💖💫RUDANI💖💫 19

216 42 14
                                    


Yau ya kasance daurin aure yanda aka daura auren Al'ameen Isma'il Albaaz da Zeenert Abdallah Albaaz akan sadaki dubu dari biyu da sisin gwal arba'in, yanda aka daura na Aameer Abdallah Albaaz da Aisha (Ashphert) Yusuf Albaaz akan sadaki dubu dari biyu da sisin gwal arba'in itama kasancewar tare sukayi deciding sadakin da zasu bayar, shirin "Kla Tulta" aka fara, side na Aunty da ba kowa wajen sai gyara da akeyi kullum aka sa Amare yanda ake Kla Tulta, Xeenerh na zaune tsakiyan palon while Ashphert na daga gefe tukun, Hajiya Amina, Friend na Ummi da sauran mata sun zagayeta suna wanke mata dogon gashin dake kanta, bayan an gama akace tayi alwala sannan ta gudanar da sallah raka'a biyu dan nuna godia saboda by that time an daura aure, Ashphert ce ta biyu the same abunda aka wa Xeenerh haka mata, ita kam bata fiye san abubuwan nan ba, hakan yasa take ta bata rai, bayan nan Duramma (mey kitso) tayi wa Xeenerh (kla yeska) a Kanuri traditional hairstyle, yanda Ashphert tace a bar mata kanta haka, gyarawa kawai akayi amma yayi kyau sai kyalli yakeyi "You look fabulous" Ilhaam ta fada tana murmushi "Not more than you" Ash ta bata amsa "Ummi na kiran ki" sukaji muryan Munnirah nama Ilhaam magana "Toh barin zo" tana fada ta tashi zuwa dakin d Ummi take, tana zaune sai Maa Laure da Suhaila dake gefe suna packaging abu, itace yanzu tunda aka fara hidima kullum saita ga Ummi na packaging abubuwa "Ga wa'innan, ki kaima Hajiya Amina, sannan zata baki wasu ki taho dasu "Ummi dazu na ganta anan fa" ta fada tana dubawa kaman ance ta nemo ta "Eh ta koma, tace sai zuwa gobe in za'ayi yini kuma" tsugunawa tayi tadau biyu kan zata kai mota ta dawo tadau sauran "Amma bansan gidan bafa Ummi" sai kuma taja ta tsaya "Yanzu duk iya rayuwan ki baki taba sanin gidanta ba?" Dan rintse ido tayi ta bude "Ohh itace ah Durumi?" Tsaki Ummi tayi jin shirmen da Ilhaam ke mata "Tana Garki 2 dai, Hajiya Sadiya ke chan Durumin" ta bata amsa, ganin Ilhaam na tsaye ta tabbatar bata fa sani ba "Zuba mun aika na" Ummi ta fada tana girgiza kai tasan koh taje shirme zata mata "Zanje fa" ta fada sannan ta juya "Dawo Ilhaam" Suhaila tasa baki "Kinsan gidan koh baki sani ba?" Kad'a kai ta fara alamun Aa "Toh shi wancan mey zaman banzan ya kaita mana" Maa Laure ta chapke "Wa wai?" Suhaila ta amsa dan bata gane waye ba "Anwaar mana" tana fada Ilhaam ta sake musu aikan su ah kasa, ganin kallon da Ummi ta mata tayi saurin durgusa wa dan tattarawa "Sai ki samesa ya kaiki ae" Ummi ta fada ah takaice "Nasan gidan, na tuna" ta fada sannan ta mike da gudu, saidai kafin ta fita Ummi ta tsaidata "Wai lafiya kike yau? Aya kika mun shirme zan sab'a miki, tun wuri in kinsan bakisan wajen ba ki fada mun gaskia" tsayawa tayi kaman mey shirin sa ihu tana rarraba ido, Ummi batace mata komai ba tadau waya ta kirasa, dama zaman banzan yakeyi as Mama Laure's saying saboda yau koh Clinic bai duba ba, samun waje Ilhaam tayi ta zauna jin an kirasa, bada jimawa ba ya karaso "Aya zaka kai mun gidan Hajiya Amina, zata bada kaika ka dawo da ita. And make sure ka shiga ka gaidata dan zuwanta dazu ta neme ka" kallon Ilhaam yayi data sauke kai k'asa, koh ba'a fada masa ba yasan kuka takeyi "Yanzu ne?" Ummi tace "Eh yanzu mana, ga sauran ka tayata dauka" da toh ya amsa ya dauki sauran, saida ta tabbatar ya fita ta share hawayen ta dago fuska, koh bari su hada ido da Ummi batayi ba ta fice, yana jikin mota yana binta da harara, ganin haka ta dauke kai kaman batasan yana wajen ba, taimaka mata yayi da sauran na hanunta suka sa a mota sannan ya koma ya shiga, ba wanda yace ma wani komai, dan yasan yana mata magana zata fara sana'a yasa bai kulata ba, saida yaji shirun yayi yawa bata fada masa yanda zasu ba kafin yace "Ina ne?" Dago ido da mamaki tayi tana kallonsa dan yanzu ta tabbatar nata ya kare, shima ba sanin wajen yayi ba amma ya yarda zai kaita "Wai..wai Ummi tace tana Garki" ta amsa muryanta na rawa "Tana kusa da Yaa Ateekah?" Ya sake jefa mata tambaya, kai ta fara kad'awa alaman Aa "Bansani ba nima" ta fada ah takaice "Ke which of the Garkis?" Tsayawa kallonsa tayi dan batasan wanne bane "Yanzu ke saboda shirme gidan Friend na Ummi ne baki sani ba?" Nan ya samu waje yayi parking, shiru ta masa gane magana yake nema, banda neman magana shima ae basani yayi ba, zai dau wayan ya kira Ummi sai ga kiran Fatima, kafin ma taga waye mey kira yayi saurin daga wayan, bai amsa ba saida ya gama ringing nasa, kiran ne ya sake shigowa hakan yasa ta daga ido ta kalle sa, ji takeyi kaman Teemerh ne, shima gudun kar tayi suspecting wani abu yasa ya amsa "Ina yini" Teemerh ta gaida sa "Lafiya lau" ya amsa kaman bashi ba "Will call you later" yana fadin haka yayi hanging, jin haka hankalinta ya kwanta tasan ba Teemerh bace toh, tasan in Teemerh ce bazai amsa ta haka ba tunda yana santa, Ummi ya kira, nan tace masa tana Wushishi street, karamin tsaki yaja gane gidan da yayi bayan an masa kwantance "Kai ka sani" kadai tace a ranta, ita batada burin daya wuce ta fita cikin motansa, ba wanda ya sake magana har suka isa, kafin ya gama parking ma ta bude mota ta fita, shidai baice mata komai ba dan ya kula yau sam ba hankali jikinta, tsayawa tayi ya ciro kayakin ta dauko wanda zata iya tayi gaba, gateman in ne ya taimaka masa da sauran, yana shiga ya samu ta baje tana bayanai "Wai tace zaki bani wani aikan" ganin Anwaar ya shigo yasa bata amsa Ilhaam ba, da fara'a ta amsa gaisuwan sa "Ashe tare kuke" yace "Eh" sannan ya zauna "Gashi, dama na riga na hada, zan taho da wannan goben da yardan Allah" ta fad'a bayan sun gaisa da Anwaar, da toh Ilhaam ta amsa tadau marble cups in dake cikin box "Ilhaam wae duk kar biki ya wuce kine kike wannan saurin?" Girgiza kai tayi alamun Aa ta koma ta zauna "Sai ki bari ae koh ruwa kusha, amma daga zuwa sai tafiya "Aunty, sauri muke dama, ni zan wuce Clinic" tace "Toh banda abun mahaifiyar kuma dai, gata da Doctors har biyu amma saita tsalla ka chan wai jinya, wannan ciwon