💖💫RUDANI💖💫 39

168 25 50
                                    


An daura aure lafiya komai normal saidai ba wani bidia, Ilhaam tayi kyau sosai Anwaar kuwa dama kunsan handsome ne lol, kar fans in Ilhaam suce nayi sankai so let's just continue "Anwaar yanzu dole zaka tafi da Ilhaam fa" , "Eh bawani matsala saidai zamu dawo basai kun damu ba", "Allah ya dawo daku lafiya mutanen UK see you soon" tayi maganan da very thrill expression "Ba rakiya?" Tace "Noo ba rakiya ka dauki matan ka, the jet is waiting" yace "Toh Aunty see you soon" nan ya tashi ya fita, ta fannin Ilhaam kuwa tana chan tana kan rera musu kuka kaman wanda aka ma auren dole "Kai Ilhaam, Allah kukan nan yayi yawa mana, tunda akace an daura kike kuka sai kace wanda bakison sa? Mey jama'a zasuyi tunani?" Kou sauraranta Ilhaam batayi ba ta cigaba da rera kukanta. Maa Laure ta shigo da gud'a "Ku matsa mu dauki amarya" nan Ilhaam ta kara sautin kuka sosai ta juya ta rungume Aunty Aisha dake kusa da ita "Ilhaam kiyi hakuri ki tashi ku tafi" ta fad'a tana patting bayanta "Noo Auntie Aisha I can't leave you guys", "Ilhaam dan Allah kiyi haquri ki rufa mana asiri ki tashi dole watarana ki barmu ae, kiyi haquri kinji Ilhaam ina" Aunty Atee ta fada tana kokarin dagota, rike Aunty Aisha tayi sosai "Ni kam na fasa auren ba yanda zanje, Ummiii" ta fada ganin dagaske suke "Toh ba'a haifeki ba tukunna Ilhaam" Aunty Husnah ta fada tare da tashi danyiwa Ilhaam dole "Aa Husnah ki bita ah hankali" Aisha ta fada tana kare Ilhaam, ba juyin da basu yi ba Ilhaam taki fita "Toh ku tsaya ku zuba mata ido tunda hake akeyi ae, in amarya taki yarda sai ah barta koh Aisha?" Mama Laure ta fada still tana tsaye tana ganin drama "Toh Mama Laure Ilhaam ce fa" dafe kirji Maa Laure tayi "Toh in Ilhaam ce fa?" Tayi saurin tambaya "Kinsanta ae" Aisha ta amsa "Toh shikenan ku fita ku barta ah dakin tunda bataso ta fito" Humainah ta fada sannan ta kalli Khadie, gyada mata kai tayi alamun su fita, tashi sukayi duk suka watse ah dakin suka barta ita kadai harda ja mata kofa "Erm.. Yaa Sabeerah ya naga kun fito? Amaryan fa?" Xeenerh ta tambaya "Tana ciki" Sabeerah ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, Xeenerh ce ta kalli Ashphert da take kokarin karasowa "Toh Ashphert sai ki ji dadin ki amaryan taku taki fitowa" kallonsu Humainah tayi tace "Da'in fushi take koh mey? Ke Xeenerh ki kiyaye ni da wannan maganan naki" Humainah ta fada tare da girgiza kai taja karamin tsaki "No Yaa Hummy bawae haka bane ba, ta tambayi Aameer kan zata rakasu ne shi kuma ya hana" harara Ash ta bita dashi, inta zauna mishi toh mey zata masa "Ashphert kinada damuwa wlh nifa ah zatona wani abun aka miki" Sabeerah ta fada cike da takaici ah daidai lokacin da Maa Laure ta karaso tareda Anwaar, bude kofan yayi ya samu Ilhaam ah gefe ta hada kai da kafa sai kuka take, tana jin an shigo ta kara volume "Hushh Ilhaam kiyi shiru" tanajin muryan shi da d'ago da sauri "Anwaar nikam na fasa auren nan, ba yanda zanje" Daga ta yayi ba musu ta tashi "Bakiso