💖💫RUDANI💖💫 52

104 27 54
                                    


Su Ilhaam kuwa bayan sun idar da sallah sukayi karatun Qur'ani sai addu'an bacci kafin suka kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa dan yau damuwanta ba sosai ba Teemerh bata nan, shi kuwa ya rasa dalilin Fatima na k'in daukan kiran sa dan daga baya ma kashe wayan tayi, tashi yayi zuwa study room dan dubawa Aameer requested book, yana cikin dubawa sai ga kiran Fatima, ajiye littafin dake hanun sa yayi sannan ya nemi waje ya zauna tare da answering call in yasa a kunne "Mr. Righttttt" ta fada cike da murna kaman wanda sukayi shekara basuyi waya ba "I've been calling you kinki dauka" ya fada, ganin littafin kusa dashi yasa yayi saurin dauka "Kayi haquri, wlh hidima ake sosai duk kaina yayi zafi, gashi kasan nice best girl" ta fada tana shagwabe murya "Okay badamuwa, ayi biki lafiya" ya fada hankalin sa bayi kan abunda take fada sosai saboda yana karanta wani line cikin littafin "Ae dole kace bakomai tunda dama chan baka damu dani ba, beside kanada mata ah gida ae nasan baka tunani na ma koh missing ina bakayi" ta fada kaman mey shirin sa ihu "You know I do" kadai yace yana cigaba da karatun sa "How will I know you do?" Ta fada tana pouting mouth kaman tana gabansa "Till this moment, I never knew myself" Ya karanta wani line cikin littafin loudly and she thought da ita yake "Wowww" ta furta wai ita ta zaci wani pickup line to show his love for her ne batasan bey ma ji abunda tace ba "What does that mean?" Ta tambaya dan ya mata karin bayani "Just reading a book, and the line came up" ya fada mata gaskia, haushi iya haushi Teemerh taji sa dan yanzu ta tabbatar hankalin sa ba'a kan maganan da suke yake ba, yana kan littafi "What is the name?" Ta daure ta tambaya "Pride and Prejudice" ya amsa yana sake duba cover'n book in, ta gane littafin sarai dan ranan ta ga Ilhaam na shirya su "So you are a reader now" ta fada dan taji mey zaice "Aameer keso, na duba masa ne" ya bata amsa cikin nutsuwa, kafin ta amsa ya sake ce "It's getting late Fatima, sleep well and make sure you pray before sleeping, am hanging" yana gama fada ya kashe ba tare da jiran abunda zata ce ba, yana hanging ya ajiye littafin ya koma dakin Ilhaam, ta fannin Teemerh kuwa bata taba ganin dan rainin hankali irin Anwaar ba, wato irin ta damesa da surutu in nan, tsaki taja sannan ta juya sai ganin Xee na zuba mata harara tayi "Miye?" Ta tambaya cike da rashin kunya "Haka zaki zauna har yanzu namiji na miki wulakanci kuma baki gajiya da masa magiya kaman shi kadai Allah ya halitta?" Ta fada tana cigaba da hararanta "Aa Malama, mijina ne na sunnah, saboda haka ki barni na nuna masa soyayyah" ta fada itama sannan ta harare Xee, "In ban nuna masa soyayyah ba wa naki mijin zan nuna?" Ta fada kasa-kasa gudun kar Xee ta jiyota sannan ta sauka kan gadon, ita duk abun duniya ya mata yawa gashi yanzu wai ita da Yaa Xee zasu kwana, dan karamin tsaki tayi sannan ta karasa wajen closet, towels ta gani sabbi nan tadau daya ta rage kayan jikinta sannan ta daura, tasa daya akai gudun kar ruwa ya tabasa, hanyan bathroom ta nufa sannan ta juyo ta kalli Xee dake danna waya hankali kwance "In ba kaddara ba mey zaisa ba hada daki daya dake, ke ba Anwaar ba, ni wajen Beey zani kawae ma" ta fada tana tsaye jin mey Xee zatace, batace mata komai ba bayan kallon ta da tayi dan ta lura yau marasa kunyan jikin Teemerh suna kusa "In kinga dama kije ki wanke kan naki Fatima" abunda ta fada kenan ta cigaba da danna waya, sa hanu tayi ta gyara towel in da tunanin yanda zata ba Anwaar wahala wajen neman soyyayya'n ta in aikin su ya kammala "Ae sai na sake karban kudi wajen sama tunda baisan zafin su ba" ta fada batasan ta fada ba hakan yasa Xee juyowa ta kalleta "Ke su Aunty sun koya miki san kudin masifa koh?" Harara Teemerh ta watsa mata kafin tace "Sai ki fada mun yanda aiki na zai yiyu ba tare da kudi ba, tunda nayi aure Daddy ya daina bani sisi" ta fada sannan ta shige bathroom dan ta biye na Xee baza tayi wanka ba


