💖💫RUDANI💖💫 9

270 54 11
                                    




Years After, still on flash back.

"Ni gaskia Mami gidan Baa zan koma, tun yaushe su Aameer suka koma mu an bar mu anan in nayi magana kice ba inda zani", "Wai ni yaushe su Aameer suka zama mates naku?" Shiru tayi batace komai ba sai fiki-fiki da ido da takeyi "Allah ya kiyaye hanya Zeenert sai kin dawo" ta fada ah takaice "Mami are you sure?" Ta tambaya dan tabbatar da abunda Mami tace "Yea, nayi magana da wata friend ina ta samo mai aiki ta mace wacce zata kula daku, dama ni gida ba mace aciki ne baniso kuje saboda ku mata ne", "Thank you Mami" Nan Xeenerh ta hada kayanta tsaf ta nufi part na Ummi, sai kamshi yakeyi dan kuwa Ummi macece mey san kamshi, dakin Ashphert direct ta wuce yanda ta tadata a baccin da takeyi peacefully "Ilhaam what's it?" Ashphert ta tambaya idonta a rufe dan duk zaton ta Ilhaam ce "Toh ba Ilhaam bace ba in zaki tashi ki tashi" tanaji haka ta mike tareda cewa "Oh Xeenerh miye kuma?" Dan baso take a dagata tana bacci ba "Gidan Baa zani in zakije kuma toh" da sauri tace "Zani mana, saidai Ummi ce bazata bari ba"
"Noo nayiwa Mami magana tace ta samo maid da zatana kula damu", "Ke kiji Mami fa, sai kace wasu babies", "Toh haka dai tace" Xeenerh ta bata amsa
"Ke Ilhaam fa?" Ashphert ta tambaya ganin basu shigo tare ba "Ilhaam na dakin Mami tana bacci tun jiya na mata maganan zuwa gidan nashi amma tace bazata yau ba", "Phew!. ana zaune fa jiya tacewa Ummi ita bazata kwana anan ba part na Mami zata" ta fada tana kokarin sauka "Ilhaam sai a hankali tashi mu tafi" nan suka sauko palo suka tarar Ilhaam har tazo tana kwance akan cinyan Ummi tana buga game "Good morning Ummi" cewar Zeenert tana jawo luggage nata "Awi eye? Ina zuwa haka?" (How are you and where are you going?) Ta tambaya tana kallon both of them "Gidan Baa zamu" Ashphert ta amsa da sauri "Toh in kunje sai kuma yaushe?" Ta sake maganan da Kanuri, wai fa duk dan su iya ake musu amma ah banza "Tabb wlh Ummi sai randa kika ganmu kawae, ga freedom ya samu" Xeenerh ta fada ciki-ciki", "Aya ke bazaki bisu bane?" Ta tambayi Ilhaam dake buga game nata hankali kwance "I'm exhausted I don't think zan iya binsu"
"Lalle Ilhaam kin raina mana hankali, daga bacci kika tashi fa, in bazaki je bane kawae fine" Xeenerh taja Ashphert "Toh tsaya in chanza kaya tunda nayi wanka dazu" saketa Xeenerh tayi ta dawo nan ta zauna parlour tana jiranta "Xeenerh miye sunan wannan game in ma?"
"Wanne?"
"Wanda naga kinayi jia"
"Nima na manta" 
"Karki fada nasan bawani mantawan dakikayi"
"Eh bazan fada ba"
"Haba Xeenerh ki fada mata mana"
"Nifa Ummi na manta ne shiyasa" daidai da fitowar Ashphert "Muje Xeenerh" Ashphert ta fada a takaice
"Toh kucewa Baa Adamu ya akai ku dan Ibrahim na hutu" Ummi ta sanar dasu "Toh shikenan" suka amsa in unison "Ku jirani na shirya zanje fa" Ilhaam ta fada sannan ta mike a cinyar Ummi, Ummi kam murmushi kawae tayi dan ta gane neman magana ke damun Ilhaam "Ba'a haifeki ba tukun, jinki zama zamuyi muna binki kamar wata Queen?" Xeenerh mu tafi kinji" Ashphert tace da ita sannan ta kama hanunta "Toh sai kuje ae xanzo daga baya" ta fada sannan ta koma ta kwanta "Eh zamuje dama" nan sukayi waje "Aya kinsan kinasan zuwa shine baki shirya da wuri ba?" Dan kallon Ummi tayi tace "Ummi nifa Aameer yace zaizo ya daukeni shiyasa"
"Aameer zai hadaku fada da 'yan uwanki fa Mamana kinga sunji haushi yanzu ma" Ilhaam dai ba wani damuwa tayi ba, tana mey cigaba da game nata tace "Shima dan uwanane ae, kuma he's my best friend" ta fada tana mika hanu sama "Toh Allah ya taimaka" Ummi ta fada

LATER..

