💖💫RUDANI💖💫 20

216 45 11
                                    




Da dare an shirya amare tass an musu kwalliya domin yin event na karshe, sunsha kyau Masha'Allah, Ilhaam light makeup akayi mata amma hakan bai hana kyaunta fitowa ba, ackin gida ne za'ayi saboda ba wani dadewa za'ayi ba, kuma decoration in da akayi yayi kyau sosai, an zurfafa cikin shagali an sake waqa Ilhaam tana gefe taqi yin rawa, Anwaar koh bayi nan, an kira Xeenerh da Ashphert suyi rawa tare da mazajen su da ikon Allah Aameer yaki tashi, badan komai ba kuwa sai dan Ilhaam da tunda aka fara ya kula she is not her absolute self "Aameen is this a dinner?" Xeenerh ta tambaya Aameen kasa-kasa dan kuwa ta rasa miye sunan wannan events saboda kuwa su Yaa Humainah ne suka hada "I don't actually know, I pray a gama da wuri"
"It's suffocating, wai su wannan abun al'adan bayi karewa ne" Xeenerh ta fada tana dan bata rai, Ashphert kam dana a dole take komai dan kuwa bata fiye san shirme yayi yawa ba, su Yaa Humainah sune masu rawa sai kudi ake zubarwa, liqi iya liqi anyi shi, su Auntie Khadie kuwa anfi karfi ta wajen zuba kudin dan kuwa bata wani iya rawa ba, koh da sukayi ma Ilhaam magana sharesu tayi dan harynzu ba shiri sukeyi ba, da suka dameta da magana cewa tayi karsu dameta she know what's good, Yaa Sabeerah ce ta jata gefe "Ke yanzu Ilhaam rayuwar rashin kunyan da kuka dauka wa kanku ya muku dadi kenan? Gashi su Ashphert aure zasuyi zasu fara ganin rayuwar aure ba daya yake dana gidanku ba komin soyyayyah" tsayawa kallonta Ilhaam tayi, ita gani take karya tayi aure ta shiga matsala "Toh sai kiyita goya musu baya Aunty, baku tab'a ganin fault nasu sai namu, whatever the situation basu isa su rabamu da en uwan mu ba" ta fada tana wani bata rai, ita koh an tambayeta bacin tan mey takeyi fa ba sani tayi ba "Toh haka kikace? Ilhaam sai randa kikayi aure zaki gane mey nake nufi" dariya ma maganan ya bawa Ilhaam"Aw yanzu Aunty so kikeyi nashiga matsala in nayi aure kenan?" Ta tambaya jin abunda Yaa Sabeerah tace "God forbid ban taba miki fatan haka ba Ilhaam, toh yanzu koh liqi bazakije kiyi musu ba?" Tace "Nayi liqin dazu, yanzu kudin hanuna yayi kasa" still dai bawani walwalan kirki tattare da ita "Toh barin baki" wani pochette nata ta ciro zata bawa Ilhaam kudi, saidai kafin ta kaiga cirowa sukaga an kashe waqan da sauri kowa ya daga ido dan ganin meke faruwa, lights in gabadaya aka kashe "Oh noooo" Ilhaam ta fada tare da dan buga kafa ah hankali "Kinga abunda nake fada miki Aunty, saida nace indai dinner ake da niyyan yi a tafi hall amma kunki, gashi workers naku basu iya aiki b-" kawae sukaga lights in ya dawo sai ga waje wide open Anwaar da Teemerh sun shigo sunsha kyau sosai domin daga airport da kanshi ya daukota sukayi wajen fashion designer ta shiryata, mutuwan tsaye Ilhaam tayi dan ta rasa mafarki ne koh kuma gaskia, Ashphert dake zaune a gujeran Amarya saida ta miqe tsaye, Ilhaam zata karasa wajensu Aunty Sabeerah ta riqeta, juyowa tayi ta kalleta sai ta kad'a mata kai alamun kartaje, fauce hanunta tayi ta karasa wajen nasu saiga en jarida sun iso "Who invited you? As far as I know banyi inviting naki ba so now out" ta nuna mata kofa "Securities??" Ta kirasu saiga su sunshigo, d'aga musu hanu Anwaar yayi alamun su dakata "Ba yanda Fatima zataje, saboda ni nayi inviting nata so you've no right to send her out" Haba sai cameras ta koh ina, Aameer da sauri ya taso ya riqe Ilhaam tunda ganin abunda ke faruwa "Aameer let me be, kabarni" ta fad'a tana kokarin kwace hanunta saidai yaki saketa "Dr. Anwaar mey zakace gameda abunda ya faru yanzu?"Tambayar wani dan jarida, ignoring tambayan yayi yace "Y'all should meet my future wife, Fatima" ya kama hanunta tareda d'agawa sama kaman yanda suka shirya shida Teemerh, wai fa ita ta dage taimakon sa takeyi, sai ihu kawae ke tashi a wajen Ilhaam kuwa sai hawaye, ita damuwanta wae in zasuyi auren nasu ma sai sun fad'awa duniya, Xeenerh da Ashphert takaici ya musu yawa "Greetings everyone" Teemerh ta gaidasu"Greetings" sai waje ya amsa "What is the wedding date Dr.?" Wata ta sake tambaya "We haven't decide yet but soon" ya bata amsa "And Ilhaam?" Ta sake tambayar "What is she to you?"
"Ilhaam is my sister and she will always be"
"Dagaske ne kun taba soyayyah da Ilhaam?" Kuka sosai Ilhaam ta fara tuni ta kwace hanunta tabar wajen, Aameen ne ya kori en jaridan yace su tafi they're not needed, da kyar suka tafi saboda naci irin tasu, haushi na hakika Ashphert taji, tasan sarai Anwaar bazai tab'a auren Teemerh ba har abada saboda Teemerh bata ma daya daga cikin jerin matan da Anwaar kesan aura, na d'aya yawo ya mata yawa, na biyu rawan kai, na goma surutu, tashi tayi tabi bayan Ilhaam, Xeenerh ma tashi tayi ta bisu, Teemerh kuwa farin ciki fal ranta kaman ta zuba ruwa ah kasa tasha takeji, haka dai ba'a gama so called dinner nasu Yaa Humainah ba ya watse "Babe, sisters naka basu kaunata koh kadan" ta fad'a tana kad'a hanu tana rarraba ido, baice mata komai ba ya karasa wajen su Shareef hakan yasa ta bisa "Ina yini" ta fad'a ganin su duka "Lafiya qlau" suka amsata in unison "Nifa banga Ahmad ba" Shareef ya fad'a yana sake dubawa "Nima banga Sarah ba" ta chapke kaman an tambayeta, dariya Aameer ya fara sanin dama Sarah ba zuwa zatayi ba, he was supposed to marry her ah yanda take shiryawa akanta "Barrister baka kyautawa" Aameen ya tsaidashi "Kai kuma ina matan ka?" Yayi nuni da Shareef "Toh yau dai batazo ba, halan sai wani lokaci" ita Teemerh ganin ta gama bata musu event yasa tace "Babe toh dare fa nayi" Anwaar da tun dazu ya musu shiru mamaki ta basa ma, tasan dare nayi tace masa tanasan attending "What are you trying to say Fatima, bazaki shiga ah karasa hidima dake ba?" Aameer ya karbesa "No, kuna ga dai sisters naku ba sona suke ba, bansan mey na musu ba, zaifi kyau ina distancing kaina" murmushi kadai Shareef yayi "Sai ki nemi mey maida ki gida" Anwaar na fadin haka ya barta nan tsaye yayi tafiyansa, murmushin dole kawae take amma ita tunda aka haifeta bame mata abunda yaga dama ta kyalesa kaman Anwaar "Muje na sauke ki" Shareef ya fada ganin abunda Anwaar ya mata "Aa Shareef, ban takura maka ba?" Yace "Aa, saidai in ba yanzu zaki tafi ba" tace "Aa yanzu zan tafi, amma banyi wa Anwaar sallama ba" Aameer sigh "Yanzu ke Teemerh miye guda daya matsalanki? Yin dare koh sallama wa Doctor?" Shiru tayi tana tunanin wanne zata zab'a chan tace "Shareef muje toh" Aameen yace "Yanzu sai yaushe kuma?" Murmushi tayi hakan yasa tayi kyau sosai "Very soon" ta bashi amsa sannnan tayi gaba, sallama Shareef ma ya musu ya wuce, Su Ash kuwa anata aikin kuka, chan Aunty Husnah tace Amare su fito, su dasuke dakin Ilhaam sun hadu sai taya Ilhaam kuka suke gashi ance su fito sai kuka ya karu, su kukan barin Ilhaam ma sukafi yi, Yaa Ateekah ce ta shigo dakin da sauri yarinyan ta na biye da ita "Zə̀ptə́" (Sauka k'asa wajen Munnirah) nan yarinyan ta chanja hanya "Toh yanzu Ilhaam ke da zaki encouraging nasu sai ki zauna tare dasu kuyita kuka?" Ganin sun shareta tace "Toh ga Ummi zata shigo fa" Sallaman Ummi ne yasa tayi shiru "Sannu da zuwa Ummi" ta fadin ganin ta karaso "Yawwa ku taso anata jiranku kunzo nan kun maqalle, Aya kiyi haquri, bawai kun rabu kenan ba kinji" tabawa Ilhaam haquri, ita duk ah zaton ta kukan rabuwa dasu Ilhaam take sai kuma ta samu waje ta zauna "Kaman yanda na muku nasiha shekaran jiya baya toh yanzu ba lokaci, ba shi zan muku ba, inaso duk abunda na fada muku ku riqeshi kuyi aiki dashi kubi mazajenku banda raini ah karkashinsu kuke yanzu, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya muku albarka" nan Ateekah ta amsa da "Amiin" saida su Humainah sukayi da gaske kafin amare suka fito ah private jet na Baa zasu tafi daman, su Xeenerh zasu New York su Ashphert kuma