💖💫RUDANI💖💫 37

148 28 17
                                    



Shirin biki sosai aka fara, Ummi da Xeenerh ke hada kayan aure, Ummi tace suje Paris, Ashphert tace Aa aje Monaco tunda shima French speaking country ne kuma they have expensive and qualitative abubuwa, Aameer kuwa yasan Ashphert da shegen san yawo yasa yace basai anje ba, suyi ordering komai kawae tunda dama lokaci ya kure, haushi sosai ya bata hakan yasa ba shirmen da bata dauka ba, ita kanta tasan wasu abun ba amfani dashi Ilhaam zatayi ba amma saida ta dauka, anzo inner wears tace na France ae yafi "Wai Ashphert ba dama a sai komai ah waje daya ne?" Ummi ta tambaya dan rawan kan Ashphert ya fara damunta "No Ummi, France sunada inners masu kyau, koh Xeenerh" Ehh kawae Xeenerh tace dan ta gane Ashphert rigima takeji "Toh kinata zuba kaya banji kinyi maganan atampa ba" Ummi ta sake magana "Eh Ummi, dama Hong Kong za'a duba, amma fa su bazai iso da wuri ba dole zuwa dakai yafi" daukan waya Ummi tayi ta kira Humainah dake sama tace ta sauko, bata jima ba sai gata ta sauko "Ni ban gane shirmen da yaran nan suke mun ba, zauna kimun koh fita zakiyi?" Ta tambaya ganinta da shiri "Eh, da kam zan fita ne, amma tunda akwae abunda zan miki sai ayi ae Ummi" ta fada sannan ta ajiye handbag nata daga gefe tana kokarin zama Ummi tace "Aa jeki kawae, dazu naga Aameer koh? Kira mun shi" da toh ta amsa ta fita, chan saiga Aameer ya shigo dan dama tunda aka fara shirye-shirye toh ba'a raba su da gidan Ummi "Ummi gani" ya fada sannan ya zauna, Ashphert sai harara take zuba mishi, Xeenerh na gefe tana dariya ciki-ciki "Atampopi nakeso kuma Ashphert tace wai sai Hong Kong" wani kallo yabi Ashphert dashi hakan yasa ta sauke kai kasa, shifa kan wannan dan banzan yawo tsaf zai koya mata hankali "Ummi, yanzu lokaci ya kure, kafin kayan su iso ma halan anyi biki" Ummi tace "Eh haka tace itama wai saidai muje" yace "That's what am saying Ummi, kinga yanzu kuma ae in kun tafi dole akwae abunda zai taso a tambayi ina kike, kawae Kano zaki tura ah kawo miki atampopi masu kyau, ba wanda bey san Kano da atampa ba", "Haba Yaa Aameer, ka bari ah sayi qualitative abubuwa kuma" Xeenerh tasa baki "Su Kano fake one suke kawo wa? Daga nan ma akan fitar chan countries in" Shiru tayi bata amsa ba jin zai fara fada "Yanzu zan kira Laure na mata bayani saina tura mata da kudin, kaga in zata taho saita taho dasu kawai", "Eh hakan ma yayi" Ashphert ta amsa tana leqa MacBook na Xeenerh "Toh karku manta ta taho da perfumes, kusan bazai biyo plane ba" Aameer ya sake fad'a "Ba muzo kan perfumes ba tukunna, but thanks for the reminder, Ummi ki tura mata kudin" Xeenerh ta fada tana kallon Ummi nan ta amsa da toh, da haka ya tashi yabar musu wajen dan kuwa yanada abunyi "Ummi sai mey kuma?" Xeenerh ta sake tambaya tana scrolling "Ansa Abayas?", "Eh anyi order daga Monaco, saidai naga kaman they are not good at Abayas za'a chanja country kawae", "Toh sai diamonds da Golds" Ummi ta fada tana dan duba MacBook in hakan yasa Xeenerh juyo mata dashi "Toh Ummi wani iri?" Xeenerh ta tambaya "Arabian" ta amsa a takaice "No Arabian gold jewelry da Indian sunada nauyi, Ilhaam kuma batasan masu nauyi, why not as French or Asian ones?" Ashphert ta tambayi Ummi "Toh sa French in, shi Diamond in kisa Asian" da Toh Xeenerh ta amsa "Sai shoes, bags da nighties" Ummi na fada Ashphert tace ah bata, ba musu Xeenerh ta bata MacBook in dan ganin mey zatayi, wasu nightgowns marasa kan gado ta dunga zab'a "Ke wae miye haka? Ke da zaki sa mata cartoon nightgowns nata data saba sawa kike sa mata wannan shirmen?", "Nifa kinga Xeenerh bansan shishigi, miye zatayi dawani cartoonists nightgown yanzu?" Xeenerh tace "Toh ki sa mata lengthy ones da kuma pajamas naga bakisa koh daya ba" shareta tayi ta cigaba da zab'an shirmenta "Toh miye abun tashin hankali kuma? Ke Ashphert ae ba ra'ayin ki kadai za'a biba, kisa lengthy ones da pajamas in" da toh ta amsa ta cigaba, saida tayi abunda Ummi tasata kafin ta mayarwa Xeenerh "Kunsa English wears?", "Eh ansa, amma nake ga kaman zuwan su in 3 weeks ne saboda shipping za'ayi, a turawa Aunty Khadie da kudin tunda tana London ta taho dasu tare da Laces, Shadda da kuma akwatuna", "Toh hakan za'ayi, Sabeerah kuma sai taje Maiduguri a hado Khumrah, turaren wuta da sauran abubuwan" tace "Ummi sai Lafayu" , "Zance Khadijah ta duba a chan shima" Ashphert tace "Aa Ummi asa Indian ones, Xeenerh kinga yanda suke lapaya yanzu kuwa" da toh Xeenerh ta amsa ta dan tasan duk wannan dogon surutu dan ah yarda da itane, Ummi ta dau waya ta kira Maa Laure da Khadijah duk ta musu bayani sannan ta tura musu kudin "Ku nutsu fa ku duba in akwae abunda aka manta, kuna nan har ku biyu bazai yiyu kumun shirme ba" ta fada sannan ta tashi zata bar wajen "Za'a kula da yardan Allah Ummi" tace "Ki kawo mun Credit card ina" Ashphert tace "Ummi yanzu?" bata amsa ba tayi sama, ganin haka Ashphert ta gyara zama "Allah Anwaar ne duk yaja wannan abun wae biki a 2 weeks, duk bata samun gatan da muka samu ba, da yanzu da kanta zataje ta zabi duk wannan abubuwa" Ashphert ta fada tana bata rai "Toh barin kira shi sai ki masa da kanki" ta fada tana kokarin daukan waya ae tuni Ashphert ta fauce "Kinsan fa Anwaar mugu ne kuma kike kokarin had'a mu" dariya Xeenerh ta fara ganin Ashphert ta tsorata "Girl I never thought he will ever fall in love, sai gashi yanzu auren sa zamuyi, he is the best" , "Dole kice haka ae tunda ke bayi miki mugunta" Ashphert ta fada tana murguda baki "Kisa Huda beauty cosmetics" ta fada jin Xeenerh ta shareta "Clinique dai" Xeenerh ta amsa "Xeenerh kisa su duka kawae" da toh Xeenerh ta amsa, haka suka yita sa abubuwa, wasu shirme wasu na amfani

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now