💖💫RUDANI💖💫 12

267 48 21
                                    



"Aameer ba wani hanya?"
"Eh baddest saboda duk cikin qannen nawa Ilhaam ce takeda wuyan sha'ani" ya fad'a masa gaskia "Gaskia Dude I love her" kallon sa Aameer yayi kaman bazaiyi magana ba, sai kuma yace "Toh gaskia Ahmad saidai ka hqaura ka bata time", "Kasan irin son danakeyi wa Ilhaam kuwa? In ban aureta ba banajin zan iya yin wani aure"
"Baddest haquri zakayi with time she will fall for you don't worry, amma sai ka chaging kafin in dau kanwata na baka" ya fad'a masa gaskia saboda Ahmad deserves no one "Don't worry, I lost interest in other women the very first time I start loving her"
"Toh da yafi" ya fad'a aha takaice "Ina take mudan gaisa"
"Bata nan taje gidan Ummi" Ahmad yace "Barrister yau kace akwae drama kenan" ya fada yana dariya "Ba kadan bafa Ahmad" yace "Yanzu yana can?"
"Eh yanacan" ya fad'a ah nitse "Ni kasan dama munyi waya yace mun ya dawo Nigeria"
"Ya dawo fa" Aameer ya fada yana dariya nan sukayi sallama kowa ya wuce, dakin Ashphert direct Aameer ya wuce, budewa yayi ya shiga danshi knocking ba nasa bane, kamshi dakin yakeyi as usual, tana kwance da sleeveless waist length nata amma koh kokarin gyarawa batayi ba saboda gadaran ta ae dakin ta ya shigo "Babe kallo kike ne?"
"Eh" ta amsa sama-sama dan hankalinta na kan kallon "We need to talk" jin hakan yasa ta tashi ta zauna "Toh inaji" ta fad'a tana gyara zaman ta "It's a surprise" ya bata amsa "Toh ba yanzu zaka fadamun ba kenan?" Ta fad'a tana yatsina fuska "No right, but close your eyes" rufe ido tayi eager to hear the surprise "Open it" ya umarce ta, tana bude ido taga shirtless Aameer da tattoo in sunanta jikinsa "Wo-wow, this is fabulous, but I don't like someone shirtless other than my man" ta fada dan ta b'ata masa rai saidai ran nasa bai baci ba "So im still not the man?" Ya tambaya da mamaki dan haryanzu Ashphert bata daina raina masa wayo ba"You will soon be" ya fad'a ah takaice "Then karki damu I can wait for you no matter the years" yana fadan haka ya fara maida rigansa "But when do you have this?" Yace "I did it the first time I love you" dadi sosai Ashphert taji amma saboda ita 'yar duniya ce koh nunawa batayi ba, dan tadi ya zauna ya mata kafin daga karshe ya fita

***
"Ummi! Ummi!" Ilhaam ke kiranta tun daga entrance door, dan kuwa heartbeat nata taji is not stable shiyasa takeson fad'awa Ummi "Naam Aya yau kin tuna da Ummin naki kenan" Ummi ta fad'a da Hausa dan kuwa tasan koh tayi mata da Kanuri ba amsa zata samu ba, saidai tana shiga wa zata gani? Anwaar mike a kujera yana danna waya, mutuwan tsaye tayi saboda in badan kallon pictures nashi ta takeyi a social media platforms nashi ba toh fa ba lalle ta gane sa da wuri ba saboda ya chanza gashi ya kara kyau sosai "Mamana?" Ummi ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, dauke kai tayi sai anan ya juyo ya kalleta, ba karya he missed her so mucchh, amma ganin bata mishi magana ba sai yi yayi kamar be ganta ba "Umm.. Ummi ina yini" ta fada ah dan nitse "Lafiya qlou Aya" ganin Anwaar koh kalllnta baiyi ba Ummi tace "Anwaar bakaga Ilhaam bane?" Sai anan ya tashi ya zauna saidai kanshi akan wayanshi "Na ganta Ummi" ya amsa sincerely "Ina yini" Ilhaam ta fada a hankali kamar wanda akasa dole "Lafiya" kadai yace da ita sai da yadau 'yan seconds kafin ya dago ya kalleta "Ya schl?" Tace "Erm.. I'm home" dan ido ya zaro yace "You must be kidding" tace "I'm serious", "Anwaar Baa yace bazasu cigaba da karatu ba sai sunyi aure" Ummi ta karbeta "Oh I see" kadai yace sannan ya maida hankalin sa kan waya, tashi Ummi tayi ta shiga ciki a zatonta koh akwae tadin da zasuyi, dan ita har addu'a takeyi Allah yasa Anwaar ya auri Ilhaam danko tana matuqar sansu tare, tunda ta tashi ba wanda yace ma wani uffan, dama saboda ita sukayi maganan dazu, Ilhaam kuwa duk zaman ya isheta dan kuwa ita kadai tasan yanda heartbeats nata keyi, shikam Anwaar mamakin Ilhaam ya faraji saboda yanda yaga tayi shiru, ba haka yasanta ba, Ilhaam dayasani me surutu ce, inda dane da yanzu ta cika mishi kunne da surutu lalle girma ba abunda ya bari, dago ido tayi ta kalleshi saidai  ba kallonta yake ba, idonshi na kan wayan nan nashi, tashi tayi da niyyan barin wajen sai ji tayi yace mata "Wait!" Tsayawa tayi chak sannan yace da ita "Come back and sit" hakan kuwa tayi, zama tayi saidai ta kasa samun sukuni, itakam kamar ba Anwaar nasu ba, she never feel nervous before but look at her now, zama yayi yana kare mata kallo tass, jin yana kallonta kasa d'ago ido tayi ta kalleshi saidai sake sunkuyar dakai tayi "Inasan magana da Ummi ne"
"And when did I said karki mata magana?" Kasa cewa komai tayi, ringing in da wayanta keyi ne yasa ta dago ido ta kalleshi alamun zata amsa waya "Answer it" yace da ita, ba musu ta daga
_
"Hello Ilhaam?"
"Hi, how're you doing?" Tayi maganan ah hankali kaman mey tsoron wani abu "I am fine. I've been waiting for your call since yesterday" kasancewar tayi masa karyan zata kirashi "Aw ban samu lokaci bane" yace "Can I visit you today?" Daga ido tayi ta kalli Anwaar da shima tunda ta fara wayan yake kallonta kamar yaji abunda akace, sai kuma ta sake sunkuyar dakanta cikin sauri "No I'm not home", "Ilhaam please, koh baki gida ae zaki dawo, you just don't know how much I love you that's why, inso na ganki pls ban taba cewa zan visiting naki kika yarda ba, saidai su Ashphert su inviting ina"
"Okay!" Kadai ta iya cewa "Kin amince kenan?" Ba tare da cewa Eh ba, tace "You can come"
"I love you" Ahmad ya fada badan yana bukata amsa ba "I'm hanging" Dipp ta kashe wayarta.
_
Dagowa tayi ta kalli Anwaar ta haryanzu take kallonta "Kallon yayi yawa" tace dashi sincerely, yii yayi kaman bey jita ba dan kuwa bai bar kallon nata ba, ganin haka ta tashi da sauri "Come back" ya tsaidata "I need to talk to Ummi pls" ta marairaice fuska, hanu ya daga mata alamun taje, ganin saurin da takeyi murmushi kawae yayi ya girgiza kai "Har kun gama gaisawan kenan Aya?"
"Ni wlh Ummi sai kallona yake tun dazu" ta fada tana marairaice fuska "Toh kin masa kyau ne ae Mamana" dan shiru tayi sai chan tace "Ni kam gaskia banasan kallon, yayi yawa, Ummi the saddest thing baije gidan Baa bafa I was shocked to see him here" tayi maganan k'asa-k'asa "Ni kuma na zaci daga can yake saboda naga acan suke sauka"