Paris zasu, Ilhaam kam cewa tayi ba yanda zataje, Humainah tace bata isa ba ta raka Ashphert ita da Ateekah, ita da Sabeerah kuma zasu NY (New York) "No Yaa Humainah I prefer going to New York, bazanje Paris ba" tayi maganan kaman mey shirin sake kuka "Chan zakije Ilhaam, bawai shawaran ki nake nema ba" Ilhaam kuwa saboda Aameer ne daman taki zuwa amma tasan Paris sosai, so in the flight, Ashphert tana zaune tare da mijinta saidai bata dago ba, Ilhaam na zaune da Aunty Atee suna facing juna sai shawari Aunty Atee take bata saidai hankalin Ilhaam sam ba'a jikinta yake ba tunanin irin yaudaran da Teemerh tayi mata kawae takeyi bayan nan bawani abu akanta, tafiyan 6hr 16mins ne ya kaisu Charles De Gaulle International Airport dake France, Paris, sun isa lafiya, Yaa Ateekah tace su shiga taxi kawae tunda Asuba ya kusa kar lokacin sallah ya wuce, nan fa Aameer yace Aa akan wani dalili zaice wa Driver'n sa yau zasuyi landing kuma yaki zuwa, daukan waya yayi saidai kafin ya kai ga kira yaga Victor hakan yasa ya fasa, haquri ya basa ganin yanda ran Aameer ya baci "Désolé je suis arrivé en retard" (Sorry, I arrived late) Victor ya fada "Ferme ta gueule et ramène nous à la maison" (Shut the f*ck up and take us home) Aameer ya fada saidai bada fad'a ba, a nitse yayi maganan "Laquelle des maisons monsieur?" (Which of the houses Sir?) "Celui du 7e arrondissement" (That of the The 7th arrondissement) ya fada sannan yaja karamin tsaki ganin shirmen da Victor kesan masa gaban Yaa Atee, wai fa dan ma bata fahimtar French sosae, jin ya ambaci 7th arrondissement ne ya sata kallon sa "Aameer what are we doing in the 7th Arrondissement?" Ta tambaya da mamaki dan kuwa tasan gidan Aameer na Neuilly-sur-Seine "Erm.. Aunty muje, I will explain this later" ya fad'a sannan yayi saurin karasawa wajen mota ba tare daya tsaya jin mey zata sake fada ba, Ilhaam da Ash na gefe sai dariya sukeyi kasa-kasa, ganin Aameer wajen mota yasa duk suka karasa wajen "S'il vous plaît conduisez vite" (Please drive fast) Aameer ya fada bayan sun shiga dan kuwa Asuba yayi "Bien sur monsieur" (Of course Sir) Victor ya amsa, tafiyan 15 minutes ne ya kaisu gidan Barrister Aameer dake Rue St-Dominique, gida ne babba, paint in duka white, wrought iron gates, wrought iron railings da entrance door ne kawae black, bude wrought gate in yayi suka shiga, nan duk suka fara bin gidan da kallo banda Ateekah dake girgiza kai kawae dan kuwa gidan bene ne, fita sukayi a motan yanda Victor ya karasa dashi cikin wani garage mey windlesham electric gate, shima fari, ba abunda yake haska wajen sai front porch lights, shiga ciki sukayi a nitse as it's just a wow, katon palo ne mey dauke da wooden sofa sets, ba abunda babu cikin wannan waje "Your rooms are upstairs" Aameer ya fada sannan yayi sama, girgiza kai kawae Ateekah tayi ganin yanda kudi yayi magana cikin gidan "Kaita dakin Ilhaam, kya fito daga baya kiyi kallon gidan" Ateekah ta fada ganin Ilhaam ta kama hanya zatace wasa ido, da toh ta amsa sannan ta rike Ashphert ta kaita har daki, Yaa Ateekah kuwa daki ta wuce itama domin watsa ruwa, suna shiga Ilhaam ta juya zata fita Ash tayi saurin riketa "Ki zauna anan mana"
"Sallah zanyi nayi wanka kar lokaci ya kure" Ilhaam ta fada a nitse "Okay, nima sallah zanyi" ta fada sannan ta mike tayi toilet while Ilhaam ta fita, daki opposite dana Ashphert ta shiga, alwala ta fara tayi sannan tayi sallah, bata tashi ba saida tayi Adkhar sannan tayi addu'a wa en uwa musulmai, wanka tayi sannan tazo ta kwanta




******
******
********
You might see fragments of yourselves in this book. Always remember that you can be Ilhaam, Ashphert, Teemerh, or Xeenerh- it's always a choice to be good💖💫

PS: I'm not a writer, just writing RUDANI as it is one of the books I want to read but it has not yet been written

#RDN🤍

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now