💖💫RUDANI💖💫 26

176 33 16
                                    




"Aunty Aisha nace dama inaso naje gidan Baa na duba Mama Laure, matan tanada mutunci wlh"
"Ba inda zakije nasan yawo ke damunki" Kallonta Ilhaam ta tsaya yi dan wai a haka sunfi mutunci da Auntie Aisha sai yasa batasan zama gidan Yaa Abu saboda matansa tanada fad'a kuma batasan soldiers in nan nasa "Nidai na fada miki" Ilhaam ta maimaita saidai wannan karan kasa-kasa tayi maganan dan dama maras kunyan karya ce "In Yayanki ya dawo nace masa me?", "Sai kice masa kin koreni" ta fada tana dariya kasa-kasa "Kinsan karya ma kenan inba so kike ki kashe mun aure ba" tace "Toh nidai koh ma miye sai nabar gidan nan"..."Gaki ga gatemen Ilhaam Allah ya kiyaye hanya, Allah kuma yasa su barki ki fitan" pouting baki Ilhaam tayi kadan tasan koh kwana zatayi ah waje ba bari zasuyi ta fita ba "Aunty Aisha dan Allah fa nace" sai kuma ta shagwabe fuska "Ilhaam yanzu ki bari ah gama case in rasuwan Mami kafin ki gane musu, yanzu Aameer suke jira" kallonta tayi tasan tsaf Aameer koh ya dawo ba abunda zaiyi, tunda ake maganan koh shaida guda d'aya bai ajiye ba "Toh Aameer in da yace mun sai nan da three days zasu dawo kuma kice mun wae saina jira"..."Toh Ilhaam karki jira", "Aunty Aisha mana" ta sake pleading "Ilhaam Hida e jam?" (Ilhaam are you okay?) "Qlau nake" sai kuma ta rufe baki "Nipa ban jin Fulfulbe" ta fada tana dariya dan tasan neman maganan Aisha ya tashi "Kinji mey nace ae tunda kin amsa"
"Noo Allah nan iya sosai ba, kawae dai wannan bayida wuya ne"..."Toh ae koya zakiyi" tace "Yeah I'm thinking same, kafin ki fara zagina ban jiba" kallonta Aunty Aisha tayi kawae tana dariya, ah haka ta gama girki ba abunda Ilhaam ta tayata dashi sai surutu, magana kadan tace ita barin gidan zatayi, daki ta wuce taje tayi wanka tsaf da dauki jakka tayi waje dan kuwa bata wani haqura da fitan ba, driver da yake kai yaran Aunty Aisha makaranta ta samu ta hada baki dashi hakan yasa suna zuwa bakin gate aka bari suka wuce kasancewar sunga driver'n yara, gidan Baa ta wuce, kasancewar ba kowa gidan har tsoro gidan ya bata, securities da suke waje har ah lokacin suna nan Mama Laure da Munnirah kuwa suna part nasu na workers.