"Baije ba shi kam" ta sake fad'a "Aameen kam ya gujeni koh, in yazo saidai ya tsaya a gidan Mami tashi" Ilhaam tayi dariya tace kuma "In-law ba", "Allah ya sanya alkhairi" Ummi ta fada da murmushi "Amiin Ummi na" ta amsa da murmushi  "Aya yaushe zaki fito da mijin ke kuma?" Rufe fuska tayi da sauri wai ita kunya, yanzu kunyar Ummin taki kike yi Ilhaam?" Girgiza kai ta fara kuma "No Ummi ba haka bane ya kamata na tafi" tayi maganan cikin sauri "Kawai yau kinji kizo ki ganni ne?" Ummi ta tambaya ganin har Ilhaam zata tafi "Ummi heartbeat ina is not stable, yana beating faster" Ilhaam ta dauko wani zancen "Toh koh akwae abunda ya baki tsoro?" Ummi ta tambaya, nan ta girgiza kai alamun Aa "Toh ki rika yawaita fadin Innalillahi wainna ilaihi rajiun aduk lokacin da kikaji haka" gyad'a kai Ilhaam tayi alamun toh "Zan tafi" Ummi dai ganin ikon Allah take yau wajen Ilhaam, daga zuwa sai tafiya kuma, tasan dai dole akwae dalilin ta na dagewa saita tafi "Gashi driver na hutu, kin shiga wajen Mami kuwa?" Tace "Eh wajenta na fara zuwa, Ummi gashi fa nacewa driver'n gidan Baa kar ya dawo, kuma yanzu nasan hala ya sake fita, ba lalle ya dawo fa" ta fada kaman zatayi kuka "Toh kuma Driver daya ne gidan Baa?" Ummi ta tambaya da mamaki "Ummi yanzu kema fa kin fada, it's December sun dau hutun Christmas" ta fada ah nitse "Toh Ilhaam ae ni bansan zaki cemasa ya tafi ba koh?" Gyad'a kai tayi "Eh hakane I will just call on Aameer or Aameen wani yazo yayi picking ina"
"No haba sai kin dago su daga gida kuma a'a ga Anwaar ya kaiki dama beje ba ae, kuma yana cewa zaije kawae ku tafi tare"
"Aaaa'aaa Ummi" ta fada da sauri sai kuma tayi shiru, da mamaki Ummi ta juyo tana kallonta "Meyasa Ilhaam?"
"Saboda kar mu takurashi koh halan sai zuwa anjima yakeda niyyan fita" ta zuba mata karya dan kuwa tasan halin Anwaar tun ba yau ba, Aameer kadai take cewa ya mata abu anytime ba tare da tsoro ba, dan murmushi Ummi tayi sannan tace baza'ayi haka ba, muje na mishi magana ya kaiki, ba musu Ilhaam ta tashi suka sauko palo saidai kamar yanda Ummi tayi zato ya tashi a parlour in "Ilhaam kirashi kice masa yazo"
"Em.. Ummi banzo da wayan nan ba na barshi a gida" tuni ta hada mata karya saboda batada digits na Anwaar "Yanzu kin fara yawo ba waya kenan" dan murmushi kawae Ilhaam tayi sanin karya tayi, Ummi ce ta dauko wayanta tare da kiran Anwaar in "Ina kake?"
"Ina wajen Mami" ya amsa in a calm way "Toh in kun gama ka k'araso" dama ba wani tadin kirki sukeyi da Mamin ba hakan yasa ya dawo side na Ummi "Aya nakeso ka mayar gida" wani kallo ya watsawa Ilhaam da saida taji hancin cikinta sun kada ae tuni ta sunkuyar dakai tasan baza su wanye Lafiya ba "Ummi ina driver'n gidan Baa? ta kirashi I've alot to do" ya fad'a yana wani bata rai dan yau duk cikin plans nasa ba fita "Batace yadawo ba, you have to take her home" Ummi ta maimaita masa "Toh Ummi" dan kuwa duk abunda Ummi ta fada mishi ya zauna, baya mata musu "Aya ki bishi"
"Toh Ummi sai anjima" nan tasa kai, ah parking space ta sameshi nan sumu-sumu ta bi wajen motan Mercedes-Maybach da yake ciki, shiga tayi batace uffan ba, kamshin turaren ta dana Anwaar ya hadu da kamshi mey sanyi da motan keyi "Ke Yanzu dan bakida kunya kinga nayi miki kama dame kaiki gida?" Domin Anwaar ba abunda ya tsana kaman asashi abunda baiyi niyya ba "Ae Ummi ne tace na bari zaka kaini" ta fad'a tana kauda kai gefe "Oh saboda na zama driver naki koh?" Kin amasa shi tayi ganin yaki Jan motan su tafi tace "Ni bance ba" tun daga lokacin ba wanda ya sake ce ma wani uffan har suka iso, suna shiga parking space sukaga Ahmad ya fito daga mota Honda NSX alamun zuwanshi kenan, kirjinta ne taji ya wani buga sosai, ganin motan Anwaar yasa ya tsaya dan su gaisa sai kawae yaga Ilhaam tashi a ciki, bayan ya gama parking ne suka fito, har zata wuce shi sai kuma tace "Sannu" da fara'a ya amsa "Hey Baddest yau kaine anan?" Anwaar ya fada tare da mika mishi hanu su gaisa "Ae zuwana na biyu kenan yau "Lafiya? zuwa har sau biyu haka?" Anwaar ya tambaya da mamaki "Nazo wajen mutumiyar ne" ya nuna masa Ilhaam da ta kusa shigewa "Oh I see, ita tace maka kazo kenan?" Ya tambaya saboda rainin hankali "Eh ita tace nazo kaga ta wuce kuma koh ganin ka ne?" Murmushi kawae Anwaar ya masa yasan bazata tsaya ba daman "Alamu ya nuna kana bullying mun future wife koh Doctor?" Dariya Anwaar yaso yin jin abunda Ahamd ya fad'a sai kuma ya daure "Why should I?" Kasanta da ra'ayi", "Wollah nima abun yana damuna taki bani chance fa" murmushi kwance fal fuskan sa yace
