💖💫RUDANI💖💫 15

247 44 20
                                    




Ta bangaren Teemerh kuwa tunda ta koma ba zama tayi bafa, wajen Ahmad ta wuce tace masa ta gama wannan sai kuma part 2 "Okay yanzu zaki shiga ciki kice wa masu cafe in nan kinaso kiyi making call, sai ki kira Anwaar and for that you have to fake a voice" wani shu'umin murmushi tayi tasan koh batayi faking voice ba Anwaar ba gane muryanta zaiyi ba, saboda shi bayi mata magana, koh ta gaida sa sama-sama yake amsawa kuma "Ashe ka tuna da komai Ahmad" murmushi yayi yace "Dole na ae inason Ilhaam" hakan kuwa tayi "_Hello I'm I talking to Dr. Anwaar Albaaz?"
"How can we help you?" Taji muryan mace ta amsa kasancewan landline na asibiti ta kira "Can I talk to Doctor Anwaar please?" Shiru taji anyi kafin akace "Hold on, Doctor Anwaar will be on the line within seconds please" dan murmushi Teemerh tayi bata sake magana ba saida taji Anwaar ya amsa "Am I talking to Doctor Anwaar Albaaz?" Ta maimaita dan tabbatar wa "Yea sure" ya amsa cikin nutsuwa "Ga Ilhaaam taka waje tare da wani shiyasa nayi tunanin kira na fada maka saboda babu wacce baisan gf naka Ilhaam ah garin nan ba harma da kewaye" dan dariya yayi dan yaji shirmen yayi yawa "So dan kawae tana gf ina sai karta fita da wani? It might be her brother" ya fahimtar da ita "And don't you dare call me again, how do you expect me to trust you?" Anwaar ya fada cikin bacin rai "Who are you and how did you reach me?" Ya sake fad'a dan yasan Ilhaam ba yawo take ba, dan ta lura bayisan yawo toh ta kiyaye, tsoro Teemerh ta faraji ganin kaman baza tayi nasara ba amma ta daure, dan kallon Ahmad tayi sannan ya mata alama data cigaba kawai "For that I'm your well wisher Anwaar, and I care about your life, Landline na kira koh ka mantane? your hospital landline is available everywhere, and if you don't trust me then come to Blu Cabana restaurant and cafe, you will see for yourself, your well-wisher bye" Diipp ta kashe wayar, wani ajiyan zuciya ta sauke kafin ta ajiye wayan, Anwaar kuwa ji yayi kanshi yana juyawa, share abun yayi ya cigaba da duba patients saidai inaaa ya kasa daina tunani, like yasan in akwae mey daukan Ilhaam zuwa Restaurant will be no one but Aameer, but yasan Aameer is busy with a case so ba yanda za'ayi ya samu time, ganin bazai samu amsan tambayan sa ba sai yaje ne kawae ya tashi zuwa office in Dr. Shareef (one of his friends) shine zai dunga zama a hospital saboda Anwaar bey fiye zama ba, so that's main reason daya sa Shareef a asibitin sa, sallama ya masa tare da fice wa a Clinic in gabadaya

