💖💫RUDANI💖💫 91

54 23 82
                                    


Dan tsayawa tayi ganin yanda ransa ya mugun 6aci "Out of my room" ya fada sannan ya mata nuni da kofa dan baisan ganinta kuma "I know I've wronged all of you but please ku yafemun, I did that out of love" wani murmushin takaici yayi "For how long will you keep deceiving me Fatima? Ni na miki laifi ba Ilhaam ba, why her? Laifin mey ta miki?" Ya tambaya curiously "Im sorry Anwaar, it was a mistake wlh" ta fada tana kuka "It was never a mistake, you did that intentionally Fatima. Nima na rasa laifin mey na miki kuma, sanki kawae na fara. I love you for you, for your personalities, amma ke makaryaciya ce, duk abunda kike nuna mun ba haka yake ba. May our paths never cross again because I despise you now" kuka sosai ta fara ganin yanda ta mugun wasa da damanta, tunda Anwaar ya kece yana santa bata ta6a gaskata hakan koh ta gani idonsa da gaske ba sai yau "Where is Fadel?" Ya mata tambayan da batayi tsammani ba "I promise you Fadel is your son Anwaar, Munnirah just misunderstood the whole situation. Yes, I told Ahmad that Fadel is his son to make him dance to my tunes. But Fadel is yours and you alone Anwaar" ta fada da regretting komai na rayuwanta "Karki sake sa Fadel cikin shirmen ki, na fiki sanin Fadel yarona na ne" ya fada kuma tana iya ganin kalan tsanan da Anwaar ya mata "So what I don't understand here is why do Ahmad have to accept Fadel?" Zuru-zuru ta farayi da ido ba amsa sai hawaye "Wani abu ya taba shiga tsakanin ku ne?" Ya sake tambaya but this time a tsawace ganin ta tsaya b'ata masa lokaci "Im sorry Anwaar, but I can't lie to you" wani kallon mamaki ya fara binta dashi "What do you mean?" Ya daka mata tsawa "Sorry but yes" ta fada sincerely hakan yasa ya tsaya kallonta kawae hawaye na zuba mishi shima, dama chan yana fama da kukan lamarin Ilhaam toh ga wani kuma "I'm sorry Anwaar but it was once and he insisted, he threatened to reveal my secrets" ta fada tana kuka sai kuma tayi saurin durgusawa, ganin Anwaar na tsaye kaman statue baice mata komai ba yasa ta mike ta k'arasa gabansa "I love you Anwaa-" bata karasa ba ya dauketa da wata gigiceccen mari "Who do you think you are Fatima? Da auren nawa akanki kika aikata irin wannan abun? Despite all the obstacles da kikayi creating tsakani da Ilhaam bai isheki ba? You are a polytheist (Mushrika) tunda har wajen boka kike zuwa, and now Zina? Im sorry, amma bazan taba iya cigaba da zama dake ba Fatima, you are a demon" kuka sosai takeyi dan tama kasa magana "NA SAKE KI SAKI DAYA, BIYU-" kafin yace uku tasa wani rikiceccen ihuuuu ta fara tsalle hakan yasa yayi shiru "Banisan sake ganin ki har karshen rayuwata, I hate you" girgiza kai takeyi tana tsalle "Nooooo" ta fada sannan ta durgusa zata fara aikin kuka ya fita ya bar mata dakin. Yana fita yaga Ilhaam dan zata shigo basa haquri kenan taji yayi saki "Anwaar please-" bata karasa fada ba ya wuce abunsa hakan yasa ta shiga dakin ta samu Teemerh yanda ya barta sai kuka takeyi, samun waje tayi ta zauna ta fara kallon Teemerh "Yanzu burin ki ya cika?" Teemerh ta tambaya, kallonta Ilhaam ta cigaba dayi with unreadable expressions, kala-kala kawae dan sun hadu sun mata yawa, ganin yanda Teemerh ke kuka yasa jikin Ilhaam sanyi, tashi tayi ah nitse ta karasa wajen Teemerh ta kama hanunta "Let go of my hand Ilhaam" ta fada da muryan kuka amma kin saketa Ilhaam tayi "I said let go of my hand" ta maimaita ah tsawace "Kiyi haquri" Ilhaam ta fada tana hawaye itama "I am sorry, Anwaar is too, kawae fa ya rasa hukuncin dazai baki ne" jin hakan yasa ta yarda ta tashi, zaunar da ita Ilhaam tayi sannan ta zauna gefe "Forgive me Ilhaam, wlh nayi nadama" ta fada tana cigaba da kuka dan yanda taga Anwaar ya saketa komai tsayawa yayi "You are forgiven Teemerh, Allah ya yafe mana" kukan kawae Teemerh ta cigaba dayi dan ta kasa tsaidashi "Ilhaam gaskian kine Anwaar bazai taba sona ba" ta fada tana kokarin share hawayen "Im wrong Teemerh, Anwaar yana sanki" saurin kallonta Teemerh tayi tana cigaba da kokarin wiping tears nata, tasan Ilhaam nasan comforting nata ne yasa tace haka, amma bazata bari Ilhaam tayi deceiving nata ba, eh yana santa kuma ta yarda, abunda ta dade tana jira amma wlh taga irin tsanan da Anwaar ya mata "But he hate me, he just said it" ta fara ma Ilhaam bayani "Halin kine bayiso" Ilhaam tried her best consoling Teemerh "Na yarda yana sona amma yanzu ya sake ni. I know this will be my fate one day saboda na cuce ki Ilhaam" Teemerh da ta fara accepting reality ta fada "No don't say that Teemerh please, nima akwae nawa laifin, both nida ke bamu yarda da kaddara ba, tun farko dana yarda cewa kowa da kaddaransa kuma