9:36 pm Dr. Farouq ya dawo gida, hankalin Aisha duk ah tashe yake tasan nata ya riga ya kare, sannu da zuwa tayi mishi harya je ya watsa ruwa ya fito domin supper baiga idon Ilhaam ba unlike before da yana dawowa ita zai fara gani complains daban daba "Banga Ilhaam ba and ina su Aareef?", "Sunyi bacci" ta bashi amsa "And Ilhaam?" Ya sake tambaya "Erm.. Ilhaam ta tafi gidan Baa" ta fada at last, spoon in abincin da zaikai bakinshi ya fasa "Kinsan abunda kike fada koh?" Ya fad'a da damuwa a fuskan sa "I'm sorry Doctor wlh na hana Ilhaam fita amma bansan ya akayi ta fita ba" ta fada ah dame itama
"Ilhaam is ur responsibility amma kin barta ta fita saboda sakaci koh?" Ya fara fad'a "Wlh Doctor na hana ilh-" saurin katse ta yayi "Can you please keep quiet" ya fada in a calm way, tashi yayi ya fita waje ya tambaye gatemen sukace basuga fitan Ilhaam ba, ba yanda bai buga ba sukace basu ganta ba kuma dagaske basu ganta ba saboda ah mota ta fita, yaje ya tambaye drivers na gidan duk sunce basu ganta ba harda driver'n yara shima dake wani munapiki ne yace bai ganta ba, daga waya yayi ya kira Ilhaaam tana ganin kiran jikinta ya hau b'ari tasan nata ya kare, ga tsoro ga sanyin laifi "Hello Yaa Farouq?"
"Kina Ina?" Ya fada da harsh voice, murya na bari tace "Inaaa.. ina gidan Baa" yace "Driver zaizo ya daukeki" yana fada yayi hanging, salati ta farayi tasan yau nata ya gama karewa, in less than 15min sai ga driver ya iso, addu'a ta shiga yi Allah yasa su wanye lafiya, suna isa taga Yaa Farouq ah cikin palo sai safa da marwa yake Aunty Aisha na zaune hawaye na bin cheeks nata dan batasan tashin hankali koh kadan, yana ganin Ilhaam ya matso ya zabga mata wani lafiyayyan marin da saida ya kaita k'asa, Aunty Aisha ta miqe da sauri zata karaso wajen ya d'aga mata hanun alamun ta dakata "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'oun, dan girman Allah Yaa Farouq kayi haquri" ta fada cikin kuka "Wlh bazan sake ba" koh sauraronta baiyi ba, belt in dake gefensa ya dauka ya shiga shafawa Ilhaam a gadon bayanta sai kuka takeyi, Auntie Aisha ce tazo da sauri ta rungume Ilhaam "Doctor dan Allah kayi haquri bazata sake ba koh Ilhaam?" Ilhaam da ta kasa magana kai kawae take gyadawa alamun eh "Mey kikeso ki xamo Ilhaam?" Ya tambaya cike da takaici "Wani gata ne baki samu ba Ilhaam?" Ilhaam shiru tayi saboda ta kasa magana, d'aga belt in yayi sai sake zuba mata Aisha ta tare ta "Aisha get out of it" tace "Aa Doctor forgive, her she's sorry" yace "No Ilhaam will never be yau ake mata fada? da kikaje can in kedawa zaki kwana ah gidan? ke kadai? sai maza? Saboda ke kika kawo rashin hankali dunia koh?" Sam shi ya manta Mama Laure na gidan, yarda belt in yayi ya wuce daki "I'm sorry Aunty Aisha, duk ni naja miki, I don't mean to put you through this" Ilhaam ta fada tana kuka "Kiyi shiru Ilhaam is okay ya wuce, tashi in raka ki d'aki" Mentholathum ta shafa mata a bayan, Ilhaam sai kuka takeyi, ah takaice dai daren ranan ba baccin kirki tayi ba, washegari bata fito yin breakfast ba Yaa Farouq yace Aunty Aisha ta kirata, ba musu taje ta kirata "Sit and eat" ya f'ada ganin ta "I'm not hungry" kallon daya mata ne yasata jan kujera ta zauna, spoons baifi uku ba taci tace ta koshi, sai tea da tadan sha kadan, tashi tayi zata koma daki ta hadu da Aareef "Aunty Ilhaam jiya ban ganki ba kuma after mun dawo daga school" ya fada cikin Kanuri yana murmushi, tsugunawa tayi ta daidaita tsayin su tare da mishi peck a cheeks nasa "Aika naje gashi na dawo koh?" Kai ya gyada "Then worry not, okay?" yasa kai yayi wajen iyayenshi, Ilhaam kuma tayi daki "Doctor I knw am wrong yesterday, amma dan Allah kayi haquri, kuma Ilhaam ba ita kadai bace gidan Baa akwae Mama Laure, indai tanason zama achan a barta tunda Mama Laure na iya kokarin ta wajen kulawa dasu" tayi maganan in a low calm voice "Nasan tana kulawa dasu Aisha, amma we are not leaving abroad, ya zama dole Ilhaam ta zauna ah gaban mu, bey dace tanada brothers haka dayawa taje wani waje ba, though Mahfouz ya koma Maiduguri but nida Major ae muna nan" yayi maganan cikin nutsuwa "Nagane Doctor, amma kafin Ummi ta tafi Canada ae wajenta take zaune, yanzu kuma ita takeso taje wajen Mama Laure as koba komai ta kula dasu tun suna yara, may be tana mata kallon uwa itama" dan shiru yayi ganin abunda ta fad'a gaskia ne, tunda Mama Laure na kulawa dasu bazata bari Ilhaam tayi something stupid ba "I will think about it" dan dadi Aisha taji dukda dai ba amincewa yayi ba, but at least yace zaiyi tunani

