💖💫RUDANI💖💫 46

108 22 54
                                    


Bai tashi ganin Ilhaam ba sai da safe akan dining suna having breakfast itada Ummi da wata 'yar uwan Ummi-Yaa Jabba sai Munnirah dake tsaye tana serving Yaa Jabba "Toh ango Allah yayi fitowan ka kenan" Yaa Jabba ta fada da fara'an ta, dan murmushi yayi ya gaidata dan ya gaishe da Ummi tund dazu, kallon Ilhaam yayi da he can't say the exact expression dake fuskanta, yasan bey kyauta mata ba jiya "Munnirah take my breakfast to the opposite living room" sannin ba kowa cikin wannan palon "Munnirah kuma bayan ga matanka? Mey ke damun ka Anwaar?" Yaa Jabba tayi saurin chapkewa, dan irin matan nan ne da basu gani bakinsu yayi shiru "Bakomai, naga tana cin abinci ne" d'aga ido tayi dan kallon Ilhaam da yace tana cin abincin sai gani tayi tana kan juya spoon "Tashi ki kai masa abinci, sai kici achan" ta umarce ta, ba musu ta mike tayi kitchen shi kuma yayi palon, cikin nutsuwa ta hada komai tayi wajen nasa, yana ganinta ya tashi da sauri ya karbeta "Ina kwana" ta fada kanta ah kasa, bai amsa ba yasan fushi take, dan ba haka take gaida saba, ajiyewa yayi sannan ya kamo hanunta ya zaunar da ita "Punish me Angelic" dagowa tayi jin abunda ya fada, suna hada ido ta sake saukewa "Bakomai fa" ta fada sannan ta zare hanunta cikin nasa "Why are you punishing me with your silence?".... "Am sorry, bazan kara ba" ta fada sai kuma tayi murmushi "That's my girl" ya fada sannan ya shafa gefen fuskanta, abincin sukaci cikin nutsuwa kafin ta tattara takai kitchen, tana fita taga Xeenerh, nan suka gaisa ta wuce wajen Anwaar dan yace mata zai maidata gida, bai wani dau lokaci ba ya fito ya sauketa gida, bacci tasha abunta, dan dama bata wani fiye san shiga hidiman ba

Ta fannin Teemerh kuwa akwae wankan maganin da zatayi kuma bai iso ba shiyasa sukace a daga daukan amaryan, tana zaune Aunty Sham na shafe mata jikinta da wani maganin da aka mixing nasa da turare "Aunty abubuwan nan basu fara yawa ba kuwa?" Ta tambaya dan tunda akace ansa auren su yau wannan gobe wancan "Wannan mijin naki mey shegen taurin kai ae kari ya kamata ki nema" ta amsata tana cigaba da shafe mata shi, Mum na daga gefe ta zama 'yar kallo, bayan ta gama ta kawo wani abu cikin bottle ta bata, ba musu ta karba "Shanye shi" Aunty Sham ta fada sannan ta zaune gefe, budewa tayi ta fara sha sai ji tayi ba dadi, daga kai tayi tana yamutsa fuska "Ki shanye nace" ta maimaita hakan yasa Teemerh sa kai tana sha tana bata rai har ta shanye tass, knocking da aka fara yasa sukayi saurin tattara abubuwan harda su kaskon turaren sannan ta karasa ta bude "Ohh Xee ashe kece, ae na zaci wata daban ne har kin samu tattara abu ba niyya" ta fada tana murmushi nan ta matsa mata ta shiga "Aunty shine koh shiryawa batayi ba? Ga en kai amarya fa sun fara zuwa" ta fada tana gyara wa Mufeedah riganta dan kuwa Mahmoud yasa an kawota ayi hidima da ita "Maza tashi ki shirya toh" Mum ta fada sannan ta mike zuwa jikin closet ta ciro mata wani lafaya, taimaka mata sukayi wajen nadawa Xee na binta da turare, tanasan Anwaar kuma ta ganta a gidansa shine burinta, yanzu kuma ji tayi duk bata wani san barin gida, kuka tasa ganin Mum da tayi bama wani abunda ya dameta, burinta kawae ya cika Teemerh ta auri mey kudi itama, ah haka suka kaita kasa fuskanta rufe tana dan kuka kasa-kasa

