💖💫RUDANI💖💫 18

220 43 15
                                    


September, 2023

Komawa ciki yayi ya fara neman Ashphert dan yau bai wani ganta ba, suna zaune ita da Xeenerh sai Yaa Ateekah da wata mata, gaisheta yayi bata amsa ba sai murmushin data masa hakan yasa ya nemi waje ya zauna kusa da Ash "Tashi zakayi ka bamu waje ae" Yaa Ateekah tayi magana ganin Aameer ya wani nemi waje ya zauna "Magana zan mata" ya bata amsa ah takaice "Gyaran jiki ake, sai ka bari in an gama kayi mata maganan" kallon su both yayi, dan neman tsokana yace "Ke Xeenerh b'aki fa ma kike karawa kullum" bata rai tayi nan Ash ta fara mata dariya sanin neman magana ke damun Aameer, banda haka ae Xeenerh fara ce "Kai Aameer bansan neman magana, ka tashi ka fita nace "Toh wai shi wannan kullum sai anyi? Tun yaushe ake wannan abun?" Ya tambaya still bayida niyyan tashi "Aameer" ta kira sunan sa "Nifa abar mun matana haka, dama tanada kyau tunda" yayi maganan hankalin sa kwance "Aameer mana" Ash tayi sauri tsaidashi, Kallonta yayi nan tace "Ka fita mana" tayi maganan kasa-kasa "Shikenan, for your sake" ya fada sannna ya tashi "Kamun magana da Anwaar" Yaa Ateekah tayi maganan ganin ya tashi zai fita "Bayi nan" ya amsa ah takaice "In ya dawo toh" da toh ya amsa ya fita, ba Anwaar ya dawo ba sai 1:3am danshi yayi imani dayin dare ah waje, ba kowa sai ya Ateekah, ganinta zaune yasa ya karaso "Yaa Atee, bakiyi bacci ba?" Tace "Ina fa maganan bacci ina jiran ka" yace "Amma komai lafiya?" , "Lafiya qlau" ta bashi amsa "Ya maganan aure?" Mamaki sosai yaji jin abunda take tambaya, haka kawae saboda zata masa maganan aure sai ta hana idonta bacci, shifa ya rasa gane matsalan Yaa Ateee "Amma wannan maganan ae koh zuwa safiya za'ayi sa" ya bata amsa "Inada tabbacin zan ganka?" Shiru yayi kawae dan dagaske ba ganinsa zatayi ba, hakan yasata maimaitawa "Ya maganan aure Anwaar?" Ya rasa amsan dazai bata dan da wuya yayi karya, yana yi ake ganewa "Ah yanzu dai babu" yayi maganan ah hankali dan bason maganan yake ba "Ka tabbata Ummi zataso zaman ka haka?" Yace "Aa dama bayan biki zan koma" girgiza kai tayi "That is what am talking about, zaman ka ah chan kana ga abu mey kyau ne?" Girgiza kai yayi "I can't say, but it is the best decision" tace "No, it will be the poorest decision Anwaar" jin yayi shiru tacigaba "Ita kuma Ilhaam fa?" Saurin kallonta yayi jin sunan data kira "Eh ita" ta maimaita "Banida plan na aurenta yanzu, bata sona yanzu" ya fada mata gaskia "Allah ya kyauta, we can't force her" kadai tace sannan ta tashi ta basa waje, ya dade zaune wajen yana tunanin lamarin, shifa ya rasa gane dalilin da yasa Ilhaam bata laifi, all that aside, shima baice ayi forcing nata ba tunda shima ba aureta zaiyi ba, how on earth zai fara zuwa yace ma Ummi yanaso ya auri Ilhaam? That is impossible saboda Ilhaam's answer will be No, and no one will force her, most especially Ummi da duk abunda Ilhaam tace dashi zatayi amfani dan bata ma sa Anwaar cikin jerin masu gaskia when it comes to Ilhaam, duk ya gama tunanin sa amma ba wani hanyan auren Ilhaam saboda shima bai sawa ransa zai aureta ba, inda ya sawa ransa Yaa Ateekah zata taimaka masa saboda itace shield nasu gabadaya, yasan yama Ilhaam ba dai-dai ba siding Fatima da yakeyi amma bayijin Fatima ta deserving hatred da Ilhaam dasu Ashphert ke nuna mata, all he knows is that Fatima is a good girl, and he believes the only way he can get Ilhaam back is taimakon da Fatima ke masa

