💖💫RUDANI💖💫 62

85 25 55
                                    


Washegari da safe Ilhaam coffee ta kawowa Anwaar saboda ba niyyan making breakfast take da ba, ana suna Aunty Sham tace wa Munnirah wai taje gida ta huta after knowing ba wani maid gidan Anwaar, ita burinta Ilhaam ta wahala. Karba yayi ya ajiye nan ta tsuguna tana gyara mishi takalimi "My Very own Doctor, nikam da yau ka haqura da zuwa clinic innan, I need your time, kaga sai muje wajen Ummi and Yaa Abu tunda ta dawo" ta fada bayan ta tashi "Toh ae akwae patients dayawa so I've to be there" Ya fada mata gaskiya "Nikam ba Shareef nacan ba?" Ta tambaya dan tabbatar wa "Zoya needs his time" ya fada yana dariya, itama dariyan tayi, Anwaar found a new hobby shine teasing Ilhaam "Oops I almost forgot, randa nakai Teemerh delivery kasan they refused to checked on us wai sai anyi payment?" Cup in dake hanunsa ya ajiye "Stop fighting people Ilhaam, I saw a video of you and Zuby online" rintse ido tayi ta bude a hankali "Na rufe fuska fa, and she tried humiliating me" yasan Zuby can do worst dan ita a haukan ta taya Fatima kishi takeyi kuma yayi maganinta for trying to disrespect his wife, he suspended her "Don't worry, Zubaida will never try that crap again" ya mata bayani as she smiled "Is that Aameer I saw with you?" Saurin girgiza kai tayi, tasan yasan Aameer ne but he tried to confirm it, batada hankali ne zatace masa Eh, har zaiyi fada ya share abun ganin how scared she looks, bai shiryawa kukan Ilhaam early morning ba, bayan ya gama ya manna mata peck a forehead zai wuce tace "Yau bazaka tambaya rakiya ba? Anyways muje
na raka ka" smiling yayi ya kama hanunta suka fita, suna fita main parlor suka tarar da Auntie
Sham zaune kaman su take jira, kuma daman jiran nasu takeyi tayi munapurci "Ina kwana Auntie" ya gaisheta calmly "Iafiya qalau Anwaar an tashi lafiya" yace "Iafiya lau" dan kallon Ilhaam yayi alamun ta gaisheta, ta gane sarai amma ta kauda kai kafin ta juya tace "Ina kwana" ta fada dan dole "Lafiya lau Ilhaam yau bazamu samu breakfast bako?" Saurin dafe kai Ilhaam tayi tasan yau wannan matan ta gama da ita "What do you mean?" Anwaar yayi interrupting "Ilhaam bakiyi breakfast ba kuma kinsan halin da Fatima take ciki?" Ya juyo da kallonshi kanta, fiki-fiki ta farayi da ido "And what are you waiting for? Kije ki hada breakfast" ya sanar da ita tare da janye hanunsa daga rikon da yayi mata "I will get going" ya fada bayan ya gama fadan kuma "Ah dawo lafiya" ta fada ciki-ciki, itama Shamsiyya hakan ta fada saidai ita da fara'a, Ilhaam kuwa koh kallonta batayi ba ta juya ta nufi kitchen danyin abunda Anwaar yasata. Tana gamawa ta fito taci karoda Auntie Sham dake sintiri wajen "What! ke in sa'mun ido kikeyi ne?" Ilhaam ta tambaya da mamaki "Ni kin gama ne koh tukunna?" Auntie Sham ta tambayeta "Kije ki dauka mata" ta fada tana kokarin wucewa amma Auntie Sham taki bata hanya. "Ki matsa mun na wuce I'm not ready for all of ur dramas, please" tayi pleading dan ta lura sam matan nan batada rike girman ta "Ki kwantar da hankalin ki Ilhaam, mu sai munsa kinbar gidan nan" Ilhaam ji tayi maganan ya shigeta amma tayi shiru kafin Aunty Sham tace tayi disrespecting nata.
*

