💖💫RUDANI💖💫 97

49 20 151
                                    


Kafin ma su gama shirin Shareef ya turo masa da sabon invite saboda anyi organizing wannan late yasa akayi canceling. Teemerh na zaune Daddy na bayanai saidai duk bayanin da yakeyi akan karatu ne yasa bai dameta ba "Kuma shi Anwaar yace zai dau nauyin karatun ki" ware ido tayi harda dan matsawa gefe, ita ah duniya ta rasa gata ne koh an rasa wanda zai sponsoring nata ne sai Anwaar "Haba Daddy, kai kuma fa?" Tana fada taji wasu zafafan hawaye sun sauko, ita kanta batasan daga ina suka fito ba "Ba tilasta masa nayi ba Fatima, kuma kinsan bawae kasa yin hakan nayi ba" girgiza kai tayi kawae cikin rasa abunyi "And the happiest thing ah gidan sa zaki zauna kiyi karatun. Dama bani sanki da zaman makaranta, kinga na samu mey kulawa dake" Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun kawae Teemerh ta iya maimaita wa, wato duk kalan tashin hankalin data shiga kadan ne compared to wanda zata shiga yanzu, ita ce zata zauna gidan Anwaar taga yanda yakesan matan sa? It's a capital NO amma bata isa fada gaban Daddy ba dan yanzu ta rasa wannan daman "Dan girman Allah Daddy in wani laifin nayi ka yafemun amma shifa yanzu ba mijina bane, I want to live in peace amma zaman gidan sa bazai yiyu ba, I might get heart attack living in with them" ta fada masa gaskiya sautin kukanta na karuwa "Daddy ni na fasa koh ina, wlh koh anan Abuja zanyi karatu amma baniso na zauna tareda su" ta sake fada ganin Daddy bai amsa ba, tasan final decision da yayi making kenan fa "Ki bude kunnenki ki saurare ni, harshi ya yarda da hakan ke kuma kice ba haka ba? Yanzu fa duk abunda zai miki alfarma zai miki. In kinga dama Fatima kije ki tada masa hankali shida matansa dan yanzu ke matsayin qanwa zaki gunsa" ciro cheque yayi ya bata ba musu ta karba, it's a blank cheque amma ganin sunan jiki yasa ta dago da sauri ta kalli Daddy "Yace ki sayi abunda zaki bukata na makaranta" yana fada ya tashi ya bata waje, binsa tayi da kallo hawaye ya fara sauka, ba tareda tayi magana ba ta yaga cheque in dan ae ba abunda zatayi da kudin sa, banda rainin wayo an fada masa kudi na maganin matsala ne, ita inda zata cire kudin ma da yawa yaji zafi da sai ta cire abunda yafi 600m in yaso ayi sadaka amma tasan ba zafin abun zaiji ba, Anwaar and his family are filthy rich, koh billions ta cire tasan bazai daga masa hankali ba tunda shi dama bai tambayan abunda za'ayi da kudi badawa kawae yake, recently ya tura mata 15m na kulawa da Fadel, tasan kawae ya tura ne dan Fadel ba wajenta zai zauna ba tunda daukan sa zaiyi, toh amma ita duk wannan bay dameta ba, ba abunda ita koh dangin ta zasuyi da kudin Anwaar tunda dama chan ae cikin gatan ta ya daukota, ba abunda ta nema ta rasa, dama Mummy che inta rasa kudi take nema ta koh ina in Daddy ya hana toh yanzu bata. For a moment tabar tunanin komai tuna maganan Daddy na karshe 'matsayin qanwa' that means she lost all the right kuma Anwaar ya yanke shawara shima, wato bazai maidata ba kuma bazai bari tayi farin ciki ba, so kawae yake ya kasheta da bakin ciki shiyasa ya yarda da komai, tasan bazai fasa san matansa ba, sannan ita kuma kaman yanda Daddy ya fada saidai ta zama er kallo, komai Ilhaam ce zatayi deciding tunda ita kadai ce matansa, yes her anger is justified kuma ae ya zama dole tayi kishi tunda akan soyyayyah takeyi, ita fa ba rayuwan data zabar wa kanta ba kenan, da gudu ta tashi tayi wajen Yaa Sakina dan yanzu abunda ta iya kenan, bata iya komai wa kanta saita tambayi shawara gudun kar tayi abunda ba daidai ba "Toh Fatima ya zama dole mu bi umarnin mahaifin ki, kuma harshi Anwaar ya yarda toh ae magana ya kare" tace "Yaya wlh Anwaar mugunta yakesan mun, so kawae yakeyi ya tara mun bakin ciki. Ni na hakura wlh zanyi karatu ah cikin Abuja ae ba mutuwa zan ba, amma haka kawae naje chan, wai fa matsayin qanwa Daddy yace. Kenan banida daman komai sai ganin abunda zai kasheni?" Yayaa tace "Kiyi haquri Fatima duk zai wuce. Kuma hakan gata aka miki. Maybe shi Anwaar baisan rabaki da yaron ki gabadaya yasa ya yarda da zamanki ah chan, kije kiyi karatun ki ah nitse ki samu ki kula da yaron naki" kallonta Teemerh tayi tana girgiza kai "Duk fa bazaki gane ba Yayaa, dole su zasu kula da Fadel saboda both the couple loves him amma miye na Anwaar da zaiyi sponsoring education ina kuma ya yarda na zauna dashi? Na gama iddah kuma hakkin kulawa na akan sa ya sauka, kuma yafi kowa sanin hakan" ta fada ah dame "Who knows koh zaki koma gidan nasa matsayin matan sane?" Kallon Yaa Sakina tayi tana share sauran hawayen nata "Yayaa that's delulu, I don't want a false hope saboda nasan bazai yiyu ba. Na riga na karbi kaddara ta tun kafin nasa araina zan koma yazo bai yiyu ba. We did more than enough for that family, ba wanda bamu tab'a ba cikin su, sunan mutane kadan ne baije wajen boka ba. I regretted this to date. Anwaar's family showed me love, nasan bani shiri dasu Ashphert amma wlh bayan su duk dangin Anwaar sona suke amma ni mey na taba yi?" Kallonta Yaa Sakina tayi ba amsa, ita taso da kawae tunda abu ya wuce subar tunawa "Kinsan mey nayi? I cheated on the one who trusted me the most after Anwaar, he is Aameer. Har wajen wani boka nida Beey mun koma dan asa soyyayyah tsakanin Aameer da Ilhaam mey daurewa yanda hakan zaisa ta samu matsala da Anwaar har ya saketa amma mey? duk banyi nasara ba. Duk saboda kishi nayi duka wannan kuma sai yanzu da lokaci ya kure mun na gane nayi ba daidai ba? I hate to call myself a selfish being but I was. Na yanke shawaran zama tare dasu Anwaar koh dan na sake jin wani zafin bayan wanda nakeji yanzu. Ni ba kowa bace face mugu-" bata karasa ba kukan da takeyi yafi karfinta "Fatima komai yayi zafi maganin sa Allah, kuma kikace zaki zauna tuna abubuwan da kikayi bazaki tab'a samun nasara ba, kullum gani zakiyi cewan kinyi cuta kuma hukunci ne ya dace dake which ba haka ba. You were good and still are" sautin kukan ta rage maganganun Yayaa na shiganta, ita kanta tana tunanin she's good wani lokacin dan akwae abubuwa da yawa da bataso ayi ba amma su Aunty Sham suka dage akai, akwae lokacin da sukace kashe Ilhaam ya dace ayi, bataso ba amma ta bisu saboda kar su ga amfanin kanta ne amma tana ki "I love Ilhaam, she did more than enough. I misplaced my friendship for a man" kukan ta cigaba dayi dan hakurin duniyan nan da lallashi ba wanda Yaa Sakina bata mata ba amma Teemerh is blaming herself for everything that has happened "Toh yanzu kukan zai dawo miki da komai ne Fatima? Duk kuskuren nan munyi sa amma ke haryanzu kin kasa yarda cewan kinyi nadama?" Aunty Sham data karaso ta samu draman tasa baki itama "Allah kikaje depression in yayi leveling ke zaki mutu" Yaa Sakina tace "Aa yi mata ah hankali. She's going through enough kuma rarrashin ta ya kamata ayi" jin hakan ne ma Teemerh ta sauke ajiyan zuciya ta fara kokarin kwantar da hankali tunda haryanzu akwae masu goyon bayanta amma hankalinta yaki kwanciya "Kije maza ki shirya kiyi wanka kinsan yau amaryan mahaifin ki zata iso" kallon Aunty Sham tayi jin abunda tace, haka kawae kuma taji ba dadi wa Mummy, abunda take yaqi akai kar ayi mata gashi anyi "Allah yasa mu dace" kawae ta iya cewa ta tashi "Kar kice zaki kira Anwaar kan maganan da akayi tunda bakisan