Ummi dakanta ta shirya komai na honeymoon duka amma wannan karon da Ilhaam za'a tafi, dan Anwaar bai yarda ta zauna ba "Meyasa kikeso kaje da Aya?"..... "Ummi already akwae gidan Ilhaam a UK kinga koh taje gidanta zata sauka" tace "Toh ae ba sai UK ba, ita Fatima zaka tambaya wani country takeso" Anwaar yace "Ummi this is too late, UK dai yanzu shine"....  "Ni kasan banison abunda za'a zo ana bakayi adalci ba saboda haka ba yanda Ilhaam zataje" kallon mamaki ya mata saboda ya rasa mey yake damun Ummi tunda ta fara maganan aurensa da Fatima duk ta chanzawa Ilhaam "Shikenan duk yanda kikace" a haka sukayi sallama, gidan Ilhaam ya wuce, be sameta ah ko'ina ba hakan yasa ya tsaya jiran fitowanta a bathroom dan yayi zaton tana ciki, bai dade ba sai gata ta fito tana goge gashin kanta alama harda shi ta wanke, tsalle tayi da sauri tayi hugging nasa "Ango kasha kamshi" ta fada da zolaya "Ke kuma amaryan ango ba" ya fada da murmushi fuskan sa shima "No amaryan ka nacan tana jiranka yanzu zamuje dauko ta ae sae ka saukeni" ta fada tana kokarin fara shafa mai kasancewar ta gama goge ruwan jikinta, key in mota ya cire ya daga mata sama "Your gift" tuni ta chapke "Oh wow, new car?" Ta tambaya hakan yasa ya gyada mata kai, ya bata wani mota lokacin bikin su fa amma gashi yanzu ya sake bata wani, she's happy ita kam gaba ya kaita "Thank you Anwaar I love you".....  "I Love you more" Shiryawa tayi tsaf yana zaune yana jiranta saida ta gama tace "Muje".... "You look stunning" ya fada tuni ta fara blushing sai kuma ta bata rai "What again? Haka zamuje kina bata rai?".....  "Ae kana ganin amaryan ka zaka ce tafini kyau" ta fada sincerely cike da kishi "Ohhh noooo, let's go" yayi saurin janta dan yasan Ilhaam akan wannan saita fasa fitan, basu tsaya ko'ina ba sai gidansu Teemerh, suna isa ta kira Ashphert "Babes are you here?" Ash tace "Eh yanzu isowana" tace "Toh muma mun iso yanzu, Xeenerh fa?" Ash tace "Tana motan Auntie Khadie".... "Oh toh shikenan" ta fada ganin Ashphert ta karaso wajen nasu "Ina yini Anwaar?" Ashphert ta gaishesa da fara'a "Lafiya" ya amsa a takaice "Ango ango" ta fada sai kuma ta sheke da dariya "Kefa Ashphert bakida hankali mu tafi kinji" Ilhaam taja hanunta "Bari mu shiga" dagawa Ilhaam in hanu yayi da murmushi suka shiga, gud'a ne kawae yake tashi har suka karisa cikin parlor, Teemerh na zaune a tsakiyan palon sai kuka takeyi ita ah dole tana kukan barin gidan dan kuwa kuka sosai takeyi tsakanin ta da Allah "Toh ah bamu amaryan mu tafi cewar Auntie Husna tana kokarin daga Teemerh "Kiyi haquri 'yar uwa haquri ya zama dole" Habeey ta fada, tunda su Ilhaam suka shigo suka matsa gefe dasu Ash, sai chusawa Ilhaam magana takeyi, ita dai Xeenerh batasan auren amma yanzu fatan zaman lafiya tasan ya kamata ayi amma Ashphert kaman wa ita aka wa, kokarin daga Teemerh suka farayi amma sai ta kara sautin kukanta, da kyar suka samu suka dagota tana mikewa Ilhaam ta karaso domin riketa "Kun ga qawayen Fatima masu shegen rawan kai koh, nace ta daina abota da qawaye masu kyau taki, ae irin wa'innan in suna zuwa biki sai su aure ma miji" cewan Aunty Sham, Yaa Xeee ce ta matsa kusa da ita tace "Uwar gidan Anwaar inne fa" dan ware ido tayi ganin tanasan yin shirme dan duk abunda yake faruwa bata taba ganin Ilhaam ba "Toh Allah ya kyauta" taso ta nemi abun zagi amma bata nemo ba  "Amiin Auntie" Habeey na daga gefe harda sake sako kai dan jin an ambaci uwar gidan Anwaar "Rate her" Xee ta fada ganin kallon da Habeey ke mata "She can take 9 out of 10. Saidai bata burgeni ba, banda dan bazan rawan kai da munapurci