ki bini UK?" Gyad'a kai tayi kaman small baby "Okay then zaki zauna anan Abuja? Koh Maiduguri?" Girgiza kai tayi "Ni ah nan gidan zan zauna" shifa ya rasa mey had'n Ilhaam da wannan gida "No that's impossible Ilhaam kinsan ba wanda zai bari ki zauna ah nan, nima bazan yarda ba" fashe mishi da kuka ta sakeyi ganin ya fara biye mata "Oh Ilhaam for the Almighty's sake kiyi shiru, yanzu gobe in Allah ya kaimu zan koma UK zaki zauna anan kafin na dawo hakan yayi?" Kai ta gyada alamun Eh! "Okay then cry no more kinji?" sake gyada kai tayi, yace "Can't you answer?" Yayi maganan ganin taki basa amsa da baki "Ok" tace ah hankali cikin siririn muryanta "How's Ammaah?" Ta tambaya "Ammaah is here in Abuja, so aure kadai muka daura ah Maiduguri" d'aga kai tayi "Sleep peacefully I love you ya mata peck a forehead nata ya fita" sa hanu tayi zata goge sai kuma ta fasa, samun su yayi suna tsaye carko-carko kaman dazu "Aunty we need to talk" Ateekah ce ta bishi gefe "You don't have to worry, both I and Ilhaam zamu kwana anan yau gobe sai na wuce UK", "Lafiya kou Anwaar?" Ta tambaya tana mamakin bawani abun aka mata badai koh "Lafiya qlou, Ilhaam batasan zuwa UK so I can't force her" ya fada mata gaskia "Toh bazaka tafi yau ba kenan?" Yace "Uhm, tafiya yau kaman na d'agashi" tace "Shikenan tunda kun yanke hukunci yanzu ina zakaje?", "I will be in the other part naga nan akwae mutane" tace "Okay fine" nan ya wuce ita kuma taje ta sanar dasu hukuncin Anwaar hakan yasa kowa ya watse "Toh ae ba kwana zakiyi anan ba Ilhaam" harara mey ni da lafiya Ilhaam ta mata "Sai ki hanani" ta fada ciki-ciki "Mey kikace?" Aunty Khadie da bataji abunda Ilhaam tace ba ta sake tambaya "Fita zakuyi kubar mun daki ae dakina ne nan" ta fada kaman mey shirin kuka "Inyee Ilhaam baki ya bude ance baza kije ba koh?" Sabeerah ta tambaya jin yanda Ilhaam tabar kukan tana rashin kunya "Toh ki tashi parts na A3 zaki kwana yau" tayi maganan more like a command "Lalle ma bakuji da kyau ba" tayi muttering amma ta jita "Ilhaam ki mana shiru" Sabeerah ta mata tsawa "Kin manta aure kikayi koh? Toh dakin Anwaar zaki abunda take nufi kenan sai ki tashi" da kyar Ilhaam ta yarda ta bisu, koh da sukaje part in ba kowa dan Anwaar in ma bayi nan sannan kowa yayi dakin baccinsa, tashi tayi palon dan bawani gane wa kallon zatayi ba, daki ta shiga nan tayi bathroom tayi wanka tazo ta shafe man gashin Anwaar ah kanta ta shafe mai, ta dudduba perfumes nasa taga ba wanda ya mata data shafa, kamshin duk basu mata ba, sai ta tunada overnight case da Ashphert ta kawo mata, tashi tayi taje ta budeshi, perfumes nata ne da sauran abubuwan da zata bukata ah ciki sai sleeping dresses guda uku, dan karamin tsaki tayi "Har uku?" Warware wa tayi saidai duk bana mutunci "Lalle Ashphert najin iskanchii yau" ta dauko wannan ta ajiye sai ta dauki wannan ta ajiye chan ta yanke shawaran sa blue one in, ta fashe jikinta da turare ta zumbula katon hijab tayi sallah sannan tabi gado.

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now