dalilin sa ba" da toh ta amsa ta wuce dakin dan koh ba'a ce karta kirasa ba ita dama ba kiransa zatayi ba. Kai ina, saida taje daki taji idan tabar Anwaar cutan ae yayi yawa kawae ta dauko waya ta kirasa, batayi mamaki ba ganin bai dauka ba, sai chan ya kirata kawae ta fara mamakin kiran kuma "Ina yini?" Ta daure ta fad'a "How's Fadel?" Ya tambaya ba tare da amsa gaisuwan taba dan Fadel ne one of priority nasa, shiru tayi ta rasa wani karyan zata masa dan yana wajen Yaa Xee sunzo Abuja, kuma tasan yanda bayiso yaji dansa wani wajen "Yana lafiya, sorry to say amma yana wajen Yaa Xee sunzo Abuja" ta fada masa gaskiya, bai sake ce komai ba yayi shiru danjin dalilin kiran nata, baisan wani dogon zance da Fatima yasa yabar maganan ah haka "Kace ka yafe mun, amma why? Na kasa yarda ka yafemun dagaske bayan abunda Daddy ya fada. Nasan so kake na wahala bayan na zauna tare da ku. I can't, please ease my pain" tana fada tasa masa kuka, shiru yayi saida ta gama kukan nata kafin ya fara magana "Hush you know what? To regret is very easy, but it is very hard to atone, yet your education and everything was decided by me kafin na rabu dake. Daddy yasan hakan kuma ya yarda. Yes, I intended to punish you with this, I want to see you in pain, amma duk wannan ya faru ne kafin na yafe miki. Bayan na yafe miki kuma komai ya wuce, I can't hurt you that way. I am to love Ilhaam before your eyes but not anymore, how can I say no to your Dad? In bakiso toh ki same sa ki fada masa, I have no qualms. You can oppose your Dad but I can't" kuka takeyi amma jin abunda ya fada ta share hawayen tana tunanin sentence nasa na farko kawae taji sabon kuka, dama tasan hukunci yaso yayi mata, wato taje taga yanda zaiso Ilhaam koh? Men are scum but he now can't oppose her Dad then how can she? Ya zama dole tayi hakuri da duk hukuncin da Daddy ya yanke. Yanzu tasan dole ta gani taki gani kawae, amma zamanta tare dasu Anwaar tana ganin soyyayyan su is the worst decision "I can't oppose my Dad too. Thank you, am hanging" kafin ta kashe ma ya rigata kashewa, dan karamin tsaki tayi ta yarda wayan ganin abunda Anwaar yayi tasa kuka, saurin sake jawo wayan tayi zata kira Shareef ta tuna batada digits nasa hakan yasa ta texting Amrah kan ta tura mata, and within seconds ya shigo "Assalamu Alaikum, Miss Fatima Shettima speaking please" ta fadi bayan Shareef ya dau wayan "Wassalamu Alaiki, How are you doing and Fadel?" Tace "Fadel is fine, but Fatima is not, can I meet you? The matter can't be on the phone" dan shiru Shareef yayi processing it, he actually hates to meet this girl haka kawae amma he can't say he hates her. He respects her for whom he was married "Shareef kana jin dadin yanda abubuwa suke? I can't be crying every day and night to sleep. I am battling sleep deprivation and I may be on insomnia if care is not taken. My Dad's bride is coming in today, I don't know whether you attended the wedding Fatiha or not but am scared she might not like me. I know you don't like my bond from the beginning and keep avoiding to me anyway. If Anwaar can agree to meet me then why you? They were here yesterday and.." kafin ta karasa ya tsaidata "He may but I can't Fatima, I will send my Invitation to you personally. Make sure to attend the event please" wasu hawaye ne masu zafi taji sun sauko mata "I want and accept the invitations that came directly from the heart. I can't burden your event" ta basa amsa "By Allah, this is wholeheartedly Fatima" ya amsa softly "See you there then. Bye" da haka sukayi sallama ta cigaba da kukanta.



💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now