💖💫RUDANI💖💫 64

84 25 87
                                    



_Ummi's Home_

"Ina yini Ummi?" Ilhaam ta gaidata da murna "Lafiya lau an yini lafiya?", "Lafiya lau Alhamdulillah" Anwaar ya amsa "Amma dai kaman ba yau na dawo ba koh?" Ta tambayesu "Uhm Ummi Ilhaam taso zuwa tun da wuri nine ban bata izini ba saboda na fiso muzo tare" ya mata bayani "Yanzu mace ne zata shiga tsakanin mu?" Kallon mamaki duk suka mata, Ilhaam kam kasa cewa komai tayi "Ummi Ilhaam ce fa, Ilhaam your daughter, she will never think of something like that, you raised her" ya defending Ilhaam "That was then, yanzu ta zama wani abu daman ita take saka ita take hanaka ae inajin labarin komai, toh ta Allah ba taki ba" Kuka sosai Ilhaam tasa ba shiri ta mike tai waje daidai ta shigowan motan Ashphert, ganin Ilhaam da tayi itama ta fito motan ba shiri tayi wajen Ilhaam "Ilhaam dan Allah kiyi shiru Ummi ce koh?" Kasa bata amsa Ilhaam tayi sai kuka "Barinje in dawo" nan Ashphert ta mike ta shiga ciki "Toh nidai na fada maka, indai kan matan kane zamu samu matsala sosai" Ummi dake fada ta cigaba dayi "Kiyi haquri Ummi amma Ilhaam batada laifi ah cikin maganan nan" ya mata bayani "So you're still backing her right?" Ummi ta tambayesa "Ummi meya faru?" Cewan Ashphert kenan da ta shigo ta samu maganan "Ina ruwanki?" Anwaar yayi saurin tsaidata "Da ruwanta mana, yau na dawo?" Ta tambayi Ashphert "Aa kin dan kwana biu" ta fada hade da samun waje ta zauna "Toh sai yau Allah yayi matanshi ta yarda suzo su dubani akan mey bazanyi fada ba?" Ummi ta zage "Ummi nima fa yau nazo gashi sun ma rigani zuwa, to akan mey zaki takurawa Ilhaam?" Ashphert ma ta goyi bayan Ilhaam "Oh kema goyan bayan nata kikeyi?" Girgiza kai tayi "This is not a situation where za'ace ina bin bayan Ilhaam or not, gaskiya nake fada gashi tana chan sai kuka takeyi"... "Tayi kukan jini" Ummi ta fada cikin I don't care tone, Anwaar ne ya tashi zai yi waje ta dakatar dashi "Koma ka zauna saboda ance tana kuka shine ka tashi ka rarrasheta koh? To tayi kukan jini babu yanda zakaje saina gama" ba musu ya koma ya zauna "Ummi Ilhaam is my responsibility inaga ya kamata nayi abunda yafi haka" ya fada bayan ya zauna "Is Fatima not your responsibility?" Ta tambayesa "She is" ya amsa mata "So why do you care for Aya more than Fatima?" Shi ya rasa meyasa yanzu maganan Ummi duk kan Fatima fa "Ummi ki daina haka" Ashphert ta sa baki "Har yaushe ne zaki daina hada Ilhaam da Teemerh? Ummi Ilhaam ke kika raineta tare fa kika rainemu, the difference is kawae bake kika haifeta ba and baki shayar da ita ba ni kuma kin haifeni kin shayar dani, then why are you putting so much pressure on Ilhaam? Inda erm Aunty right?" Ta tambaya tareda cigaba "Inda Maman Ilhaam na raye zataji dadi yanda kike nuna banbanci tsakanin 'yarta da kishiyar ta ne? Kema bazaki fara yin hakan ba amma saboda kinsan Ilhaam has no one to call a mother shiyasa kike fitar da halaye kala daban daban. To let me tell you something, in dai zaki cigaba da yiwa Ilhaam hakan then congratulations you lost me saboda am just like Ilhaam, ita 'yar uwatace bazan kuma iya rabuwa da ita ba. I love Ilhaaam very much kuma itama tana sona amma ke mey kika tabamun da zan yarda cewa you're a mother? Kullum damuwan ki shine a gabanki bakisan...-" ae bata karasa ba taji tassss saukan mari a fuskanta, kafin ta ankara ta sake jin daya tana daga kai taga Anwaar ne ya bata wannan slaps in "Damn these words, how dare you?" Ya tambayeta "Toh..to...toh ae duk abunda na fada gaskine" ta fada da muryan kuka nan ta juya ta basu waje. Koh da ta fita batayi kan crying Ilhaam ba ta shige mota ta cigaba da kukan nata, bata jima ba taja mota fiiiiiii tabar compound in. Koda Anwaar ya fito ah cikin mota ya tarar da Ilhaam tayi kukan har ta gaji, bece mata komai ba yaja mota sukayi gida., suna isa ta fita da gudu tayi ciki, ah daki ya sameta tana zaune tayi shiru "Look IIhaam" hanu ta daga masa alamun ya isa "Look what Anwaar? Do you want to tell me bayana zaka bi? Or do you want to say Ummi tayi kuskure? Duk ciki babu wanda zakayi saboda haka ba ampanin magana, Ummi is a mother and duk abunda tayi daidai ne bai kamata muyi challenging nata ba. But she is not my mother anymore, I married her son shiyasa take haka, she's a MIL and they can do worst"..... "Ilhaaam!!!" Ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta a tsawace "I am sorry" ta fada ah hankali sannan ta tashi ta shiga toilet domin wake fuskanta, wanke fuska tayi ta dauro alwala koda ta fito bayi nan, batayi mamaki ba ta shimfida abun sallah tayi.

💖💫RUDANI💖💫Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin