💖💫RUDANI💖💫 45

112 23 28
                                    


Suna shiga daki Fatima ta fara kuka "Ke bafa kuka zakiyi ba" Habeey ta jata jikinta "Mey zanyi ya soni? Cin mutuncin Anwaar ya fara yawa ga wancan Ashphert in da batasan nayi farin ciki" ta fada sautin kukan nata na karuwa "Tun farko ae kene bakiso ayi abu ya wuce ba, in anyi magana kice bakison Anwaar wajen malamai, toh in boka bai saita miki shi ba waye zaiyi haka?" Pausing tayi ganin Teemerh ta fara share hawayen "You can't believe me in nace miki mun kai sunan Anwaar wajen malami kafin ya fara kula ki" saurin tashi jikin Habeey tayi "Anwaar? Yaushe?" Ta bata double questions lokaci guda "Wancan time in zuwan ki Jigawa kikace mun you are in love with wani Anwaar, amma bayi koh amsa gaisuwan ki, kin lura koh ganin ki baisan yi. Kin tuna?" Gyad'a kai Teemerh tayi dan ya kan yi wuya tayi magana ta manta "So shine na fadawa Mamana, randa zata koma Ekiti kan wani aiki na tuna mata, karshen zance ma dani akaje na bada sunan ki da nasa. Toh kinji yanda akayi ya fara kula ki in ma" shiru Teemerh tayi tana kallon Habeey, ashe duk abunda Habeey take mata tana santa sosai haka "Kinzo kina hauka wa wasu Mum wai bakiso sunan sa yaje wajen boka, jin ki kawae Mamana takeyi ae dan sunan shi ya dade wajen su" saurin hugging Habeey tayi "I am so sorry Beey, nifa duk zato na zaki zago ma kice kina san Anwaar, ashe kina sona tare dashi, am so stupid. Toh yanzu ya za'ayi Anwaar ya soni?"...... "Oho kuma yanzu kam, danshi wancan na Ekiti bata tare dashi tunda yaci mata kudi aiki baiyi ba" Habibah ta amsa "Koh dai ban zo cikin kaddaran Anwaar bane Beey? Kina ga sai an gama da wannan wancan ya taso, na yarda da cewan yanzu yana kulani and he is not finding me irritating amma bayiso na koh kadan wlh, Ilhaam kadai yake so".... "Banza kinzo cikin kaddaran tasa yasa kika ga haka. Ni yanzu Ilhaam in nakeso na gani" yamutsa fuska tayi dan ita dai tasan Beey tasan Ilhaam halan ta manta tane, fara neman waya Teemerh tayi, saida ta samu ta tuna da ta goge hoton Ilhaam da wanda sukayi tare kap wayanta saboda dan banzan kishi "Zaki ganta ae tunda biki bai kare ba, ana kaini wajen Ummi zaki ganta" tabe baki Habeey tayi "Tee ki kwantar da hankalin ki. Dole ma Anwaar ya soki" tana fada ta tashi zata fita sai kuma tayi saurin dawowa kaman ta tuna wani abu "Mallah tace na sake baki haquri wai ta kira ki kina mata bala'i taqi zuwa bikin ki. Sadiq fa zaki blaming danshi ya cewa Abba bazai zo ba dan ba'ayi hutun school ba. Shiyasa itama aka hanata" both Mallah (Malika) takwara akayi wa Mummy and Sadiq are Habeey's siblings "Ba komai" Teemerh ta fada cikin karfin hali dan yanzu tana cikin damuwa, Habeey bata sake ce komai ba ta fita dan ita batada damuwan komai ah duniya, saboda duk abunda takeso sai ta sameshi, ta bar Teemerh da tunanin Anwaar, wato shikenan bazai mata abu dan Allah ba sai an hada da bokaye, ita wlh Anwaar is her worst exprience, tunda uwarta ta haifeta Anwaar ne ke bata wahala