Koh da safe da wuri yabar gidan zuwa clinic dan 2 days baije ba, Aameer kadai ke gidan dan Aameen ma bayi nan, dama shi bai cika shiga shirme ba, Aameer ne komai akeyi saiya shiga, palo-palo yake bi rike da cup yana gaisuwa dan mutane sun taru, dakin Ummi ya wuce neman Ilhaam dan yasan bazai sameta koh ina ba sai wajen, tana zaune da abinci gabanta sai juya cokali take, bata ma san ya shigo ba dan bawae sallama yayi ba, kamshin turaren da taji ne ta dauko ido, kafin tayi magana ma Ummi ta rigata "Fita kamun sallama" komawa yayi kaman yanda ta fada yayi sallama kafin ya shigo "Toh Allah ya shirye ka, miye ajikin sallama da bazakayi ba sai ka fadowa mutane daki haka?" Suhaila (Ummi's maid) ta fada da bacin rai "Maa Sully nayi bata ji bane" hararansa tayi ta cigaba da abunda takeyi, bai bi kanta ba ya karasa wajen Ilhaam "Ina kwana" ta gaishe sa, duba wristwatch nasa yayi jin tace ina kwana sai ganin afternoon yayi, whatever shi ba gaisuwa ta yake so ba "Ilhaam can we go out?" Saurin d'aga ido tayi ta kalli Ummi dake damuwanta, taji sa sarai amma bata kula yinsu ba, Suhaila ce tayi saurin amsawa "Ba yanda zata, kai baka rayuwa saida yawo koh?" Kallonta yayi yasan ita fa tana masa shishigi amma bai isa yayi magana ba ga Ummi wajen "Kaje, ina zuwa" ta fada ah hankali, cup in daya ajiye ya sake dauka ya fita hankali kwance, yana fita ta tashi itama "Koma ki karasa abincin" Ummi ta tsaidata "Na koshi" ta fada ah hankali "Kan naki yabar ciwo? Wai jiya da nace Anwaar ya baki magani ya baki kuwa?" Ita kanta yabar ciwo, dan harta manta ma "Ya bani" ta amsa, tasan tace bai bata ma Ummi ba barin zancen zatayi ya wuce ba, jin Ummi tayi shiru yasa ta fita, tana fita tayi wajen su Xeenerh dan bataga dalilin da zaisa taje wajen Aameer ana zaman lafiya ba "Babe, I've been looking for you daman" Ashphert ta fad'a ganin Ilhaam "Dole kice nema na kike ae tunda kin nemi ne" ta fad'a sannan ta zauna nesa da ita "Is this because I love you?" Ash ta tambaya, charap Xeenerh ta amsa "And you will continue to do soo" hararan Xeeenerh tayi irin waya sa bakin ki, suna cikin magana Aameer ya shigo danshi fa ya gaji da jiran Ilhaam kuma Munnirah ta fad'a masa tana nan "Xeenerh zo mana" ya fad'a fuska ba yabo ba fallasa hakan yasa ta tashi ta bisa "Xeenerh yarinyan nan avoiding ina take fa" tabe baki tayi ganewa da tayi Aameer bayida damuwa koh kadan "Ina miki magana kina jina?" Tace "Toh kayi haquri" ta fad'a dan batasan mey zatace bayan wannan ba "Xeenerh kinada hankali kuwa? Gani nake kaman laifi na mata" shiru tayi tana tunani wai dama shi Aameer gani yake beyi laifi ba kenan, toh koma miye bata isa shiga maganan sa da Ilhaam ba "Erm.. perhaps she is avoiding you saboda wani dalili, kaga ba ita zaka aura ba, kuma magana na Allah kun takura mata" finally dai Xeenerh ta fad'i abunda ke ranta "What do you mean an takura mata?" Xeenerh tace "Toh tunda biki ya matso duk kunbi kun dawo nan, ni sai nake ga kaman zaifi ku koma chan gidan Baa ku barta tayi biki lafiya" ta fad'a ah hankali "All that aside Xeenerh, I want my old Ilhaam back, yanzu fa koh magana bata bari muyi balle naji meke damunta" ita dai Xeenerh jin sa kawae take, banda haka ae Ilhaam ba damunta take fad'a masa ba tunda sai yayi dagaske, kuma duk yanda akayi dai yau Aameer bai sha komai ba, badan haka ba tasan answers in da take basa da tuni ya mata ba dad'i "Ke magana fa nake miki" ya dawo da ita daga duniyan tunanin nata "Do you have any gift in mind?" Yace "Wanda zan bata wai? Ilhaam is not getting married so No", "Then find something to give her, you know she love surprises" yace "Can a car do?" Har zatayi tsaki tayi saurin rike baki tuna ah gaban wa take "Kai kenan Dan Allah komai mota" zata sake magana ya d'aga mata hanun saboda ringing da wayansa yayi, shiru tayi tanaso taji waye "Hi Yesmin" taji ya fad'a hakan yasa ta sake baza kunne "Yesmin kina tunanin ni za'a wa auren dole? Don't be stupid ni da kaina nace inaso na auri Ashphert" taji ya sake fad'a dan ba bawae jin abunda Yesmin ke fada take ba "Calm down Yesmin, we are not meant to be together, so chill" kawae yayi cutting kiran abunsa, ganin kallon da Xeenerh ke masa yasa yace "Kee da lafiyanki?" Shiru tayi ta fara b'ata rai dan tayi imani da cewan inda Aameer qaninta ne toh saida mishi duka, amma inta tuna Ashphert zai aura sai tayi farin ciki tasan Ash will tolerate nothing of that sort "Ke Xeenerh matsala a dake munapurci, shiyasa kullum kika kara muni" murgud'a masa baki tayi ta juya zata tafi, ita duk kyaunta Aameer sai yana ce mata batada kyau "Ke na gama magana ne zaki tafi?" Ya tsaida ta hakan yasa ta juyo "That your Ilhaam, ki barta kawae inada abunyi yanzu, and for the gift, I will gift her something for being the stubborn sister ever" yana fadin haka ya juya ya bude fridge, tsaki yayi tunawa da ba komai ciki, dole ma ya fita yabar gidan nan yanzu "Aameer, don't start this, zan fad'awa Ummi" tsayawa kallonta cikeda takaici yayi, shii yanzu munapurcin Xeenerh ke damunsa, banda neman magana miye zata samo diary ta fara rubuta names na girlfriends nasa harda pictures nasu, toh duk ya share baice mata komai ba, yanzu kuma ce mata yayi zaisha wani abu da zatace zata fadawa Ummi "Go out, before I lose it" ya daka mata tsawa, da sauri ta fice tana cigaba da murgud'a masa baki




