin wai basuyi magana ba "Amma Babe can you speak that Shuwa language?" Kallonta yayi jin tambayan nata bayi kan hanya, ita sai ana zaune ta fara dauko tad'in shirme, dan shiru tayi dan batayi tsammanin amsa ba ganin kallon daya mata "Na iya, koh kin manta Ummi is also Shuwa?" Ya tambaya ba tare da ya kalleta ba "No ban manta ba, amma naga you hardly speak Kanuri ma balle Shuwa" ta fada tana murmushi jin ya fara amsata, ita yanzu batada wani damuwa daya wuce Anwaar ya yarda zai aureta, tasan in ya aureta to zai iya rabuwa da kowa amma banda ita "Ke Fatima kinada surutu, yanzu da muke magana da Hausa baki fahimta ne?" Tabe baki tayi "Amma for the future generation fa?" Dan murmushi yayi gano abunda take nufi, hakan ya kara fitar da kyan da Allah ya masa, tsaya admiring nasa kawae tayi itama tana murmushi, yau Anwaar ne ke zaune tare da ita, kuma tayi magana har yayi murmushi "I so much love kids Fatima" ya fada still da murmushi, yanzu kam ta gama gane dalilin farin cikin sa dan kuwa tayi maganan coming generation ne "You will be the best father In Shaa Allah" ta fad'a da same expression dan kuwa bataso moment in ya wuce "Im going" ya fada sannan ya tashi hakan ya dawo da ita daga duniyan tunanin data tafi, kai kawae ta iya gyad'awa sannan ya wuce, tunanin rayuwanta kawae ta fara, bata fiye san haihuwa da wurin nan ba, ita fa haihuwan bey ma wani dameta ba dan kuwa batasan wahala saidai kullum ayi wanka a fita, amma yanzu ta gane Anwaar yana san yara kuma zata iya komai saboda shi, murmushi dake fuskanta ne fad'ad'a "I will give birth to your kids" ta fada ah fili sannan ta mike, kitchen ta karasa, Munnirah bata ciki sai tayi dakinta, rike da waya ta sameta kaman tana waya, tana ganinta ta kashe ta mike da sauri tana wage baki "Ke naketa kira ae Teemerh ashe kina hanya" hanu Teemerh  tasa ah cikin Celine bag nata ta ciro wayan taga more than 10 missed calls na Munnirah "Ke bakida hankali ina? Kiga kiran da kika dinga mun kaman mahaukaciya? Toh ah silent yake shikenan? Any progress? Anwaar sunyi magana da Ilhaam?" Ta sake tambaya dan tabbatar wa "Aa jiya dai bai kwana ah cikin gidan ba sai Yaa Aameer yana yawan zuwa" ta bata amsa "Good ki cigaba da samun ido" Nan ta juya zata fita Munnirah ta tsaidata ta hanyan kiran sunanta "Teemerh" Juyowa tayi cike da rawan kai "Miye kuma?" Sai kuma ta wani b'ata rai "Akwae labarin da yafi koh wanne muni" Munni ta fad'a mata gaskia, k'ankance manyan idon ta fara tanaso tayi masifa, daurewa tayi dai ba tayi ba ta karasa wajen Munnirah "Toh jira kike sai nace ki fad'a kafin ki fad'a mun?" Tayi maganan cikin masifa, Munnirah batace komai ba, kaman bazatayi magana ba tace "Ummi ta had'a auren Yaa Anwaar da Ilhaam" tayi maganan so calm, but to her surprise Teemerh na tsaye kaman bata jiba "Teemerh kinji abunda na fad'a kuwa?" Ta tambaya dan tabbatar wa, tsaki Teemerh tayi "Mey kikeso nayi? So kike nayi ihu da hauka saboda Ilhaam tayi nasara akaina? Koh so kikeyi nayi murna, rawa da tsalle saboda taya Ilhaam murnan samun nasara?" Shiru Munnirah tayi tana kallonta hakan yasa Teemerh kwashewa da dariya, tsayawa kallonta akwae Munnirah tayi, tasan dama Teemerh batada hankali, bata tabbatar ba sai yau "Ki zuba ido" abunda Teemerh tace kenan, Munnirah kuwa zuba idon tayi tana kallonta "Ki zuba ido Munnirah, ran daurin aure zai zo, zaki gani, nima zan gani, amma ah maimakon Ilhaam, da Teemerh za'a daura" saurin kallonta Munnirah data sauke ido k'asa tayi jin abunda ta fad'a "Duk fa ba wannan ba, ki fara tayani murna dan kuwa na zama amarya" tana gama fada tayi rolling eyes ta fice, girgiza kai kawae Munnirah tayi, chan ajima saiga Ashphert tazo ta yini wa Ilhaam sai dare ta tafi, anan take fadawa Ilhaam tanada ciki, duk Ashphert tabi ta shiga damuwa yanda zata fara rainin ciki saboda tanada san yara amma tana tunanin halin Aameer, bey dace ya zama mahaifi da halin shaye-shaye ba, Ilhaam ce tayita kwantar mata da hankali

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now