💖💫RUDANI💖💫 78

46 24 74
                                    


MAIDUGURI.

Daga jiya zuwa yau kuwa sun baza hali tun ba Asmah mey dan banzan kishi ba, Ilhaam kuwa harta fara sanin halin su, Muhammad Najeeb duk ya fisu hankali but she can't say otherwise tunda shine babba, Abbaas kuwa banbancin sa da Aameer kadan ne danshi bayi shan komai, koh daga labarin da sisters nasa suke bata yanada yan mata da yawa. Ita kuma Asmah bakin kishi sai Bilqis da Halimah ba laifi sunada saukin kai, tun jiya da dare da sukaji labarin auren Yesmin ya d'aga musu hankali, tun ba yanda Yesmin ta kira Mummy tana kuka ba, Mummy bata wani bata goyon baya ba dan dalilin da yasa basu je bikin bama lokacine ya kure "So Yesmin is married dagaske?" Abbas ya tambaya dan a zahirin gaskiya ya kasa yarda "Yaa Abbas, dama fa chan Yesmin ba auren ka zatayi ba kuma duk kunsan haka, ba yanda za'ayi tayi dating Yaa Najeeb kuma tazo ta aure ka ae tayi baya tunda kai ba Yayansa bane" Billy ta fada amma koh ah jikinsa, shi damuwan sa auren dole da aka mata amma nothing like maganan aure tsakanin sa da Yesmin ae, wani sanyi ran Asmah yayi jin dagaske fa Yesmin aure tayi sannan taja hanun Khalifah suka wuce "But who's the guy?" Leemerh ta tambaya tana kallon Ilhaam, shiru Ilhaam ta mata dan ita kanta batasan waye ba tukun "That aside kowa auren nan dole yayi fa, so Ilhaam where can I see that your brother Aameer?" Leemerh ta tambaya "I can't say gaskia, yace zaizo dai yau but Aameer is a busy someone" ta fada gane Aameer take nufi "Oh wow guy in ya hadu, I remember seeing his magazine, first day ah office, he has been my star from that very day" shiru Ilhaam ta mata daga farko dan duk yanda take tunani Aameer ya wuce nan fa "Aameer fa bai cika mutunci ba dan kar ku hadu yaqi miki magana kiji haushi" Ilhaam ta bata amsa sincerely "Kuyi dariyan ku yanda kukeso but im crushing on that guy" ta fada factly ganin Billy da Abbas na dariya "But he is married and his wife came here" Bilqis ta bata amsa kafin azo ana wallahi tallahi da Leemerh "Yeah he is married" Ilhaam ta amsa calmly "Toh ae dadin abun mata hudu akace suyi" Leemerh da bata haqura ba ta fada, dan murmushi kawae Ilhaam tayi danta lura basu san waye Aameer ba, on the other hand Ashphert "So ke yaushe zakiyi aure?" Abbas ya tambaya in a flirty manner, kallon mamaki ta masa sai kuma ta fara wasu tunani, dariya Leemerh ta fara gane wannan ya dage wa Ilhaam fa, hawayen da suka ga Ilhaam ta fara ne suka nutsu "Sorry Ilhaam did I said anything wrong?" Girgiza kai tayi da sauri ta tashi zuwa sama, nan ta samu missed calls in Yesmin tayi calling back suka sha kukan su dan kowa da matsalan ta.


ABUJA.