"Ahmad dan Allah a dinga bin abubuwa ah hankali, toh miye dan ka aiko da gifts Anwaar yace ah maida? It doesn't make sense to send lots of gifts saboda kawae matansa ta haihu" ta masa bayani "I don't care amma your husband is not well again. I will be leaving this country for good, zan dawo after good 2 years In Shaa Allah dan bazan zauna nan ina ganin mijin ki da matansa ba" ya fada rai bace "Ahmad ka auri Sarah dan Allah, Sarah is in love with you kuma tanaso kabar halayen da kakeyi" yace "You are mad, Sarah is currently in school wae sai ta gama karatu tayi aure. And it's my promise nasa Anwaar kuka, so I will take Ilhaam even if it's by force" haushin magana takeji dashi amma jin yace Anwaar zaiyi kuka ta girgiza kai tana murmushi, Anwaar will never cry for Ahmad amma dai zataso ta gani "Fatima come and have your breakfast" taji muryan Aunty Sham da sauri tayi cutting, at least yanzu zata samu sauki tunda Ahmad is leaving the country "Auntie Anwaar in fita yayi?" Ta fara pretending kaman ba abunda tayi "Eh meya faru?" Teemerh tace "I thought zai shigo amma kinga ya fita abunsa",
"Ke Fatima wai mey yake damunki ne? Jia da bakinki kika cemun yace yana sonki kuma ba abunda zai raba ku right?" Kai Teemerh ta gyada ah hankali tana sake tunanin rayuwanta, Anwaar's different personalities pissed her up sometimes, she's very sure bayi taba fita bai ga Ilhaam ba "Eh hakane Auntie amma-", "Amma mey?" Aunty Sham tayi cutting nata "Bakomai.. inaga I will call back Munnirah kawae" ta fada sanin yanda situation zai kasance "And why calling her back?" Tayi tambayan tana b'ata rai "Saboda Ilhaam bazata jure mun breakfast ba, kuma bayison bacin ranta zaice ta bari karshe ke zaki shiga kitchen fa Auntie" saurin dafe girji Aunty Shamsiyya tayi "Lalle yarinyar nan kin rainawa kanki hankali, toh ni koh a gidan mijina bani girki ke kin sani ae, toh wae ma ke a ko yaushe baki iya jan hankalin namiji ba? Fatima mace ita zatayi abunda namiji zai sota fa kar ki manta wannan amma kullum akayi magana kice Ilhaam, ke meyasa bazaki yi zuciya ace Fatima ba? Wawiyar banza kawae" ta fara fad'a "Auntie Sham duk abubuwan da kukace inayiwa Anwaar shi nakeyi, da na fara nuna kishi nakeyi da ita, amma na lura bazai soni ba inna cigaba da haka, I took your advice bana nuna masa ina kishi da Ilhaam amma ita qiri-qiri take nuna hakan amma sai cewa yake tanada zafin kishi ne, ni bansan mey zanyi kuma in burge shiba" ta fada shaking her head "Aunty may be dasan yarinyan nan aka haifesa" Teemerh ta daura "Toh ki bude kunnen ki ki saurare ni" kallonta Teemerh tayi "Im all ears Auntie Sham" ta amsa giving her all her attention "Kinga na farko karki bari ranshi ya baci akanki, sannan kar kiyi abunda zai kawo sabani ah alakan ku ma'ana karki bari kuyi fada, sannan ita kuma wancan aljanan kina yi mata zagon kasa dan ita bakisan mey take ce masa akanki ba" girgiza kai Teemerh tayi "Auntie Sham wlh baza ki taba gane halin Anwaar ba, ba abunda take ce masa akaina, I know Ilhaam tun ba yau ba kawae bayi ganin laifinta ne koh kadan, lokacin nadayi sanadiyan barinta gidan nan nima ban samu kwanciyar hankalin ba harsai lokacin da ta dawo, ah nikam ita rahama ce agareni" sauran kadan Aunty ta maketa saboda haushi ta matsa "Wawiya abunda nakeso ki fahimta kenan tunda koh Malamin chan yace cire soyayyan ita aljanan kishiyan taki a zuciyan Anwaar in bamai yiyu bane amma ke be Ilhaam and let her be you Teemerh, ki zama kece yake gani yaji dadi, ki zama kece mai kawo farin ciki ba waccce za'a bawa farin ciki ba. Ki lura da duk wani abunda Ilhaam take masa sai ki daura akan nata. Abunda tayi da wanda batayi ba duk kice tayi saboda ki batata ah idonsa" dan shiru tayi kafin tace "Oh wow Auntie Sham shiyasa nake sonki, amma kinsan ance wani baya taka rawan wani" Sham tace "Toh ki zauna karki taka nata kina zaune ta maidaki bazawara" ta fada tana huci saboda haushi "Aa Auntie ae dole nayi aiki da maganan ki, kefa uwace" ta fada dan ganin ran Aunty ya fara baci. Tashi Sham tayi ta karasa wajen crib in da Fadel yake "Yana ta bacci abunsa"... "Eh yakan dade yana bacci in badai yunwa yaji ba"

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now