Ashphert yakai gidan sannan ya juya zuwa gida bayan ya zuba mata warning tabar neman fada dan bayiso ana fada. Koh ina shiru kaman ba kowa cikin gidan, dakinta ya fara dubawa yaga bacci take, ahankali yaja mata kofan ya fita zuwa dakinsa, wanka yayi yasa pajamas ya fita zuwa dakin Ilhaam, nan yayi bacci, taji shigowan sa sarai amma bata nuna alaman ta tashi ba, ah haka ta sake maida bacci, da asuba shi ya fara tashi yayi wanka da alwala yayi raka'atanil fajr sannan ya tashi Ilhaam ya wuce masallaci, ita har mamakin Anwaar takeyi dan she never thought he is religious haka saboda basu wani spending quality time tare balle tasani "Alhamdulillah" kawae ta furta for such a religious man, saida tayi raka'atanil fajr itama kafin tayi asuba, bayan ta idar tayi adkhar tunawa da in batayi ba sai sun kusa fada da Anwaar, ta dade tana addu'a kafin ta dau Qur'ani ta fara karanta shi cikin murya mey dadi da nutsuwa, bata dade da farawa ba Anwaar ya dawo, yaji dadin ganin tana karatu and that too his favorite Surah-Suratul Yusuf, murmushi yayi yasan Ummi and Mami, most especially Maa Laure sunyi kokari wajen ganin su Ilhaam sunyi karatun addini, baiso fita ba dan karatun nata ya masa dadi, amma sanin yanada abunyi yasa ya wuce daki cikin farin ciki, he just can't imagine life with this gem, kwanciya yayi ya lumshe ido kaman wanda baida abunyi, yakai 15mins kwance kafin yaji shigowan Ilhaam, tashi yayi ya zaune dauke da murmushi a fuskan sa "Morning" ya gaisheta kafin ita tayi "Ina kwana" ta fada bayan ta karasa "Hope you recited suratul Kahf as well?" Girgiza kai tayi alamun Aa tunawa da tayi yau Friday, kuma ita bata karantawa da Asuba normally saida Zuhr, ringing in wayansa ne ya hana su karasa conversation in "Lafiya qlau Alhamdulillah. Ina kwana Malam" Ilhaam can swear banda Ummi ba wanda Anwaar yake ma magana haka "Eh yau ne Malam" ya amsa dan Ilhaam bajin abunda Malamin ke fada takeyi ba "Amin, addu'a anayi fa, anjima zamu shigo ma da yardan Allah" ya fada kafin ya ajiye wayan "He is Malam Abdallah, one of our Islamic teachers from Maiduguri" ohh itafa tasan Malam Abdallah, dan kuwa kullum in anyi waya dashi koba da Anwaar ba duk wanda sukayi waya dashi sai ya tuna musu maganan addu'a, Malam Abdallah is the Malam everyone will be proud of having, yanada san jama'a and everything na mutunci yanada, full definition of mutumin kirki kawae in short "Baki karanta ba koh? Let's recite the first ten verses then" yana fadin haka ya sauka tabi bayan sa, chan prayer room suka nufa, dakin so calm da kamshi, praying mats ne shimfide wajen guda biyu, daga dan gefen dakin kuma wani book shelf ne mey dauke da Qur'ans, Hadiths, Fiqh, Bulugh Al-Maram, Sahih Muslim and Sahih Bukhari, Sunan ibn Majah, Sirah and every other Islamic books, Qur'ans guda biyu ya karasa ya ciro sannan ya bata daya suka zauna, tare suka fara cikin nutsuwa, ga muryan Anwaar so Masha'Allah, har sukayi first ten verses basu sani ba saboda yanda karatun ya musu dadi, karshe dai saida suka karasa surah, cikin nutsuwa ya daga hanu ya fara addu'a, ganin haka Ilhaam ma ta hade nata hanun, ita dai bazata ce ga abunda Anwaar ke roko ba, shi kuma addu'a yakeyi Allah yasa in anyi auren, Ilhaam da Fatima su zauna lafiya sannan Allah ya sassauta mata kishi, bayan nan yayi addu'a wa 'yan uwa musulmai, bayan ya idda addu'an ya juya ya mata peck a forehead "It's getting late, barin shirya" ya fada sannan ya mike dan kuwa gari ya waye, murmushi kawae tayi ta tashi, tunawa tayi yau ne fa daurin aure, girgiza kai tayi