ni yazo a nawa dole ah mun kishiya da duk haka bai faru ba. Ji nake I am the only one that deserves Anwaar's love and no one bayan ni. Ke kuma da kin cire believe na cewa in Mummy bata zauna da kishiya ba kema baza ki zauna da ita ba, da duk haka bai faru a rayuwan mu ba. Once upon a time, we were both Anwaar wives Teemerh. But look at us today ba wacce take da auren sa akanta" shiru Teemerh tayi jin Ilhaam is making sense "You are right Ilhaam, duk munyi kuskure but I don't know if I might have a better chance than this, congratulations Ilhaam, you are the one for Anwaar, abunda na kasa yarda yau na yarda wlh, nasan dole ke Anwaar zai maidaki. This is a game of love and I am defeated and shattered" kawae ta daura hanu akai "Kema zai mai dake Teemerh da yardan Allah" Ilhaam ta fada cike da tausayin Teemerh, she finds it hard saying it amma ta fada, barin kukan Teemerh tayi tana so ta tabbatar ba aljanu jikin Ilhaam jin abunda tace "Ilhaam karya kikeyi wlh, nasan bakiso Anwaar ya maidani" Ilhaam hummed "Fatima try to understand me please, banida daman da zance kar Anwaar ya maida ki fa, kuma banida daman cewa yayi" shiru Teemerh tayi ta cigaba da kuka, Ilhaam dai na gefe batace ta bari ba "I want a heart like yours Ilhaam" tana kokarin hugging Ilhaam Ash ta ja Ilhaam dan shigowan ta kenan kuma bazai yiyu ba "Na tausaya miki Teemerh, amma wlh nayi farin ciki da abunda ya sameki" Ash ta fada sannan ta sake hanun Ilhaam ta zauna kusa da Teemerh "Wani lokaci sai kaji zafi, ka shiga bakin ciki kafin ka gane abunda wani yakeji, if Anwaar and Aameer can hate you who are we?" Samun waje Ilhaam tayi ta zauna ganin wae Ashphert ke kuka, that too dalilin Teemerh "This is my vengeance, Anwaar avenge this for me. The Muhammads are the most peaceful creatures I ever met, I am fighting Anwaar for no reason but he is good, his mistake was marrying you Teemerh. I am misunderstanding Aameer for no reason too because he was siding you. I hate to say they hate you but they did. Indai Aameer zai tsane ki toh duk duniya ma sai sun tsaneki, Aameer is everyone's favorite" tana fada Ilhaam ta fara nodding kai tana hawaye, Aameer is her favorite being, he is so good "We are sorry indai mun tab'a cutar dake, forgive us please, amma dan Allah stay away from my family Teemerh" Ashphert ta roketa hakan yasa Teemerh barin kukan tana kallonta, ganin da gaske Ashphert keyi ta kalli Ilhaam, kauda kai Ilhaam tayi ta fara share hawayenta dan abun sunyi yawa "Am I this bad?" Teemerh ta tambaya disturbingly "I don't know" Ashphert na fada ta tashi taja hanun Ilhaam dan su fita, they need to heal. Suna fita kuwa tayi wajen Ummi ita kuma Ilhaam ta koma daki, Anwaar ta gani rikeda Baby ya gama mata hud'ubar, batasan mey yayi ba, shiyasa bata tambayi sunan ba ta karasa wajen nasu ta dugursa daga kasa "Ka yafemun, for all the blames, the accusations and everything, nifa duk na zata san Teemerh kakeyi shiyasa abunda suke faruwa duk suka faru, na kasa yarda cewan obeying Ummi kayi, I love you Anwaar and I went blind doing so" ajiye yarinyar yayi ya kama hanun Ilhaam ta zauna gefensa "Marrying Fatima was under Ummi's behest but never my wish, choice or everything, I obeyed Ummi shiyasa nayi auren, no way am hurting you Ilhaam daga auren mu nace zan sake wani, you know I had no intention of keeping a second wife and Aameer told you this number of times. I love you and you alone, but Fatima? She was good and kept yearning for love, I love her for who she was and what she showed me, she was a saint in my eyes, na zata kishi kadai yake damunta, but why? She broke my heart" kasa share hawayen Ilhaam tayi ta bari yana zuba "We all are wrong Anwaar" kallonta yayi jin dalilin fadan haka "I know you tried your very best to deal justly between me and Teemerh, kayi abunda zaka iya sannan ka kwatanta adalci yanda ya kamata da kuma yanda zaka iya, amma ka kasa boye irin san da kake mun Anwaar. Fatima is a human and has a heart too, dole zataji ba dadi and that will trigger her tayi duk abunda tayi ma. She wants love, she yearns for love but in the wrong way. She is wrong and we are too" ta fadi last sentence in dakyar tana kuka, Anwaar shi bai damu ba, abunda yasani guda daya shine Fatima ta cutar da mutane dayawa, shi ya mata laifi shi kadai tunda duk akansa tayi, amma tayi hukunci harda wanda ba ruwansu, kuma abunda Ilhaam tace is not an excuse da zai sa Fatima yin abunda tayi "I can't love my wives equally Ilhaam, you can take all the 100% and she will take 10 from it. I can't and I would never force myself to" yana fada ya tashi dan yanzu he has nothing to do with Fatima.



💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now