💖💫RUDANI💖💫 36

155 27 26
                                    


Gidan Baa Teemerh ta ajiyeta sannan tayi gidan su Ahmad, Amrah kadai ta samu tana kokarin fita, ganin Teemerh ta dawo ta zauna "Ke kuma ina zuwa haka?" Teemerh ta tambaya tana wani yamutsa fuska "Zan koma school, kinsan ya kamata na kimtsa, shopping zani"  "Toh duk Australia ba mall sai anan Abuja koh?" Amrah tace "Toh wai Teemerh haushin na mene ne ba gashi yanzu na dawo ba? Dama kar ah barki ke kadai ne ina?", "Ina Mama?" Ta tambaya ganin bata ganta ba "Mama tana office , shi kuma mutumin naki ae kinsan yanda zaki same sa", "Ke ni rufamun asiri da zuwa gidan Ahmad, ina ne kuwa yanda zan same sa in ba nan ba? Mutumin da ba aure yake da ba" tabe baki Amrah tayi tace "Uhm wai Ilhaam zatayi aure koh?" Ta tambayi Teemerh dake cika tana batsewa "Toh ni miye ruwana koh bakisan Anwaar zata aura ba?", "Allah ya baki haquri Teemerh, na manta ashe kina sansa" wani kallo Teemerh ya bita dashi harda wani jan tsaki ita ah dole taji haushi "Toh Teemerh school fa?" Ta chanja tadin ganin Teemerh ta share ta "Wai ni Amrah kinga na miki kama da mey yin karatu? Yanzu fa kike kara tuna mun wanda nakeso na aure zaiyi aure, kuma kina tunanin zan fasa aure na wuce karatu koh? Toh miye riban boko ba turanci bane? Toh tun kafin na fara zuwa school na iyashi" ta fada cike da takaici, Amrah bata amsata ba, dan tasan koh ta fada mata advantages na western education ba fahimta zatayi ba, waya ta ciro tayi dailing number'n Ahmad amma harya gama ringing bey dauka ba "Amrah mey ke damun Yayanki? Na kira bey dauka ba" Amrah tace "Tunda yaji labarin auren ae ya kasa sukuni, shiyasa ma ya tattara yabar nan" dan biting finger'n ta tayi dan tunda taji haka ba daukan wayan zaiyi ba kenan "Kina nufin dai yanzu bayi daukan wayan kowa kenan?", "Eh toh Mama kadai ke kira da ya dauka" dan tsaki Teemerh taja "Amma wlh Ahmad anyi ragon namiji, saboda mace zai wani boye kansa?" Takai 2mins dayin maganan kafin Amrah tace "Yarinyan bata dace da Ahmad bama, I always wanted making her my friend, sai kuma kika rigani" girgiza kai Teemerh ta fara "Gaki ga ita ae, I've nothing to do with her, yanzu ita ba qawata bace" Amrah kam kasa magana tayi dan ta rasa miye akan Teemerh kwana biyu "Wai duk san nashi ne ya saki haka?" Ta tambaya ganin Teemerh nasan zama mahaukaciya "Har abunda yafi haka zanyi, indai saboda Anwaar ne" ta fada tana kad'a kai kaman wannan tayi abun kirki "Amma Ilhaam tanada saukin kai Teemerh, kuma tana sanki, da tun farko kin fad'a mata kinasan Anwaar da bazata bari abun nasu yayi nisa ba, nasan koda bey soki ba, bazata yarda tayi soyyayyah dashi ba" Teemerh da kaman jira takeyi Amrah ta karasa zancen nata tace "Kin gama? In kuma baki gama ba sai ki karasa mun sauran, ita batada hankali ne da bazata fahimta ba?" Tayi magansn tana hararan Teemerh "Dole ta fahimta ae, tunda wahayi ake mata, kin samu na fasa fita dole ki zauna kina mun ra'ayi, auren Ilhaam da Anwaar kuma baza'a fasa ba" Amrah ta fada cikin fushi sannan ta mike, fashewa da dariya Teemerh tayi ganin ran Amrah ya baci "Toh qawar Ilhaam, I hope kina cikin bridesmaid" dan rufe baki tayi kaman ta tuna wani abu "Oops ae na manta, bikin da za'ayi shi cikin gaggawa ae ba events in da za'ayi, inda za'ayi events kuwa dasai naje na bata komai" dan murmushi Amrah tayi ganewa da tayi ba hankali jikin Teemerh "Da kuwa Anwaar in ya koya miki hankali" ta fada sannan ta fice, gyara zama Teemerh tayi tana cigaba da trying number'n Ahmad koh zai daga, bey dauka ba hakan yasa ta ajiye wayan ah gefe, bada jimawa ba kuwa sai ga Ahmad kaman yasan tana jiransa, Amrah na bayansa sai tura baki take "Kaman kasan zaman jiran ka nake" , "Ae kuwa sa'a kika ci dan daukan abu nazo ma"  ya fada yana kokarin wucewa, ganin Amrah na tsaye ya daga mata tsawa "Zaki wuce koh A'a?" Kai ah kasa tayi sama kaman mey shirin kuka, bey ce mata komai ba yazo ya zauna ah one of the seaters "Ahmad amma kasan dai ance abunda kayi dole ah maka" kallonta yayi cikin rashin fahimta "Naga you're overprotective akan Amrah, ashe ba'a b'atawa ka b'ata sisters na wasu" shiru ya mata yana jiran ta gama "Toh banda abunka addu'a kawae zaka mata, naga ma tanada hankali, ae yanzu shopping zata fa-" hanu ya daga mata alamun ta dagata, shiru tayi ganin yanda ya wani bata rai "Su suka kawo kansu, Amrah kuwa bazata kai kanta ba" tabe baki tayi tace "Toh Allah yasa, wai ina keepers in gidan nan? Nazo ba'a bani abinci ba", "Amrah zaki tambaya, ni da ban zaman gida, barin kirata ta kawo miki" ya fada sannan ya ciro waya, ringing biyu ta daga yace ta sauko "Ahmad wai duk saboda auren ka koma chan? Kenan bazaka daurin aure ba" yace "Zanje, amma in basu kaishi Maiduguri ba, which zaiyi wuya" zata amsa taga Amrah, nan ta fasa magana "Ban abinci, yunwa nakeji" ta fada idonta kan Amrah "Wai ni na hanaki cin abinci kafin ki fito gida?" Harara Ahmad ya watsa mata "Amrah, zaki bata abinci ne koh Aa?" , "Gani nayi fa tasan hanyan kitchen" tunda yaji haka yasan fada sukayi "Wai ke Teemerh akwae randa zakizo bakuyi fada bane?" , "Allah kai bazaka gane bane, daga zuwa ta fara cemun wai Ilhaam zatayi aure, toh ina ruwana?" Dariya Ahamd ya fara tsakanin sa da Allah har yaba Teemerh haushi, Amrah na tsaye sai girgiza kai takeyi ganin yanda Ahmad ke dariya "Allah yayi mugu, dadin abun kaima abun ya shafe ka" tsaida dariyan yayi "Yau naga daman rabuwa da ita zanyi hakan, but I can't be defeated" Amrah ce tayi saurin bashi amsa "Already an defeating naka ae, Anwaar is taking the girl" shiru ya mata dan ba gane abunda yake nufi zatayi ba "Sorry, ni zan fita fa, kinzo da mota ne koh na sauke ki?" Yayi directing question in wa Teemerh "Da mota nazo" ta fada sannan ta mike "Abincin fa?" Amrah dake tsaye ta tambaye ta "Amrah zan tafi kawae, yaushe zaki zo?" , "Kafin na koma dai" , "Toh Allah ya nuna mana" Amin ta masa sannan su Teemerh sukayi waje, ita kuma tabi Ahmad da harara yazo ya katse mata yawo, har sun fita ya dawo yayi sama dan ya manta abunda yazo dauka


💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now