💖💫RUDANI💖💫 38

159 28 19
                                    


Ana turawa kudi kuwa yace ah basa 2 hours, zama sukayi ba sallah ba salati suna jiran kiran sa, basu kai 2hrs in bama ya kira yace taje ta samu mahaifiyar Anwaar suyi magana, ya tabbata bazata ce Aa ba, dan tsayawa tayi kaman mey tunani "Yaya yanzu ba lokacin tunani bane fa, shiryawa zakiyi kije ki sameta" , "Shamsiyya tunanin abunda nakeyi kenan, kinsan haka mukayi akan shi wancan yaron Aameer mahaifiyar sa taki yarda" dan dariya Shamsiyya tayi tace "Yaya, wancan karon ae ba'ayi aiki ba, yanzu kuma yace kije ba matsala" dan shiru tayi kafin tace "Toh shikenan, barin tashi naje na samu na dawo da wuri dan kuwa yau Alhaji zai dawo" tace "Yawwa Yaya, koh Xee ta dawo fa karta koma masa, zai an bashi wahala yazo da kansa tukunna" , "Karki damu Shamsiyya" ta fada sannan ta tashi, Hijab ta dauka da key suka fita tare da Shamsiyya, basu tsaya koh ina ba sai wajen Ummi, ah guest palo suka zauna yanda akayi mata magana, bada jimawa ba ta sauko "Hajia Malika ne gidan namu?" Ta tambaya da murmushin ta na kullum sannan ta zauna "Hajia Hajarah mun yini lafiya? Ya shirye-shirye kuma?" Da fara'a Ummi ta amsa da "Alhamdulillah" Shamsiyya ce ta kalli Mum alamun tayi abunda ya kawo su "Erm.. dama alfarma mu kazo nema" Sham ta fada ganin kaman Mum batada niyyan magana "Eh, Allah yasa mu samu" nan Mum ta samu karfin guiwan amsawa "Toh Allah yasa bai fi karfi ba, da yardan Allah kuwa bazai gagara ba" Ummi ta assuring nasu "Kar dai aga kaman nayi rashin hankali, nasan shi Anwaar in aure ma yake da niyyan yi, toh amma wani hanzari ba gudu ba, ita fa yarinyan wajena Fatima shi takeso, kuma a fadanta sunyi soyyayyah yanzu kuma yace aure zaiyi bada ita ba" nan ta dakata ta kalli Ummi dake sauraran duk abunda take fadi "Toh a gaskia dai duk mane nan nata ta koresu Hajiya Hajjo, indai bazai zama matsala ba koh zai aureta? Dan yanzu ma haka tana kwance ba lafiya" dan shiru Ummi tayi maganan Mum na shiganta ah hankali, indai gaskia take fadi kuwa ae Anwaar beyi wa yarinyan nan adalci ba, toh amma yaushe ma yayi ta farkon bare ta biyu? "Allah ya bata lafiya, zaizo ya dubata da yardan Allah" Ummi ta fada cikin nuna kulawa "Toh shi maganan auren fa?" Aunty Sham tayi saurin chapkewa "Ban k'iba dai, amma shi Anwaar in ae koh auren farkon ba'a daura ba bare ta biyu" kallon Sham Mum tayi saurin yi, ita fa ta tsorata kar matan nan tak'i, saboda tasan Ummi is a religious woman da wuya shirmen su ya kamata "Eh hakane Hajiya Hajarah, amma ya kamata a duba lamarin yarinyan nan" Shamsiyya ta fada da sauri, shiru Ummi tayi tana nazari, chan tace "Toh shikenan, dama tun farko ban k'iba, zanyiwa Anwaar magana, nasan innasa baki zaiyi" tayi magana bada san ranta ba, saidai taji bazata iya ce Aa ba "Toh Alhamdulillah, ae haka mukeso, shiyasa yin tarbiya wa yaro yake da dadi, wani d'an ae baka isa sashi ba, kuma baka isa hana shi ba" Mum ta fada da murmushi, itada Ummi bawai san hada zuri'a da Malika take sosai ba