Teemerh na zaune ita kadai sai bata rai take, gani take fa tana binsu Florida toh maganan zuwanta biki bashi "Ke lafiya kika zauna kaman kin rasa uba?" Kallonta tayi kaman baza tayi magana ba "Yaa Xee, wai dole sai naje grad naki?" Harara mey ji da lafiya Zainab ta bita dashi "Bangane ba? Toh suwa nake dashi banda ke dasu Mummy? Zuwa kam ae kinsan dole ne" ta fad'a cike da nuna isa "Ba maganan dole anan, ni na hanaki yin karatu da wuri? Kin zauna kin bata lokaci yanzu kuma zamani na bazaki barni nayi yanda nakeso ba?" Ta fada cike da rashin kunya, gane rashin kunya ke damunta Xee bata amsa taba "Ke bazaki yi karatu ba?" Ta tambaye ta "Sai Anwaar yace nayi" ta bata amsan abunda ke ranta "Saboda Ub*naki ne shi koh? Dole ya yanke miki hukuncin rayuwa. Fatima meyasa ke ah duniya dan wayon nan da mutane suke dashi ke bakida?" Kallonta kadai Teemerh tayi dan ita karatun bayi ranta ma fa, akan wani dalili zata tafi karatu tabar Anwaar nan? Kalan tana chan ah kirata ace an daura masa aure da Ilhaam, ae bazai yiyu ba "Yaa Xee, kinsan Anwaar kuwa? So calm and gentle, randa za'a zo nema wa Anwaar aurena wajen Daddy zaki gane cewan I made the best decision" ta fada da murna, tsaki Xee tayi "Mutum da shegen girman kai, bayi gaishe da mutane fa Fatima" tabe baki Teemerh tayi "Ke gaisuwan sa ya dama, ni koh kullum safiya duka zai ringa mun ban damu ba, soyyayyah kadai nake dubawa" shiru Xee tayi tasan Anwaar bayison Fatima, amma ba'a isa ah fad'a ba "Yaa Xee, what is the secret to a successful married life?" Tayi tambayan ganin Xee ta shareta "Kiyi maintaining figure naki, ba daga shiga ki fara haihuwa anyhow ba" tabe baki tayi tace "Yazo gidan sauki ae" dan ita dama sam haihuwa bayi gabanta, akan wani dalili zataje ta haihu tasha wahala? Nan fa ta zauna ta fara tunanin rayuwanta. Washegari kuwa suka wuce Florida, yanda tasa ah ranta kafin ah gama events na biki ta dawo as she can't afford to missss. Da kwana hudu kuwa aka fara hidiman biki, duk wanda aka gayyace sa da ikon Allah yazo, Teemerh kam bata k'asan ma balle abun ya d'aga mata hankali

#RDN!

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now