"Ilhaam kinsan nifa banison jira koh?", "Toh dan Allah Aameer ba gani ba" ta fada tana gyara veil nata dake kokarin fadi "Ummi mun tafi" Ummi tace "Toh Allah ya kare" shiga mota sukayi nan suka kama hanyan gidan Baa "Yaushe ne tafiyan naku?" Ilhaam ta tambaya "In 3wks time" ya bata amsa"Oh Allah ya kaimu, yanzu in kun tafi sai kunyi 5yrs kafin ku dawo?" Yace "Eh kinsan Baa yace bai yarda muna dawowa hutu ba" ya fada hankalin sa nakan driving da yakeyi "Gaskia Baa bai kyauta ba, i will miss you" ta fada tana bata rai "I will miss you more Baby girl" nan ta sake ce "Yanzu shikenan in kun dawo zamu samu Lawyer, Doctor da Captain a Family" ta fada da very thrilled expression kwance face nata "Kin manta Yaa Farouq Doctor ne shima? We had one already, kuma Aameen will be an Architect ba Captain ba", "Toh nikam gaskia my Anwaar will be the best Doctor ever" Aameer yace "Toh nikam keda Anwaar naki ku auri juna mana kawai" saurin kallonsa tayi tace "Shhhh!" Ta zaro ido "Kar kayi Yaa Abu yaji maganan aure daga bakina, kasheni zaiyi" dariya ta bashi soasai "Okay I'm kidding amma closeness naku na duba ae", "Whatever, but Aameen ba Captain yakesan zama ba? Kuma kana ce masa Captain sometimes", "Yeah ya fasa inaga, yanzu dai he will go for the Architecture" shiru tayi batace komai ba dan bawai ta wani gane baya nan Aameer bane, haka sukayita tadi har suka iso gidan, tana ganin soldier na Yaa Abu tace "Za'a zo a dame mutane ba" Aameer yace "Yaa Abu ne zai dameki koh soldiers  nasa?" Ya tambaya dan confirming "Both mana, ace wai mutum koh ina zaije sai soldiers suna wani backing nasa" ai kuwa suna fita daga mota suka hango su Aameen da Anwaar kneeling down. "Subhanallah meya faru Aameer?" Ta tambaya ayayinda da gudu ta karasa wajen "Aameen meya faru?" Ta tambaya sannan ta tsuguna wajen "Ilhaam don't put yourself in any of this trouble kindly go inside" ya umarce ta "Aameen please" tsawa ya daka mata yace "Goo!" Soldiers in da suke tsaye ne wasu biyu suka karasu wajen da sandan su irin na soldiers da belt nasu suka fara dukan Aameer kaman an aiko su, dayan ne ya buga bishi sandan a kafanshi nan ya durkusa kasa da sauri "Auwch, awwghh da zafi fa, what are you guys doing ku barni haka" ya fada da muryan da ya fara shan wahala amma koh sauraransa basuyi ba suka cigaba da dukansa "Hey! Hello ku bakuda imani ne? meya muku? Ilhaam ta fada sannan tayi saurin hugging Aameer dan subar dukanshi amma dayan dake shi yafi rashin imani ya daga hanu ya shauda mata belt in a gadon bayanta, wani tayi sosai "Now get out of here" yace da ita cikin katon muryansa, Aameen da Anwaar a 360 suka tashi daga kneeling in da suke cikin rana sukayi kan Ilhaam suka rirriketa ganin abun nashi bana kare bane "How dare you raise ur hand on our sister? we're the ones who suppose to bear the punishment not her" Anwaar yace cikin bacin rai a dole shime mey qanwa, daya mey sandan ne ya kwada mishi amma koh kara baiyi ba dukda yaji zafi "Ilhaam kibar nan wajen meyasa baki ji?" Aameer yace da ita "Noo I won't let you guys" sauran Soldiers inne suka karaso suka raba jikin su Anwaar da Ilhaam suka rikesu gam-gam yanda bazasu iya mosti ba, wani cikinsu ne yazo zai kama Ilhaam nan tasa hanu ta hanyar dakatar dashi "Don't you dare touch me" Ta fada cikin muryan kuka, bey sake ce da ita komai ba yayi wuce warsa, shiko marar imanin belt in yayita zuba mata duk dan ta sake Aameer amma tana rike dashi tana kuka "Hey!" Sukaji an daka musu tsawa daga nesa, suna juyawa sukaga har Abu ya karaso, barin abunda sukeyi sukayi suka sa hanu a gefen kai alamun we salute you Sir, mari ya kwasawa Emanuel "Don't you have some shame?" Ya fada cikin bacin rai sosai "I only asked you to punish the boys then how dare you touch my sister? don't you think she's young to bear such a pain?" Ya fada tare da sauke masa wani marin nan sauran suka karaso wajen shi "You guys should take him along and do what's right" ya fada cikin haushi "I'm sorry Si-" bey karsa cewa sir inba suka jashi, tsugunawa Yaa Abu yayi amma har lokacin Ilhaam bata sake Aameer ba, janta yayi jikinsa, nan ta sulale sai anan Aameer ya samu karfin gwiwa "Ilhaam" ya kira sunanta zai tabata Yaa Abu yace "Don't" nan ya koma baya da sauri "What are you waiting for?" Yace da wasu soldiers guda hudu nan suka matso dan sake musu second round, daukan Ilhaam yayi har ya fara tafiya sai ya juyo ganin dukan da ake musu yayi saurin dauke kai ya cigaba da tafiya dan bayiso su basa tausayi, motan su Yaa Mahfouz neh ya shigo gidan, fitowa sukayi suka karaso wajen su Anwaar nan soldiers suka musu alamun gaisuwa "Give them the beating of thier life" Yaa Farouq yace yana danna waya dan kuwa baida aikin da ya fi wannan, shiyasa zaka gansa da glasses saboda danna wayansa yayi yawa, Yaa Mahfouz kam dama wani dirty look yake watsa musu dan ba karamin bata musu rai sukayi na, akan basuda mafad'a ne zasu fara fita cikin dare? "Doctor let's go" yace da Farouq

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now