zuciya dai Allah ya yaye mata shi" saurin sa hanu cikin gashin kansa yayi jin abunda wannan mata ta fad'a, he is very sure Ilhaam batasani ba, amma gashi yau taji ah gari, itama kallonta tayi sai hawayen daya taru ah idonta "Ummi?" Ta maimaita "Eh mana, Allah dai ya yaye mata" ta amsa dan ta zaci abun gwaninta tayi, hawayen dake idonta ne ya sauko jin wai Ummi is suffering from heart attack, toh shi Anwaar as a cardiologist miye amfanin sa? She is very sure Baa died of heart failure, toh yanzu ga Ummi kuma, girgiza kai kawae tayi tadau box in ta fita ba tare da sake tsayawa jin wani abu ba "Kaje kawae Anwaar, za'a fito da sauran dan ba iyawa duka zakayi ba sunada yawa" da toh ya amsa yadau boxes biyu ya fita, nan aka ringa fitowa da sauran, Ilhaam na gefe sai kuka take kaman wanda aka ma mutuwa "Look, ba kuka zaki tsaya yimun ba, c'mon get into the car" share sa tayi ta fara share hawayen kafin ta shige mota, har suka fara tafiya batayi shiru, tana share hawayen tana sake sabon kuka, shifa bayisan kukan nan koh kad'an, koh ce mata kayi wani abun zai samu Ummi oho mata "Koh kiyi shiru koh ki fice mun a mota" ya daka mata tsawa, maimakon tayi shiru saita k'ara masa volume, ganin ba shiru zatayi ba ya samu waje yayi parking, ganin yayi parking ta d'aga idon dake zubar da hawaye ta kallesa "Lokacin da kikayi deciding dena kuka, inform me" yana fad'in haka ya fita yabar mata motan, kukanta ta cigaba dayi, saida tayi abunda ya isheta kafin ta fito tana neman sa, street in so silent kuma bayi wajen, sabon kuka taji, tsoron ta Allah tsoronta ta koma gida ba aikan Ummi amma da tayi tafiyan ta dan tasan Anwaar dan rainin hankali ne tun ba yau ba, kukanta ta cigaba da rerawa wajen koh motan ta kasa komawa, tayi kukan harta gaji idonta harya kumbura amma hawaye bai bar zuba ba, tana tsaye tana share hawayen taga ya fito daga gidan da yayi parking motan dai-dai gate in wajen, shida Shareef suka fito "Man, da Ilhaam kake shine-" kafin ya k'arasa ma Anwaar ya tsaidasa "Shine mey? Miye zata shiga tayi ah gidan ka?" Girgiza masa kai kawae yayi, at least dai saiya kira sa yace gashi ah waje ya fito su gaisa "Ilhaam ya gida" Shareef ya fada ganin sai faman goge hawaye take, bata ce masa komai ba ta shiga mota "Gobe sai ka sake ganinta ka mata magana ae" Anwaar ya fad'a cike da takaicin abunda Ilhaam tama Shareef "Ka sata kuka, kuma kana blaming nata?" Anwaar baice masa komai ba ya juya zai shiga mota ya tsaida shi "Bazaka ce ta shiga su gaisa da A'eesha ba?" Kallon da Anwaar ya masa ne ya sashi dariya "Ohhh na manta ashe Fatima zaka kawo mana" ya fad'a still da dariya "Ita fa Fatima tanada kirki and she is not my girlfriend, itama tasan haka" Shareef yace "Nima ae bance batada kirki ba, yes she's kind amma banga advantage in abunda kukeyi ba, you are hurting Ilhaam, kuma hakan kakeso ta koma maka?" Anwaar yace "Karka damu, bayan biki zan koma, koh ita Fatima bazata sake ganina ba, and that will be the end of everything" nan Shareef yace "Okay, see you