"Ahmad kanaga Anwaar bazae gane ba kuwa? Duk na tsorata" Teemerh ta fada tana zuru-zuru da ido, dan dariya Ahmad yayi "Ke kin fiye tsoro Anwaar baya tsananta bincike Babe, kinga abubuwan ma zai tafi mana da sauki, yanzu dai mu karasa ciki"
"In muka shiga ciki ae plan in will not go well Ahmad, bari muga zuwan su, kuma Allah dai yasa yazo kasan ba karamin aikin Dr. bane yaki zuwa"
"Karki damu nasan indai akan Ilhaam ne zai iya komai fa" ya comforting nata "Anya kuwa zaizo?" Ta sake tambaya "Teemerh ki kwantar da hankalinki ni nasan Anwaar zaizo, yanzu dai bari ni na kira Ilhaam in" dakai ta amsa ta cigaba da danna waya, kiran Ilhaam yayi bata daga ba sai ah karo na biu shima saida ya kusa tsinkewa kafin ta dauka "Hello cutest" Ahmad yace da ita, cikin siririyar muryanta tace "Hi"
"Uhm two days kin mantani, koh da yake banida amfani ne shiyasa"
"Aa kawae two days ina busy ne Ahmad" ta fada a nitse "Toh yasu Xeenerh da Ashphert?" kallonsu tayi sai kuma tasa a speaker tare da cewa "They are fine"
"That's good" Teemerh ce tayi interrupting zancen tare da cewa "Hey Ahmad" da karfin inda Ilhaam in zataji "Ahh Hy Teemerh kece?" ya fad'a kaman yanzu ya ganta "Eh Anwaar ne yace bazaku gaisa ba? Gashi can fa" Ilhaam saida taji rass, saurin kallen su Xeenerh da suka zaro ido suma tayi, holding call in Ahmad yayi saboda kar Ilhaam tayi zargin wani abu, kawae so yakeyi tayi tunanin baisan taji wannan in bama "Good" Teemerh tace tare da nuna masa thumb nata!.. "Hello Ilhaam are you there?", "Eh" tace ah hankali "Sorry ina magana ne"
"No bakomai" ganin bazatayi magana yanda sukeso ba Ashphert ta karbi wayan "Ahmad muryan wa nakeji kaman na Teemerh?" Saida Teemerh taji wani rass jin muryan Ashphert saboda tana mugun shakkanta "Yea itace wae sunzo nan Blucabana da Anwaar sun ganni shine sukeso mu gaisa"
"Ohh I see, amma ba Anwaar na gidan mu bakoh?"
"Shi mana Ashphert"
"Noo nasan Anwaar bazai bi wannan 'yar iskan yarinyar ba"
"Ashphert I'm serious in kinaga karya ne you should come and see for your eyes"
"Eh gani nan zuwa" ta fad'a ciki da masifa "Keda Ilhaam tawa zakizo?"
"Bansani ba" ta fada cike da haushi, cutting call in tayi tare dajan tsaki "Ilhaam sai ki tashi Mahmoud ( Driver) ya kaiki, ki gani wa idonki wannan ikon Allah" Xeenerh ta fada "Ba yanda zanje, Anwaar wa kanshi yake yiwa ae" tayi maganan kaman mey shirin sake kuka "Noo Ilhaam kiyi haquri kije" da kyar suka shawo kan Ilhaam ta yarda zataje saidai tace su rakata nan ma duk sukaki wae su sun dawo agajiye.
***
Motan Anwaar ne ya shigo ah 360 sai kuwa ah idon Teemerh "Ahmad ya iso" ta fada cike da murna "Yanzu saura lhaam" ta fad'a tana tsalle "Daga gidan su Ilhaam zuwa nan ba nisa, yanzu zata iso karki damu, yanzu kiyi sauri kije ki tareshi tunda bata karaso ba" da sauri ta tashi tayi hanyan wajen da yayi parking, ae kuwa tana tashi saiga motan su Ilhaam ya iso nan Ahmad da sauri ya karasa wajenta, tafiya Teemerh takeyi kaman munafuka saboda Anwaar yayi noticing nata ae kuwa sai gashi ya ganta, kaman bazai mata magana ba sai kuma ya kira sunanta a nitse "Fatima?" Ya gane kayan jikin nata saboda is one of his favorites, bayi gane kowani kayan Ilhaam, but this? Bazai manta ba as shi da kansa ya bata kuma he loves everything about the dress, the color and everything, amma baiyi magana ba dan yasan qawan Ilhaam ce "Naam" ta amsa tare da juyawa, mamakin karya tayi sai kuma ta saki wide smile nata me kara mata kyau "Ina yini?" Ta fada da fara'a "Lafiya, mey kikeyi anan? koh tare kike da Ilhaam?" Ya jero mata tambayan "Erm.. Aa dazu dai na ganta da Ahmad bansan koh sun shiga ciki yanzu ba" wani takaici yaji a zuciyanshi sai kuma ya daure "Ahmaddd" ya nanata a zuciyarshi "Ta ina?" Ya tambaye ta "Ta can" ai kuwa tana nunawa saiga Ilhaam da Ahmad suna zaune suna magana, ta glass na wajen Anwaar ya hango su, itama cike da mamaki ta d'ago tana kallon Anwaar saboda batasan Ilhaam ta karaso ba, shima kallon nata yayi "Ahmad?" Ya tambaya, kai kawae Teemerh ta gyad'a, ta wajen su Ilhaam kuwa tambayan shi tayi "Ahmad ina Anwaar yake?" Yace "Kalli can" ya nuna mata parking space dan koh basu da nisa as ba ciki suka shiga ba, zabura tayi da sauri ta mike kasancewar yanda taga Anwaar yasa hanu akai Teemerh na rike da hanun nashi, daurewa tayi ta juya tana kallon Ahmad "Teemerh ce fa" ta fad'a still idonta kansu danta kasa gane dalilin Teemerh nacin amananta, ita tafi trusting Teemerh akan Anwaar fa "Eh itace, ae na fada baku yarda ba" hawayene taji yana sauko mata, sai ah lokacin Anwaar ya juyo yana kallon su Ilhaam, Ahmad yana ganin Anwaar ya juyo yayi hugging Ilhaam, da sauri ya dauke kansa saboda he can't take it, da sauri Ilhaam taja jikinta daga rikon da yayi mata tareda daukeshi da mari, saboda batasan yanda Ahmad yake behaving, tasan kuma womanizer ne so she has no other option but to slap him "How dare you?" Ta fada still hawaye na sauka ah idonta, jan jakkanta tayi ta wuce Ahmad na kiranta amma taki juyawa "Anwaar take a look tatafi" Teemerh tace dashi saidai shi daya daga kai kallon Ahmad yayi nayiwa Ilhaam waving alamun bye! wanda ita batasan yayi bama, saboda tunda ta tafi bata juyo ba, harta shiga cikin mota bata ce su tafi ba sai kallon Anwaar nata da wata takeyi, Anwaar kam cike da fushi ya kama handle in mota zai shiga "Uhm Anwaar dan saukeni a gida" Teemerh ta fad'a da afraid of rejection, baice mata komai ba hakan ya bata dama shiga, ita koh Teemerh ta zaci Ilhaam ta wuce tuntuni amma ina, shigan Teemerh cikin motan keda wuya Ilhaam ta hangosu "Let's go" tace ga Mahmoud

💖💫RUDANI💖💫Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang