💖💫RUDANI💖💫 7

286 56 11
                                    




Dakin Ilhaam ta nufa, knocking tayi da kyar Ilhaam ta bude kofan ganin Xeenerh tayi saurin hugging nata very tight, da kyar Xeenerh ta iya rabasu nan ta shiga dakin "Ilhaam dan Allah kibar komai ya wuce, Yaa Atee is here she might sense something is wrong" ta fada kaman zatayi kuka dan Ilhaam ta bata tausayi "Xeenerh am hurt to the extend that I won't be able go further" ta fada hawayen na cigaba da zuba "No Ilhaam you can, be the Ilhaam I used to know, be the Ilhaam I used to know in the past, be our courageous who is weak but never show it" Kai kawai Ilhaam take kadawa alamun baza iya ba, not anymore tana wani kuka mai tsuma rai, jawota Xeenerh tayi suka zauna akan couch dake dakin "Ilhaam idan har zaki iya daina san Anwaar then who's Aameer?" Da sauri ta dago ido ta kalleta "Yes Ilhaam, idan har zaki daina san Anwaar toh Aameer is nothing compared to him" ta fada danta convincing Ilhaam tabar damuwa "Yes, Aameer is incomparable to Anwaar that is the reason I love him so much, Xeenerh how can Aameer stood so low?" Ta fada hawaye na zuba "Ilhaam dan Allah kiyi shiru, you know? Ashphert tana sonshi sosai saboda batasan keda Aameer kuna dating ba remember?" Kai Ilhaam ta gyad'a alamun Eh "Kinga inta sani this will hurt her feelings, zataga kaman itace tajawo miki komai da kike ciki yanzu"
"Ashphert will know nothing about this, and I wish them a successful married life" tana gama fadin haka ta shiga share hawayen amma yaki tsayawa "Kinsan abunda ya faru?nasan Aameer ya miki laifi bawai kuma inaso na kareshi bane amma-" nan ta zayyane ma Ilhaam abunda taji a daren "I made a mistake Xeenerh"
"I accused him wrongly, amma meyasa bai fada mun gaskia ba? I know that I love Aameer, amma farincikin 'yar uwata ya fiye mun komai" nan ta fashe da kuka ta rungume Xeenerh, Xeenerh kam mamakin irin halin Ilhaam takeyi, She can sacrifice everything for her love ones, most especially Ashphert, Ilhaam nasan Ash sosai "Ilhaam has a big heart, Indeed" Xeenerh ta furta ah hankali

***
               ****
                                 *****

Ahmad kwance kan wani katon gado daga shi sai sleeveless shirt yana danna waya, abunda ya gani ne ya mugun basa mamaki at the same time yayi farin ciki "Yesssssss" ya furta sannan ya mike da sauri ya bude closet, yana cikin duba kayan da zai sa wata budurwa ta fito daga toilet "Babe ina zuwa haka kuma bayan bamu gama ba?" Wani kallon banza ya bita dashi "Na samu abunda ya fiki mahimmanci, why do you think yanzu kinada wani amfani ah wajena?"
"What do you mean?" Ta fada tana gyara towel nata "Im getting married soon" ya fada yana cigaba da abunda yakeyi, kallon mamaki ta tsaya binsa dashi dan duk duniya bata ga wanda ya raina mata hankali kaman Ahmad ba "To who?" Tayi karfin halin tambaya "To Ilhaam Albaaz" ya fada ba tare daya kalleta ba, wani shedanin dariya ta fashe dashi hakan yasa ya tsaya kallon ta "Kuma kana tunanin zata aure ka right?"
"Toh why not?"
"Ahmad kenan, ka gama lalata mun rayuwa, kuma kayi tunanin zaga dauko somone like Ilhaam a matsayin matan ka?" Ta fada tana pointing nasa "Maryam tunda bana karfi na miki ba ae da sauki, ke kika kawo kanki, then why are you blabbering?"
"Bakomai amma kasan ina sonka ne shiyasa na yarda na baka kaina"
"Ke kinga sauri nakeyi in kin gama abunda kikeyi ki fita ki barmun gida" yana fadin haka ya fita, direct gidan su Teemerh ya wuce abunsa
***

"Aameeerrrr!" Ta kira sunan shi dan ta shigo bata ga alamun akwae wani ah gidan ba "Lafiya kika shigo sai ihu kike wa mutane?" Munnirah ta fito tana fada rai bace "Ke kinga na miki kama da sa'arki balle ina magana ki amsa?" , "Toh waye sa'an naki ah gidan nan?" Munnirah ta tambaya "Aameer na nan koh bayi nan?" Tayi maganan tana dake juyawa koh zata gansa "Sun fita shi da Ashphert dazu" Munni ta fad'a ah takaice "Toh kenan gaskia ne?" Sarah ta tambayi Munnirah dan sake tabbatar wa "Gaskiya mai kuma?", "Is he really getting married to Ashphert?" Ta tambaya kaman mey shirin kuka "Gaskia ne mana" Munnirah ta fada sannan tasa hanu kan sofa ta dauko magazine ta bawa Sarah, kaman bazata karba ba sai kuma ta karba, Aameen & Xeenerh ta gani ana farko sai na biyu Aameer & Ashphert wanda hoton sune ah cover na farko, an rubuta The Albaaz set to wed boldly "Nooo this can't be amma Aameer ya cuceni" ta fada da karfin dan tama kasa yarda, wani dan dariya Munnirah tayi da har tayi tunanin Yaa Aameer zai aure ta "Amma kema Sarah from the very beginning kinsan fa Yaa Aameer ba aurenki zaiyi ba" Munnirah tayi stating sincerely, saboda tsantsan takaici kasa amsawa tayi ta fita tana kuka
**

Teemerh dai na zaune ta gama jin abunda Ahmad ke cewa amma bataga kaman plan nasu zaiyi dai-dai ba hakan yasa tace "Ahmad are you sure plan namu zai tafi daidai?" Teemerh ta tambaya dan kara tabbatarwa "Eh gashi kuwa ya fara tafiya, I told you Aameer bazai aureta ba and gashi kinga zahiri yanzu" ya fada very excited "Eh haka ne, amma zan raka Mummy Florida, kafin auren dai zanyi kokari na dawo saboda ayi komai dani"
"Narju 'an nashhadah" (Toh Allah ya nuna mana) dan dariya tayi jin yanda ya fada "Amin" ta amsa, dan yau tun tashin ta batayi bak'in ciki ba, tunda kuwa ta kira Anwaar ya yarda ya dauka toh tasan ya daina fushi da ita

      
           Anwaar's Room

Gaba daya unsual yake jinshi ya kasa sukuni koh kadan, ji yakeyi kaman  akwae abunda yake damun Ilhaam "But what's it?" Ya tambayi kansa, wata zucia na cemasa yaje ya dubata dayan kuma na hanashi, dan rabon daya shiga dakinta ya manta, chan kawae yayi deciding zuwa, knocking yayi ah hankali kuma a nitse wanda ya bama Ilhaam tsoro dan she can't think zata manta yanda Anwaar yake mata knocking, sai wata zucia tace mata "Don't deceive yourself, Anwaar bazae taba zuwa ba" Nan tayi karfin hali tace "Come in" Ahankali kamar bazai shiga ba kawai yasa kai ya shiga kaman an sashi dole, mutuwan tsaye sukayi duka ganin juna da sukayi a haka bayan long time, kamshin da dakinta yakeyi a kullum shine yau ma, maganan  da Ilhaam tayi ne ya dawo dashi daga tunanin da yake dan tabbas yasan wani abu ya sameta duba da yanda fuskanta ya nuna alaman tayi kuka amma he can't ask her "Mey ya kawo ka dakina?" Sai kawae ya wani dake saboda kar tace ya damu da ita "Banda daman shiga yanda nakeso kenan, wow" ya fada cikin muryansa mey sa nutsuwa "Eh bakada wannan daman Anwaar, ka rasa wannan daman har abada" ta fada muryanta na shaking dan kuka takeson yi, ga tsoron da takeji dan dama chan ba wanda take tsoro gidan sai shi "Wait calm down, I don't come to here symphatize with you but to make you go through the worst because you deserve it" ya fada haka kawae dan ya b'ata mata rai dan kuwa dazu wancan shirmemmiyan ta kira ta masa shirme wato Teemerh, dama chan ita ke tsara mishi abunda zaiyi wa Ilhaam, wasu zafafan hawaye ne taji yana sauko mata dan tasan Anwaar baiji labarin abunda ya faru da itaba ganin yanayin tane yasan akwae abunda yake damunta shiyasa yace haka "Even I don't like ur sympathy, akan ka tsausaya mun na gwamnace mahaukaci ya tausaya mun and now out of my room because I despise you and don't you ever show me ur face, just looking at you disgust me" ta fada a yayinda heartbeat nata ke beating faster "And that make us even, dan koh duniya zata hade bazan taba sonki koh respecting naki ba saboda wannan respect in ya riga ya gushe a idanuna and to tell you how worthless you're pets na Fatima sun fiki fahimmanci" ya fada kansa tsaye, ganin kaman zatayi kuka ne ya dauke kai saboda bey san kukan mace, most especially Ilhaam, in a duniya akwae abunda ta tsana toh shine taji Anwaar na kiran Teemerh, kasa cewa komai tayi sai hanu datasa tayi mishi nuni da kofa "OUT" Fitan kuwa yayi dan ya gama abunda ya kawo sa, dama shigowa yayi kawae dan ya tabbatar tana lafiya, kuka sosai ta fara, ashe akwae randa Anwaar zai daina sonta haryaji ya tsaneta? Allah kar yayi abunda bazai wuce ba amma Teemerh ta cuceta duniya harda lahira

   ASALIN LABARI


Follow and vote for the full gist. Flash back will be drop soon In Shaa Allah

I saw your messages Rookieymaamah😂🫶 Aameer dai bayida fans😂

Team#Anwaar

#RDN!

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now