mey ya kawota?" Tayi maganan da karfi dan Ilhaam taso ji, kallonta kawae tayi suna hada ido ta bita da harara, ita Ilhaam dariya ma Habeey ta bata, banda haka miye nata. Fita sukayi harda su Aunty Xeee dansu zasu rakata kawae suka sata motan Anwaar, shi mamaki ma yayi dan ba daukan amarya yazo yi ba, mey ma zai sa yazo daukan amarya, zama sukayi su uku a baya, Yaa Xeee, Teemerh da Auntie Sham, sai Ilhaam a front, Habeey na daga motan Ahmad wai she can't withstand Ilhaam, cikinsu ba wanda ya mata magana hakan yasa itama batace musu komai ba "Sannu Anwaar an yini lafiya?"..... "Lfy lau ina yini" ya amsa kasa-kasa "Lafiya, toh Allah ya bada zaman lafiya"....  "Amiin" Yaa Xee tayi saurin amsawa, kaman yanda ya saba yana driving sai ya rike hanun Ilhaam hakan yauma yayi, kamo hanunta yayi saboda ya gama mantawa, Yaa Xeee ce ta taba Auntie Sham alamun tagani, kama baki Auntie Sham tayi cike da mamaki, ahaka har suka isa gidan Ummi dan chan za'a fara kaita ta gaishe da Ummi kafin washegari ta wuce gidanta, shiga yayi compound in yanda kowa yake shiga yayi parking nan suka fita da Teemerh, ganin baiyi niyyan fita ba Ilhaam tace "Uhm can we?"..... "Kiyi sauri ki fito mu tafi" ya fada ah takaice... "Bazaka shiga ba?" Ta tambaya "Ba abunda zanyi koh na shiga" Ya fada ba tare da ya kalle ta bama, bata sake ce masa komai ba ta bude mota ta fita, tana fita taji anja hanunta "Awch da zafi fa" ta fada dan yanda Ashphert taja hanunta ya mata zafi "Koh zuciya wai bakida shine?" Ashphert ta tambaya cike da takaici "Ash mey nayi kuma?"
"Mey zaisa kizo wajen Ummi? Yanzu nasan bawani abun zata muku ba, sai cewa da zatayi ku zauna lafiya" Ilhaaam tace "Ke kuma zaman lafiyan ne bakiso koh?" Dariya Ashphert tayi ta kama hanunta suka shiga ciki, samu sukayi palon a cike, Ummi da sauran en uwanta na zaune a kujera Teemerh na kasa hanunta cikin na Ummi kaman mutuniyar arziki "Yawwa Aya come here" Ummi ta fada ganin su Ilhaam sun shigo, sake hanun Ashphert tayi ta karasa kaman yanda Ummi ta fada ta zauna kusa da Teemerh dan wajen ne akwae space "So abunda nakeso daku shine ku hada kanku" Ashphert najin haka ta d'aga ido ta kalli Xeenerh dake gefe sannan tayi waje "Ku hada kai dan banson tashin hankali koh kadan, kar naji kunyi abunda ba daidai ba" Ummi ta fada tana kallonsu da duka kansu ah kasa "Ke Ilhaam ga amanan Fatima mun baki ke da Anwaar, ku rike mana ita amana dan batada hayaniya koh kadan kar a cutar da ita ta kowace irin hanya" Aunty Sham ta fada kanta tsaye, kallonta kawae Ilhaam tayi idonta ya fara cika da hawaye, ga aure mata miji da akayi ga maganan banza, Habeey da tun shigowan Ilhaam take halkance da ita tayi wani murmushi dan haka kawae taji dadin ganin hawayen Ilhaam, haka sukayi tayi Ummi nayi suma sunayi, ta fanni Ashphert kuwa tana fita direct wajen Anwaar ta wuce, a jikin mota ta samesa rikeda waya, jin tafiya ne yasa ya dago ya kalleta "Ya ke kuma kika fito?".... "I might get heart attack sitting in there"..... "What for?" Ya tambaya "Wai fada ake musu su zauna lafiya, gashi kwana biyu banida lafiya haka kawae bazan zauna su karan ciwo ba" ta fada sincerely "Ke kuma bakison zaman lafiya?"....  "Indai da Teemerh ce toh gaskia baniso" ta fada masa gaskiya "Hope wannan bakin naki bai cewa Ilhaam wani abu ba?" Shiru tayi tana kallonsa dan tasan ta fada "Am I not asking you? Kinsan bansan ana tashin hankali koh?".....  "Toh dan Allah zuba ido zamuyi muga ana wa Ilhaam hakan?" Bai sake ce mata kala ba hakan yasa ta cigaba da bayani "Kuma tashin hankali ae ya zama dole tunda ka auro munapuka" Girgiza kai kawae yayi zaiyi magana sai gani yayi ana fitowa hakan yasa yayi shiru