"And you will never get that chance" ya fada sincerely cikin husky voice of his "Why?" Ahmad ya tambaya da mamaki "You know that very well" Anwaar na fadin haka ya bar Ahmad a wajen, dan kansa ya fara binsa zuwa ciki, saidai maganan da Anwaar ya fada "And she will never give you that chance" shi yake maimaitawa, suna zuwa palo Anwaar bai wuce koh ina ba sai dakin Ilhaam yanda yabar Ahmad a main parlour, yaje haurawa sama ya hadu da Ashphert a balcony ita da Xeenerh sai tadi suke tana ganinshi ta tashi tayi hugging nashi "Ae Ilhaam tana ganin ka a gidan su Ummi ta mana texting cewa ta ganka" Xeenerh ce ta mike itama tare da cewa "You're welcome our latest Doctor" ta fada hakan da wide smile "Thank you" yace da ita tareda raba jikinshi dana Ashphert "Tana ciki?" Ya tambayesu "Eh meya faru?" Ashphert uwar gulma ke tambaya amma koh kallonta ta beyi ba ya karssa dakin Ilhaam tare da knocking "Come in" he just love everything about Ilhaam's room, most importantly the scent, gaban Vanity yasameta tana warware ribbons dake kanta alamu dai wanka zata shiga "Will you keep him waiting?"
"Who?" Ta tambaya kaman wani bata sani ba, hakan yasa baice da ita komai ba ya samu waje ya zauna akan gadonta, tashi tayi ta karaso wajen nasa "Anwaar what is wrong?"
"I love you Ilhaam" ya fada sincerely, Ilhaam kuwa banda dariya ba abunda takeyi dan tasan Anwaar is kinda funny sometimes, mutumin da kullum hade rai yakeyi ne zaice wai yana santa? Tayi yaya dashi? Saidai tayi ya isheta kafin tace "Wait, don't imitate Ahmad please, yanzu zanzo na samesa" ita duk zaton ta Anwaar imitating Ahmad yakeyi saboda shi ke cewa "Ilhaam I love you" tana fadin haka ta dau towel, zata shiga bathroom ya rike ta "Ilhaam why?" Yayi maganan so calm "Anwaar what's it?" Ta tambaya ganin yanayin sa "Ilhaam why will you choose to hurt me? don't you know that I love you and I wanna be with you for the rest of my life? then why do you choose to bring in Ahmad?" Wasu zafafan hawayene taji yana sauko mata dan yanzu ta tabbatar ba wasa yakeyi ba, saboda yanda yayi maganan say it all "Ilhaam I loved you tun ina school, I can't think of anyone sai ke Ilhaam, that's the reason why I'm not calling or chatting you so as to forget you, amma kaman kullum kara mun sonki akeyi Ilhaam, I love you Ilhaam" ya fada sincerely, kasa cewa komai tayi kawae tana tsaye tana jin yanda maganan Anwaar ke mata yawo, ga yanda heartbeats in nata yaki tsayawa dai-dai, she know she can do anything but she just can't hurt her brother, she just can't, a hankali ta zame hanunta, zata wuce yayi sauri ya sake riko hanunta "I love you Ilhaam" ganin hawayen dake sauka daga idonta daya na bin daya yayi hugging nata, lumshe ido yayi jin yanda gashin kan Ilhaam ke fitar da kamshi mey dadi, itama kamshin turaren duk ya cikata, da sauri taja da baya ta hanyar raba jikinsa da nat "Enough" Ta fada adan tsawace, itama saida tayi mamakin kanta "Im not ready for this Anwaar" Ta fada sai kuma ta fashe da kuka, kokarin sake hugging nata yayi sai dai kafin yayi hakan tasa hanu ta dakatar dashi "Ilhaam believe me you can do this there's absolutely nothing wrong in falling in love, and that too with me? I promise to never hurt you"
"Anwaar you're saying this now, and you will fall out of love one day"
"Ilhaam you've to believe me, I'm nothing of that sort" yayi assuring nata "Is that the reason you've been avoiding me Anwaar? Don't you have the courage to face what you love?"
"Ilhaam I've the courage and confidence" ya fada kaman zaiyi kukan shima, ganin ta fara girgiza kai yayi saurin hugging nata gam-gam saidai to his surprise sai ta zagaye hanunta a bayansa suna shakan kamshin jikin juna, ah hankali sautin kukan nata kuma ya ragu, dagota yayi ya share mata hawayen nata duka "Look Ilhaam, I can't force you to love me but please don't stop me from loving you" yana fadin haka ya durgusa putting his knees down. Su Anwaar an iya soyyayyah ashe.



Where Are the Anwaar fans? This page is yours💖

I'm not a Writer😄 just trying.

#RDN!

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now