Da wuri Ilhaam ta tashi tayi komai ta gyara gida da dakuna duka ita kadai sai nishi take, Anwaar da fitowan sa ah kitchen kenan ya fara dariya ganin yanda take rike da baya ita ah dole tayi aiki "Ae sai kayita dariya kuma" ta fada tana murguda baki "Yaa Ateekah tace she's sending a maid amma kinki" ya fada yana controlling dariyan sa "Aa nida ita kuma sai an wani dauko maid, lada zamu samu in munyi ae kuma naga bakaso ma" ta fada da murmushi "Okay, the food is ready" dan ware ido tayi dan da yace ta bari zaiyi making breakfast in bata wani zaci zaiyi sauri ba dan ita batasan sanda Anwaar ya iya girki ba, binsa kawae tayi zuwa kitchen yanda girkin yake ta kamshi "Kaji kamshi kuwa, wow ban sake yin girki ashe kai zakana yi" ta fada da zolaya "If that will make you happy, I will, it's my promise to make you happy" ya fada yana daura mashed potato muffins cikin plate "Anwaar is so sweet" ta fada ah ranta sannan tasa hanu ta karbi plate in daga hanunsa ta dau daya ta fara ci harda kad'a kai "Bad manner" ya fada yana sa mata smoothie straw cikin Chocolate covered strawberry smoothie, dan kallonsa tayi dan batasan mey tayi ba "Ba kyau cin abu a tsaye" ya fada ah takaice, maimakon ta nemi wajen zama sai ta ajiye masa plate in tayi tadau smoothie dan tasan nata ne "Wa yace miki naki ne?" Murmushi tayi zata fara sha ah tsaye ya tsaidata "The chocolate in it says it all" tana fada takai baki, ganin kallon da Anwaar ke mata yasa tabar sipping tare dace "Sorry" ta zauna kan kitchen chair mustard "Bazaka sha ba?" Yayi dadi fa, murmushi yayi ya jawo Romany bar stool ya zauna akai "Will only drink from your cup" yayi nuni da glass cup nata, ba musu takai masa baki, straw in ya kama yayi sipping tareda ce "Thanks" murmushi tayi ta cigaba da shan abunta, ita kadai sai kad'a kai take, wayan sane ya fara buzzing hakan yasa ya duba waye, ganin Fatima ne yasa ya daga, tana jin ya daga tasa kuka "Subhanallah" yayi whispering, Ilhaam dake kallonsa cigaba da kallon sa tayi dan ita ta lura kullum take having moments da Anwaar sai Teemerh ta kirasa "What was the actual thing Fatima" ya tambaya jin tayi shiru da kukan "Yanzu haka maganan da nake maka an fasa auren" ta fada tana shekan kuka "What?" Yayi exclaiming "Why?" Ya tambaya kuma "I don't know, amma gani muke aljanu sun shigeta dan haka kawae ta haukace wai ita batasan auren, yanzu ma shiri ake za'a tafi Niamey nema mata magani dan bakaga yanda ta hana mu bacci ba jiya" ta fada sai kuma ta sake fashewa da kuka dan ya cigaba da sympathyzing abun "This is terrible, amma har sai sunje wani k'asa?" Ya tambaya da mamaki dan baiji maganan nata ya bada sense ba "Eh ae kasan taje chan kafin biki, shine ake ga halan ah wajen ta kwaso su, nikam ma fa ba zuwa zanyi ba dan nace ban fada maka ba, iya Chadi mukayi zan tsaya" ta fada da sigan munafurci, baisan lokacin da murmushi ya escaping lips nasa ba ganin how submissive Fatima is, murguda baki Ilhaam tayi ganin yayi murmushi "But you can go, duka zasuje kuma ke kice Aa?" Wani sanyi Teemerh taji ah ranta dan tasan dama ta gwada masa batasan zuwa saboda bai bata izini ba zaiyi permitting nata, gashi kuma yayi "Thank you very much Babe, yanzu nima zan shirya saboda mu isa da wuri kar mu isa ana magrib" yace "Ya wuce kuyi 2 hours ne Fatima? Chad zuwa Niger ba nisa ae" ya fada calmly "Kasan duk kudin wajena ya kare kuwa, duk ta samu kashe kudi wai yanzu ta fasa biki, a mota ae zan tafi, nikam duk ta gama cuta na, tun ina Nigeria na tura mata da wasu kudin ae, da na tafi muka kashe sauran" ta fada cikin nutsuwa yanda zatasa maganan yin dai-dai "You don't have to, yanzu nawa kikeso?" Ya tambaya yana kallon Ilhaam da tadau Potato muffins nata tana ci hankali kwance "Babe, kashe kudin zaiyi yawa, ka bari naje a mota kawae" dan karamin tsaki yaja jin yana tambayan ta abu tana masa shirme "Ina tambayan ki abu kina mun shirme? You know very well hanyan su ba kyau, sai kin kwana ah hanya ba iya magrib zaki kai ba" ya fada ah tsawace hakan yasa Ilhaam ta tsaya kallon ikon Allah, yanzu zakuyi maganan mutunci dashi, yanzu kuma zai fara bata rai yana gwada wani King's attitude "Yi haquri toh, banso bata maka rai ba wlh, koh nawa ma zaiyi" Teemerh ta fada in a low calm voice "Shikenan, take care" ya fada sannan ya kashe kiran, tashi yayi yabar kitchen in, tabe baki Ilhaam tayi tare dace "ALLAHUMMA INNI AS' ALUKA AL'AFIYAH" (O Allah, protect me from any pain & suffering)

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now