tanaso ta manta abun tayi kitchen ta fara breakfast, ganin zai iya saukowa anytime ta fara gyara wajen, tayi mopping tasa turaren wuta tuni yadau kamshi ba laifi an iya gyara waje kam, bata gama hada breakfast ba ya sauko hakan yasa ya bita kitchen, kujeran kitchen island in yaja ya zauna ganin akai take jerawa "Yanzu zan fitar dama" ta fada ganin ya zauna "Don't worry, the aroma won't let me" ya fada sannan ya bata wide smile, murmushi itama tayi tasan koh bayi dadi ba he always motivate her, Tortilla fish wrap, Vanilla French toast, Taco Quesadilla, Green smoothie sai iced coffee, Tortilla fish wrap in ya dau biyu yasa a plate "Let's eat" ya fada yana kallonta, karasowa tayi ta ajiye masala tea ba tare da ta zauna ba "Tea zansha" ta fada sannan ta zuba ah cup ta fita, kallonta kawae yayi yasan tunawa tayi zaiyi aure, shi kadai yana cin abinci yana lumshe ido, loving Ilhaam aside abincin yayi dadi, balle ace dan yana santa yasa yace abincin da dadi, yau ba'a yi gwaninta ba, tasa komai kadan-kadan hakan yasa yaji dadin cin abincin, guda daya yaci yasha iced coffee nasa ya tashi yasa mata Taco Quesadilla gefen Tortilla yayi sama, tana zaune gefen gado rike da cup in da har ah lokacin bata shanye ba ya shigo, karasawa yayi ya zauna gefenta yasa plate in kusa da ita "Eat something please"....  "Nifa banjin yunwa" ta fada sannan ta sake sipping tea "Toh zamu fita bakici abinci ba?" Ya fada sannan ya yanka yakai mata baki, ba musu ta bude bakin yasa mata, tanaci yana mata surutu kaman ba Anwaar ba harta koshi "Barin shirya toh" saida ya bata magani kafin, ita Anwaar ya dameta da wasu magunguna gashi bata isa ta tambaya ba sai rai ya baci, gashi ita dai tasan lafiyanta qlau. Bayan tasha tayi bathroom, fita yayi yakai cup da plate nata kitchen, gidan yanata kamshi, that is one of things he love about Ilhaam, kamshi. Fitowa tayi cikin bathrobe da towel daure akanta, zama tayi kan vanity chair, warware towel in tayi tuni dogon gashinta ya sauka gadon bayanta, nan tayi drying kan nata, ta shafa wannan ta shafa wancan har Allah yayi ta gama, khumrah da mulke jikinta dashi sannan ta karasa closet ta ciro wani swiss lace blue da touch in green tasa, dan light make up tayi tasa red lip stick, tayi kyau sosai looking so Masha'Allah, daura dankwalin tayi sannan tasa veil tadau handbag nata da slippers in Hermes, wani oud ta sake fesawa sannan ta fita, bayi palon farko hakan yasa ta karasa na biyu, yana zaune yana kallo harta karasa, jin kamshin turare yayi hakan yasa ya dago ido ya sauke su kan stunning Ilhaam dake sakar masa murmushi, kasa daga ido yayi akanta dan wani kyau ta kara "Anwaar mana" ta fada ganin kallon da yake mata "You look so takeaway, amma bazaki fita ah haka ba" dan sake kallon kanta tayi taga dai shiganta so modest, tashi yayi ya gyara mata yanda tasa veil in tare da rufe mata jiki dashi, itafa ta gane so kawae yakeyi ya bata mata kwalliya hakan yasa ta bubbuga kafa tayi gaba, murmushi yayi ganin abunda tayi yabi bayanta, a parking space ya sameta tana tsaye, baice komai na ya karasa ya bude mata kofan, ba koh kunya ta shiga dama jira takeyi ya bude ta shiga sannan in sun isa ya bude ta fita, zagawa yayi side nasa ya shiga ya kama hanunta ya rike dan yafi san hakan, nan suka fice, already