tonight, yanzu kana b'atawa Ilhaam lokaci" ya fada sannan ya basa hanu suka gaisa, har zai tafi Anwaar yace "Doctor Shareef" Juyowa yayi "Ka sake gaishe da amarya" , "Kak'i zuwa biki ae dole" murmushi Anwaar yayi yace "Gashi ae na wanke laifinta nazo yau" da haka dai sukayi sallama Shareef ya koma gida Anwaar kuwa ya shiga mota, shiga yayi ya samu ta gama waya da Ash kenan ma, he can't say the exact expression dake fuskanta, but one thing for sure is she is not happy "Yanzu ke saboda rashin kunya, Shareef kika ma wancan shirmen? After fully knowing who Shareef is to me right?" Shiru ta masa, ita ah dole ya b'ata mata lokaci  "This is the last time da zan miki magana ki shareni" nan ma shiru ta amsa hakan yasa yaja motan suka tafi, suna isa ta fita da gudu koh kayan bata tsaya daukan wasu daga ciki ba, gidan an cika, kowa sai kallonta yakeyi dan da ganin idonta kowa zai gane tayi kuka, hijab in dake jikin ta taja ta rufe fuskan zata wuce daki ita mey wayo taji muryan Ummi na kiranta, saurin sake rufe fuskan tayi ta k'arasa wajenta, bata ce mata komai ba ta kama hanunta sukayi daki "Miye na rufe fuska kaman mara gaskiya?" Ta fada tana jan Hijab na Ilhaam baya "Meyasa meki?" Abunda Ummi ta tambaya kenan ganin idonta, kad'a kai tayi alamun ba komai "Kika mun karya zan kwad'a miki mari" Ummi tayi assuring nata hakan yasa tayi saurin matsawa "Nifa bakomai, shine ya barni ah mota ya fita" Ummi sighed "Zatayi magana ma taga Anwaar in yayi sallama ya shigo da wasu boxes, baice komai ba ya ajiye zai fita ta tsaidashi "Ka kyauta Anwaar, ka cigaba da b'ata mun rai kana samun yarinya kuka" tsayawa yayi jin Ummi ta fara magana "Kai duk duniya ba wacce kake jin zaka sauke muguntan ka kanta sai ita koh?" Shifa yasan ainihin kukan bashi yasa Ilhaam ba, amma dai yasan ita fa Ummi bazata yarda ba "Kiyi haquri Ummi, hakan bazai sake faruwa ba, it was a mistake", "In kaga dama ka sake, ke kuma kije kiyi wanka, ki wanke fuskan nan mutane sai tambayan ki suke" kallon Anwaar tayi kafin tayi gefensa ta fita "I am terribly sorry Ummi" ya maimaita ganin bata kulasa ba "Kaje ka kawo mun sauran aika na" ta fad'a da serious tone hakan yasa ya fita. Ta fannin Teemerh kuwa dogon tsaki taja jin wae ta kira Anwaar amma yana ce mata zai kirata daga baya "Ke da lafiya ki koh?" Aunty Sham tayi saurin tambaya jin tsakin da tayi "Aunty imagine na kira Anwaar bai tsaya yaji mey zance masa ba wae zai kirani" itama Sham in tsakin tayi, dan ba sosai take san jin sunan yaron can bakin Teemerh ba "Toh mey zaki ce masa?" Xee ta tambayeta "Yaa Xee kinsan basu inviting ina biki ba kuwa?" Tace "Toh taimakon mey zai miki?" Teemerh tace "Shine zan fada masa basu inviting ina ba gashi anjima zan shigo Nigeria" tabe baki Xee tayi tace "Allah ya kyauta" Shamsiyya kam dama chan bata kula yin ta ba "Amiin, zasu sha mamaki, biki dai dole naje" ta fad'a cike da gadara da nuna isa

Okayyy... we can be Ilhaam or Teemerh. It's a choice

RDN!

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now