Duk yanda Yesmin tayi ta cire damuwan nan ah ranta ta kasa, kawae inta tuna sai ta fara kuka. Ta gama waya da Ilhaam tana zaune ita kadai tana hawaye Rafeeq ya shigo mata da breakfast "I know I am wronged to marry you without your consent Yesmin, but please forgive me" kallonsa tayi kawae batayi magana ba hakan yasa ya zauna kusa da ita "Forgive me, forgive me, please. There aren't certain rules in this marriage and it will surely work, I fall for you and I pray we find nothing but peace in this marriage. I know what you went through. I am guilty and I admit it, there are no constraints in this marriage Yesmin. You only have to cover your body wherever you go" ah hankali ta juyo ta kallesa tana share hawayen "Yes I mean it. And I will take you back home, call me whenever you feel like accepting me as your husband, but please don't mention something like divorce. Bazan sake ki ba har abada" shi kansa saida yayi murmushi jin yanda yayi maganan "So please eat something" yana fada ya tashi zai fita "Rafeeq" Yesmin ta kira sunan sa hakan yasa ya juyo "Thank you" ta fada ah hankali, baice komai ba ya fita. Yana fita tadau waya ta kira Ilhaam, bai jima yana ringing ba ta dauka kuwa dan yana kusa da ita, ae basu jima dayin waya ba "Hi Ilhaam" ta fada ah nitse "How are you?" Ilhaam ta tambaya "I am fine and will be coming to Maiduguri" Ilhaam tace "Yess are you mad? Da izinin wa?" Dan shiru Yesmin tayi "He just set me free.." ta mata narrating yanda sukayi da Rafeeq "Wai bayan mun gama wayan ne ya shigo?" Yesmin tace "Eh fa" ta amsa "But he is nice by how he's reacting to your stupid acts" shiru Yesmin tayi kaman mey tunanin maganan Ilhaam, kuma gaskiya ta fada dai amma Rafeeq bayida mutunci koh kadan "Yesmin you heard from Anwaar?" Ilhaam ta tambaya jin Yesmin tayi shiru "Ilhaam yaushe ma na samu na fita? But I will stop by asibitin sai na duba sa" Ilhaam tayi saurin cewa "Nooo, ki barsa kawae before he starts asking questions, beside you are married kar mu fara batawa Rafeeq rai. Just make sure to check on Fadel please" dan karamin tsaki Yesmin tayi jin Ilhaam ta kira sunan Rafeeq, bata tsane sa ba amma taya za'ayi ya aureta ana zaune qlau? And that too Bilal da su Zoya suma sun cuceta da basu fada mata gaskiya ba, da bata ga wanda ya isa ya daukota gidansu ba, ba damuwa dai tunda yanzu yace zai maidata amma ya saketa gabadaya sai su cigaba da mutunci, nothing like love relationship "I need to take my breakfast, and try taking your medications am sure that is what Anwaar is calling for" Yesmin warned "Ni banda magani nan wajen" Ilhaam ta fada mata gaskiya "I will call that lousy Najeeb and inform him sai kuje asibiti a baki wasu" ta fada tana bata rai dan irin haushin Najeeb da takeji Allah ne yasani, jiya harda mata wasu long essays wai happy married life "Don't call him lousy, he is good and nice also" shiru Yesmin tayi ae ita Ilhaam bata dade da Najeeb ba balle tayi shaidan sa "Take your time and enjoy your meal" Ilhaam ta fada jin Yesmin ta shareta "Thank you am hanging" tana fada ta kashe, abinci kadan taci tayi wanka, rasa wani kaya zata sa tayi ma kawae tasa Abaya ta fara neman Rafeeq ya wuce ya kai ta gida, daki daki ta fara bi tana budewa bayi ciki, ae yasan zata nemesa ya kama ya wani je ya maqale, bude wani daki tayi ta zauna, tasa ah ranta koh bayi nan ah wajen zata jirasa saboda taga dakin is so big and calm. Takai 5mins tana zaune luckily kuwa ya fito wanka, dan karamin tsaki tayi ta juya "Hurry" abunda ta fada kenan ta ciro waya ta fara game "Can we?" Abunda taji ya fada kenan after the long wait, ya shirya abun sa and he looks so handsome, sharesa tayi taki basa hanunta ta tashi, tana tashi ya riketa "Come and sit" ba musu ta dawo ta zauna "Tell me about yourself before going on the leap" kallon mamaki ta masa, toh miye kuma bai sani ba, tasan so yakeyi ya bata mata lokaci yasa kawae ta yanke shawaran fada ya