**
Ta fannin Ilhaam kuwa bayan an gama ta tashi taje yin kukanta cikin resting apartment na Ummi, the room was beautifully designed for rest amma ita kuka taji tayi ah ciki, zama tayi cikin daya daga cikin kujeran dake wajen ta fara rera kukan nata "You have to be strong" taji muryan da batayi tsammani ba hakan yasa tayi saurin dagowa, sai handkerchief daya miqa mata alamun ta share hawayen nata, karba tayi ba musu ta fara share hawayen "Mey kakeyi anan?" Tayi masa calm question "Am here to gather some information akan case na Mami, by the way why are you crying?" Girgiza kai tayi "Nothing" kawai tace ta tashi zata bar dakin "Ilhaam-" ya kirata sunanta a nitse "Aameer ka barni tukunna, I've to go Anwaar is waiting" tana fadan haka ta fita ya bita a baya, samun Anwaar sukayi yana jiran Ilhaam dan kuwa har sunsa Teemerh a motansa dan Ummi tace a kaita gidan ta kawai tunda an riga anyi abu mey amfani, karasowa sukayi ita da Aameer kanta a sunkunye ta shige mota "Dr kai da kanka?" Aameer ya fada sannan ya basa hanu suka gaisa "Yea ka samu kuwa?"..... "Nope a ranan da abun ya faru Ummi ta dawo bayan tafiyan mu, so bawani information da zan samu yanzu dole sai an gama hidima" ya masa bayani "See you tomorrow then" Anwaar ya fada sannan ya shiga mota, ahaka suka isa wani gida dake chan Neil road, ba marabansa dana Ilhaam sai yanayin paint haka, dan tsaki yaja kara ganin shirmen da Aameen ya masa, kaman shi ya ake sa yayi designing wannan gidan irin wancan, kuma ya masa magana sai ya maida abun na dariya, fitowa sukayi da Teemerh sukayi ciki, da kaman Ilhaam bazata shiga ba, sai kuma tabi Anwaar ciki, zuwa sukayi suka duba dakin daya musu sannan suka sata a ciki, Yaa Xeee ce ta sauko ganin shirun yayi yawa, tana saukowa ta samu Ilhaam da Anwaar na shirrin haurawa saman "Yawwa ni zan maida Ilhaam" dama abunda zaije fada musu kenan "Toh karde ka dade kasan ba kwana zamuyi ba" koh kallonta beyi ba yace "Angelic let's go" ya kama hanun Ilhaam sukayi exit, mota suka shiga sai gidan Ilhaam suna shiga ya kwanta a gado abunsa "Very Own mey kakeyi haka? Your bride is waiting"..... "Ke kuma fa?" Tace "I can manage kuma ae akwae securities a gidan so karka damu" dariya yaso yi ganin yanda Ilhaam tayi zaton zai koma wajen Fatima, shi duk cewan da yakeyi bayida abun yi da Fatima wato gani suke shirme yakeyi "I will miss your warm body" tace "I will miss you too ka tashi ka tafi kar mu shiga hakkinta" har cikin zuciyan shi bason zuwa yake ba amma ya ya iya? Yasan Ilhaam yanzu sai ta fara feeling guilty "Can I bath here?" Tace "No kaje can kayi kar su sani a bakin duniya" tashi yayi yazo kusa da ita ya mata peck a cheek "Sleep sound Angelic I love you" sannan ya fice, yana fita yayi dakinsa ya sa lock, warm shower ya sakar ma kansa, yana fitowa ya kashe wayoyin sa ya kwanta kaman ba er mutane ya bari chan gidan ita kadai ba, yana fita tahau gado ta bude chaptern kuka, she can't imagine sharing her husband. Saida tayi mey isarta tayi bathroom ta hada ruwan wanka mey dumi, ta dade cikin bathtub tana kuka sannan ta fito tasa lengthy nightgown tayi addu'a ta kwanta, batasan sanda bacci ya dauketa ba, batasan ba yanda Anwaar yaje ba da bata wahala wajen kuka ba.

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now