fa Anwaar ya hiring securities as Ilhaam's suggestion, ringing wayansa ya fara, yana dubawa yaga Fatima ne, bai amsa ba saboda driving da yakeyi sai sawa ah silent da yayi, Ilhaam na halkance dashi saidai batayi magana ba, ah ranta tace "Ku kuka sani" ta wani bata rai ta juya, bai ma kula da ita ba saboda hankalin sa nakan driving da yakeyi, ah haka suka karasa gidan Ummi cikin silent driving dan bawani so yakeyi ya mata magana har yayi nisa suyi fada ba, kin fita tayi bayan yayi parking, shi kuma sanin aiki sa ya zaga ya bude mata sannan ya kama hanun nata suka karasa entrance door, koh da suka shiga kowa ya hallara Anwaar kadai ake jira wai ah dole shine ango, saurin zame hanunta tayi cikin nasa ta karasa ciki da sauri ta fara gaida mutane "Ina kwana" ya fada sannan ya zauna, duk suka masa da "Lafiya" Ilhaam na tsaye kaman wanda akace karta zauna "Ilhaam zauna mana" Yaa Humainah tayi magana "Ina Ummi?" Ta tambaya ganin bata ganta ba" sannan ta zauna "Ummi na sama da mutane, bari ma mu karasa shirya boxes in chan" Ateekah ta fada sannan su Humainah suka bita, Aameer kam na daga gefe beyiwa kowa magana ba da gani kasan bai samu abunda yakeso ba "Su Abu na waje tun dazu fa, ku tashi ku tafi" Ummi ta fada tana saukowa Maa Laure na biye da ita, dan duqawa sukayi suka gaisheta "Aya biyo ni" ta fada ganin Ilhaam wani iri, da toh ta amsa sannan ta mike tabi bayanta "Doctor muje" Aameen ya fada sannan ya tashi "Shareef fa?" Ya tambaya dan tabbatar wa koh yazo "Yana hanya dai" tunawa yayi da Fatima ta kirasa dazu hakan yasa ya ciro waya dan kiranta, ringing biyu ta daga dan daman yana hanunta wayan "Morning Babe" ta fada cikin farin ciki kaman wanda aka daura auren "Kin tashi lafiya?" Ashphert ce ta wani kura masa ido kaman tana jin abunda Teemerh ke fadi "Lafiya lau, today is the day" ta fada still da murna "I know" ya amsa ah takaice "Su Daddy suna airport" bai amsa ba yayi shiru yaji dalilin kiran nata "Yawwa, akwae gidan Gramma ah Maiduguri, ya kamata kuje ku gaidata ta saboda tanasan sanin ka"....  "Daurin aure zamu Fatima, ba visitation ba" ya fahimtar da ita "Will call you later, Mummy na kira na" nan tayi hanging ta tafi kiran Mummy "Muje" ya fada sannan ya tashi Aameen ma ya tashi "Barrister muje mana" Aameen ya fada ganin Aameer na zaune, ganin kaman Aameer baida niyyan tashi yace "Barin duba Ilhaam kafin nan" ya fada sannan yayi sama "Don't keep them waiting, kasan halin su Yaya" Aameer ya danyi raising voice nasa dan Anwaar yaji, koh da yaje bai samu ya mata magana ba dan mutane ne koh ina, hakan yasa ya dawo suka fice "Ash, ya kamata ki sake ranki fa, koh ita wanda za'a mata kishiyan ma ta haqura" Xeenerh ta comforting nata "Xeenerh auren yayi kusa dayawa, kuma kinsan Teemerh batasan zaman lafiya, ina tausaya wa Ilhaam" ta fada tana girgiza kai "Same here Ash, haquri duk zamuyi, bakiji abunda Ammaah tace ba dazu? Fada ta kira tana yi wai yaushe yayi auren farko da zaiyi ta biyu?" Kallonta kawae Ashphert tayi batace komai ba dan ita Aameer koh da wasa bai isa ya mata maganan kishiya ba saidai ya kare da magana akan Ilhaam, tasan Ilhaam kuma bazata kulasa ba, beside she is married, kuma Anwaar bazaiyi tolerating wannan ba

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now