wuce, in bata fada ba tasan yayita kawo wasu abun kenan "I am Yesmin, I do whatever pleases me, I hate it when something is forced on me, and your marriage is one of it. I've two best friends, Ilhaam and Billy. My father is late, and I have been in many failed relationships, but Yesmin and Anwaar's will forever be iconic. Don't find me offensive or arrogant, I love Aameer but I knw that he had no intention of marrying me. I love Anwaar and I know there will never be marriage between us too. He married Ilhaam, my cousin and friend, no way am betraying our relationship, I love her" murmushi kadai Rafeeq yayi though he was hurt "Anwaar moved, why can't you?" Girgiza kai tayi "I already moved tunda nayi soyyayyah da Aameer, amma ae dole watarana na tuna daban auri wanda nafi so bako?" Gyad'a mata kai yayi dan bayisan wani trouble "Tell me about yourself too" ta fada harda gyara zama "I am Rafeeq Azeez, the Azeez heir and-" kafin ya acigaba ta tsaidasa "That's isn't your complete name, and too, Rafeeq is not a real name" yace "Yeah, Yesmin is not a real name either but I asked not about it because I already knew your real name. You know my real and complete name so why-" cutting nasa tayi "Shknn nikam" tana fada ta tashi "Kaini asibiti" kallon mamaki ya bita dashi "Are you sick?" Tace "Koh kwanan da nayi cikin gidan na kasan dole nayi ciwo Rafeeq, I don't love you. Amma yanzu lafiya ta qlau, I just want to meet someone" kafada ya daga dan yasan wajen Anwaar takesan zuwa "Learn to talk with respect first. I am your husband, and you have no right to see someone after marriage. In kinada niyya muje na kaiki gida" binsa da kallo tayi har ya fita, maganan sane suka fara mata ringing akai, mey yake tunanin kansa? A King? Barin tuanin tayi ta bisa suka fita, it was a silent drive dan Yesmin batayi rashin kunya ba shima bai kulata ba har suka isa gidan su. Ae kuwa yanda Maāmaa take shiga batanan take fita ba, ta wanke Yesmin tass harshi Rafeeq daya biye mata "In taga dama tabi duniya tana ce musu kai ba mijin ta bane ita keda zunubi tunda aure an daura sa" kuka Yesmin ta cigaba dayi kawae ganin yanda Maāmaa ke mata, waya ta dauka ta kira Bilal, bada jimawa ba sai gashi ya shigo, ganin su Yesmin ya karaso da sauri "Ina kwana?" Ta fada tana san barin kukan "Lafiya lau Yesmin. Rafeeq" ya basa hanu suka gaisa "Gata sai ka zauna ka mata fada hala taji naka ta zauna ah gidan aure" Maāmaa na fada ta tashi Yesmin ta bita da kallo "Yesmin miye matsalan ki ah duniyan nan? Kinsan dai auren nan dole kiyi sa koh ba yanzu bako? The earlier the better" kallon Bilal tayi ta hade rai ta fara share hawayen "Rafeeq is not my husband, he has no right commanding me" ta fada tana kallon Rafeeq hakan yasa ya sauke ido kasa kawae "Na yanke shawaran kawota gida, call me whenever your need arise" yana fada ya tashi Bilal ya hade rai ya ciza baki "Tashi ki bisa" Bilal ya fada ganin Rafeeq ya tashi Yesmin na zaune, sake gyara zama tayi hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, shiru ya mata kawae ya tashi yayi sama, bada jimawa ba sai gashi ya sauko da bulala, bata kula ba dan ta maida hankali kan waya kawae taji an zuba mata daya tuni tasa ihu "Husshh" yayi saurin sa hanu ah baki, kafin Yesmin ta gudu ya jawota ya mata shegen duka dan har kuka ta kasa ita kadai nishi take, tunda uwarta ta haifeta zata iya ce Bilal koh mari bai tab'a mata mata ba, mugu kawae "Har ke wacece da za'a ce ga abunda zakiyi kice ba haka ba? Karya zamuyi ba'a daura miki aure ba muce anyi?" Saurin girgiza kai tayi kafin ya sake second round "Dan Allah kayi haquri Yaa Bilal" harara ya bita dashi jin tace Yaya "Wawiyan banza wawiyan wofi, dole ki koma wajen Rafeeq" tace "I know, nasan dole na koma" ta amsa muryan na shaking, yarda bulalan yayi ya wuce ta, har Allah ya isa taso cewa amma ta kasa kawae ta cigaba da kuka.



💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now