💖💫RUDANI💖💫 14

242 42 33
                                    



"Xeenerh what's it?" Ta tambaya ganin yanda Xeenerh ta dage sai taje "Come and shine your eyes babes" bata ce komai ba ta tashi ta bita daga chan nesa ta hango Aameer da Yesmin a tsaye alama ya nuna sun gama maganan su tafiya zatayi, Aameer ne yayi hugging nata bayan sunyi breaking hug in ta mishi blowing kiss ta tafi yana murmushi ya juyo kawae sai hada ido da Ilhaam yayi, hawaye sai sauka yakeyi, ita kuwa Xeenerh farin ciki tayi dan tasan Aameer bason Ilhaam yakeyi ba kawai iskanci ne dan ace he is dating Ilhaam yasa yace yana sonta, shiyasa koh da wasa bata fadawa Ashphert ba saboda taga hankalin Ashphert sam bayi kan Aameer rather Muhammad (her bf) "Ilhaam" ya kira sunanta da karfi amma kafin ya karaso ta shige ciki abunta "Duk ke kika hada wannan koh?" Ya tambayi Xeenerh rai bace "No, why should I? fitowa mukayi fa zamu dan-" bata karasa bama taga ya wuce ciki abunsa "Kaji dashi dai, player kawai" tana fadin haka ta dau waya dan kiran Aameen saboda shi bai samu zuwa ba

***
"Look Aameer, ba abunda zakace mun, your actions say it all" shiru yayi dan yasan tabbass Yesmin gf nashi ne amma at the same time bayiso ya rasa Ilhaam "Im sorry Ilhaam" ya fada calmly "Amma I've never loved you" wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata tana mamakin dalilin da zaisa Aameer ya mata haka "So cewa da kayi zaka aureni duk karya ne?"
"How do you even think zan aureki? for the Almighty's sake, Ilhaam you are my sister, kawai I said that to make you feel like a queen saboda you deserve to be love" rasa abunyi tayi dan ta tabbatar Aameer bafa santa yakeyi ba dan yanda yake magana ba wasa ciki, cire zoben daya sa mata ranan ta yar abunta "This is for wasting my time" tana fadin haka ta share hawaye ta barshi a tsaye, murmushi kawae yayi at least ta sauko, komai zaiyi wa Ilhaam ah duniyan nan bazata iya fushi dashi ba, that is one thing he has as a weapon. Bayan 3 days suka bar Georgia

Magazines ne sun kai 5 da kuma different newspapers, tanada san karanta magazines so anytime ta gani sai ta duba, na farko ta dauka Vogue ne hakan yasa ta bude ta fara dubawa, it contains fashions and more, bata gama ba ta ajiye ta dauko na biyu, a zaune take amma saida ta sake gyara zaman ta "FIRST DAY AT THE OFFICE" ta ga an rubuta da hoton most handsome guy her eyes has ever seen "Masha'Allah" ta furta a hankali sannan ta bude, "Barrister Aameer Albaaz first day in court, read article below" abunda taga ansa kenan, nan ta fara karantawa saida ta karance sa tass tana admiring Aameer, tana gamawa ta tashi da sauri zuwa dakin wani brother nata dan shi ke karanta both magazines da newspapers, zata shiga taga ya fito "Halimah what's wrong?" Ya tambaya ganin yanda take nishi "Yaa Najeeb dama inaso na tambaye kane" ta fada tana wasa da hanunta "Sauri nakeyi zan fita" ya fada ya wuce ya barta tsaye, ganin haka ta tabe baki tayi kasa, dinning area ta nufa yanda ta samu Abbas zaune ga abincin amma baci yakeyi ba yana waya, girgiza kai tayi tasan bayida aikin da yafi na 'yan mata mahimmanci "Leemerh lafiya kika sa Yaa Abbas kina kallo haka?" Bilqis ta tambaya sannan taja kujera ta zauna "Bashi nake kallo ba" ta fada calmly, sai ah lokacin Abbas ya gama wayan ya dago yana kallon su "Miye kuma?" Ya tambaya yana wani bata rai dan ba sosai yakeso yana zubawa 'yan mata karyan zai aure su ah katse sa ba "Erm.. Yaa Abbas kasan wani Aameer Albaaz?" Ta tamabya tana jiran amsa, kallonta yadan yi kaman bazai yi magana ba yace "Ke kuma ah ina kika sansa?" Ya tambaya kaman wani bey san waye Aameer ba "Yanzu na karanta magazine, so I saw his article" kallonta Bilqis tayi da sauri tace "Toh mey kikeso ya fada miki kuma bayan kin karanta article?" Ta tambaya harda ware hanu "Help me asked her, as you read there in the magazine, he is a Barrister here in Abuja"
"Yaa Abbas is he your friend?" Halimah ta tambaya "Nah I've never met him in person, you can asked Yaa Najeeb halan ya sanshi, as you know the magazines belong to him" ya fad'a without showing concern "I will surely like to meet that guy, ya burgeni sosai, like he is amazing fa" kallonta kawae Abbas yayi bey ce komai ba dan ya san Haleemah da shirita "Toh wai in yanasan ganin ki koh in bayiso?" Bilqis tayi saurin tambaya jin abunda Haleemah tace "Gane mun hanya, Aameer is a busy man, you can't meet him haka kawae" Abbas ya fahimtar da ita "Kaifa kace yana Abuja shima" ta fada kaman mey shirun kuka "Girl in kika ce zaki bi na wannan guy in toh da sauran ki, dan banzan girman kai gareshi" Bilqis ta fada sannan taja tsaki tabar wajen, kallonta Haleemah tayi tana tunanin ah ina Billy ta sansa "Ke fa bakida matsala Haleemah, be ready to see his interview yau at 9" Abbas ya fada sannan ya mike ganin yanda Haleemah tayi shiru kaman mey shirin kuka, batace komai ba har yabar wajen tadai sa a ranta kuwa zaga interview in, kuma saida ta gani, tun daga ranan ta ishe su da maganan how charming Aameer is

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now