dan maganganu yayi yawa akanta, amma ta rasa dalilin daya sa ta kasa ce Aa "Toh mu zamu tafi, ayi biki lafiya" Shamsiyya ta fada sannan ta tashi, ganin haka Mum ma ta mike "Har tafiya kuma?" Ummi ta tambaya ganin duk sun tashi "Dama abunda ya kawo mu kenan, zamu wuce karki damu", "Toh a gaisheta da jikin, zaizo ya dubata da yardan Allah"Ummi ta maimaita "Allah ya kawo shi lafiya" suka amsa suna murmushi sannan suka fita, Ummi kuwa zama tayi ta fara tunanin lamarin, ah haka Ateekah ta shigo ta sameta "Ummi kiyiwa yarinyan nan taki magana, taki bawa gyaran jikin nan mahimmanci, gashi Anwaar ma dan rashin kunya samu na yayi wai a barta tunda bataso" ta fada sannan ta zauna kusa da Ummi, saida ta zauna ta lura kaman Ummi na cikin wani hali "Ateekah ae ba bin nata zakuyi ba, kunsan da yarinta a lamarin nata" , "Ummi wani abun ya faru ne?" Ateekah dai finally ta tambaya, dan ajiyan zuciya Ummi tayi sannan ta kwashe yanda tayi dasu Mum ta fada mata "Yaushe Anwaar yakai wanda zaiyi mata biyu, anya bawani abu kan ita Maman Fatima?" Ta tambaya da mamaki "Ummi kuma toh in an duba ita Fatima ae sai a duba Ilhaam ma, Anwaar bazai taba iya fada mata wannan ba, you made the choice, cewan ya auri Ilhaam, ya yarda and I don't know how, amma yanzu yana santa dayawa, kinga wannan ma biyayya ne" ta fada "Toh Ateekah koh nace suyi haquri? Danni gaskia hankali na bey kwanta wa abun ba" itama Ateekah batason abun, dan ita daman chan she's against polygamy, amma bataji wannan ya tsaya mata ah rai ba "Yanzu kam ae kin riga kin amsa Ummi, muyi addu'a kawae, khairan In Shaa Allah" ta fada ah takaice "Toh Allah yasa, kimun magana da shi Anwaar in" da toh ta amsa ta fita dan kiransa, shi kadai ya shigo Ummi na zaune wajen da Ateekah ta barta, daga ta kasa ya zauna kusa da kafanta "Ummi wai kina nema na" yayi maganan in a calm way "Eh, yarinyan nan Fatima batada lafiya fa" dan d'aga ido yayi ya kalleta danshi yasan Fatima dayawa "Ita dai Fatima'n daka gane kak'i ganewa toh ita nake nufi, er wajen Alhaji Shettima" ta amsa bayani "Ummi kiyi haquri, bansan batada lafiya ba shiyasa" yayi defending kansa "Yanzu dai duk ba wannan ba, ka shirya kaje ka dubota" dan daga ido yayi ya kalli Ummi jin abunda ya fito a bakinta yanaso ya sake tabbatarwa "Erm.. Ummi gani nake mun gama maganan Fatima tuntuni, I told you ba abunda yake tsakanina da ita" , "Bance akwae abunda ke tsakanin ku ba, cewa nayi kaje ka dubata" kasa amsawa ma yayi sai gyada kai da yayi dan bayisan mata musu, itama ji tayi bazata iya masa maganan auren Fatima a yanzu ba, tashi yayi kai da gani kasan ransa a bace yake "In kaga dama karka je, ae nasan halin ka in bakaso abu ba, kar dai nace baka amsa ba shine ka gyada mun kai ka tashi da fushi zaka fita koh?" , "Aa zanje, kiyi haquri" ya bata haquri "Gaisuwan rashin lafiya zakaje, sauran kaje hanu ba komai, nasan ba hankali gareka ba" bey ce komai ba ya fita yana tunanin what comes over Ummi haka

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now