**

Da yamma Ahmad yayi mata waya akan zaizo, da kyar ta yarda, daya zo ta shigo dashi palon Yaa Farouq kasancewar baya nan Aunty Aisha kuma tayi bak'i "Sannu da zuwa" ta fada da wide smile, tsayawa kallonta yayi nan tace "What?" Ta tamabaya ganin kallon da yake mata "Are you really the one?" girgiza kai tayi tace "Eh mana so ya su Mama?"
"Suna lafiya tace na gaisheki"..."No fadi gaskia dai Ahmad batasan fa zakazo ba".."Toh ae kullum saita ce na gaisheki" tace "Kuma baka fada koh?" Murmushi yayi "Toh yaushe ma inna kiraki kike dauka?", "No Ahmad karka mun sharri har yanzu baka shirya aure bako? Mates naku sun fara fa" kallon mamaki ya tsaya mata "Meya faru?" Ta tambaya "Ilhaam ke na tsaya jira kuma kina mun zancen aure, kin shirya ne?" Shiru tayi tana tunanin fara fad'awa duniya aure zatayi, duk surutun da take zubawa Aunty Aisha ma ta k'asa fad'a mata "Ahmad actually dama inaso na fada maka, I can't go against Ummi saboda ta sama mun miji" ta fada ah nitse
"Duk kinayin hakan saboda Anwaar ne?" Ya tambaya dan duk ah zatan shi karya take masa, shiru tayi batace komai ba dan tasan ba yarda zaiyi ba balle ma kuma tace masa Anwaar, shiyasa ta yanke shawara bazata fad'a ba, tunda abokin sune ae zaiji "Ilhaam answer me".."No ba saboda shi bane, as I say this is Ummi's doing" ta fad'a tanaso ta fahimtar dashi amma yaki fahimta "Nasan saboda shine don't fool yourself Ilhaam ki bude ido kiga gaskia, Anwaar ya manta dake meyasa ke bazaki manta dashi ba? He moved with Teemerh" ya fada dan ya b'ata mata rai "Karyane Anwaar bayison Teemerh, he's just using her against me I knw" Murmushin takaici yayi ya tashi tare da buga kujeran da kafan shi, yasa hanu ah cikin gashin kanshi tare da furza iska ah baki alamun jin haushi, tunanin wani karya zai mata ya fara sai chan dabara ya fado masa "Banyi niyyan fad'a ba Ilhaam amma ya zama dole in fada, Anwaar zai aika gidan su Teemerh" hawayene ta farajin na sauka ah idonta saboda tasan Teemerh bata boyewa Ahmad komai me yiyuwa gaskia yake fada, kuma ba abunda yafi bata mata rai kaman ta tuna Teemerh taci amanta, duk ba wannan bama, yasan da auren Teemerh kuma ya yarda zai aureta? Juyawa tayi da gudu tayi daki, tasan tunda Ummi tace Anwaar ne toh ba abunda zai hana auren, hakan ya bashi daman ganin shatin bulala ah gefen hanunta, har ranshi yaji dukan amma ya ya iya? Yasan bazai samu amsa ba, ah hanyan fita ya hadu da Yaa Farouq ya gaisheshi cikin girmamawa tare da ce mishi wajen Ilhaam yazo, Yaa Farouq yace toh inda gaske yakeyi ya turo iyayensa, murna kaman zai kashe Ahmad, yau zuwanshi yayi fari, Ilhaam kuwa kukanta tasha mey isarta tare da alqawarin cire Teemerh da Anwaar ah ranta, waya ta dauko ta hada musu conference, Ashphert da Xeenerh nan ta zayyane musu komai, tuni Ashphert ta dau dumi, akan wani dalili zaice zai auri both Teemerh da Ilhaam, itafa Ashphert Allah ne yasa tazo ah qanwar Anwaar ba yayarsa ba, da wahalan da zata basa Allah ne kadai ya sani

Paris~~~

Yana zaune da iPad ah hanunasa, you can't say the exact expression dake fuskan sa saidai da gani kasan akwae wani abun, dan har Ashphert ta karaso bey sani ba "Babe kaji abunda ke faruwa kuwa? wai Anwaar zai aika gidan su Teemerh" iPad in hanunshi ya ajiye in shock "Pardon" maimaitawan kuwa tayi..
"Princess don't be fool, kinsan wannan bamai yiyu wa bane Dr. bazai auri wannan yarinyar bafa" zata sake magana ya dakatar da ita, banda shirme su waye Anwaar in zai aika ba'a ji lbr ba "Ku kun fiye kanamun magana, yarinya duk ta tsole muku ido, miye ma ina ya aureta ma, a peaceful human like Fatima" shiru tayi kawae jin ya kira Teemerh peaceful "Wai ma waye ya fada miki?" Ya sake tambaya "Ilhaam ce fa" ta amsa ah nitse "Ilhaam" ya nanata "Ni bansan Ilhaam da irin wannan abun ba duk kun koya mata" ya fad'a kanshi tsaye "Oh Babe yanzu muke koya mata kenan? Ni bansan meyasa kake backing Ilhaam kullum ake magana ba"..."Toh zaki hada kanki da Ilhaam kenan?" Tabe baki tayi tasan duk bai wuce dan ta hanasa mata shaye-shaye cikin gida ba, ba kuma zata lamunta ba "Kayi haquri bafa haka nake nufi ba" ta fad'a dan kar abun ya zama fad'a "Aa hakan kike nufi dai" tashi tayi ta karasa wajenshi, durgusawa ah gabanshi tayi ta rike haunshi "Kayi haquri Babe bawai inaso in hada kai da Ilhaam bane ba, I'm sorry dazu Xeenerh tace mun zasu tashi hala sun tashi ma" ta chanja topic in dan in ba haka ba yayita fushi kenan har su koma Nigeria yanayi, ignoring nata yayi ganin haka ta miqe ta zauna kusa dashi hanu tasa ta juyo da fuskanshi yana kallonta "I said I'm sorry" ta sake maimaitawa "Naji" kawae yace, zai juya tayi leaning ta cike gap in dake tsakanin su tare da owing lips nasa, pulling nata yayi sai kuma ta marairaice fuska tace "Please" yi yayi kaman be jita ba, juyawa tayi alamun tayi fushi, ganin hakan yasa ya girgiza kai ya jawota jikin shi ya fara kissing nata ah haka har aka zarce.






Team
#thealbaaz #aameer #ashphert



#RDN!

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now