💖💫RUDANI💖💫 68

63 24 66
                                    




Teeeeeeeeeeee♥️💫 Allah barmun ke!
~*~*

Kusan dai ranan ba'ayi bacci ba, Mummy ta dawo daukan Ilhaam ma en uwanta suka hana suka shaida mata ae Ilhaam matar aure ce ba yanda za'ayi ta tafi wani wajen bayan mijinta na nan, Ilhaam na tareda en uwanta tana shan gata, ita kuma Teemerh kwana tayi tana kuka ganin yanda Anwaar ya nuna ya damu da Ilhaam, kawae komai Ilhaam, ta masa magana ya bata haquri yace ae Ilhaam batada lafiya ne. Ashphert kuwa kusan kwana tayi tana fadawa Aameer cewan ita bata yarda da Teemerh ba, kusan saida sukayi fada kafin ya sauko yana bata haquri, ganin ta kashe wayan ya sake kira, saida ta bata masa rai kafin ta dauka "Teemerh ta muku asiri ae, and if I can remember dama kayi soyyayyah da ita. Nikam ae ka gama zubar mun da mutunci wlh" shifa sai yanzu ya tuna ma ashe wai yayi dating Teemerh "Look I am sorry" ya bada haquri "I will come over tomorrow da yardan Allah" tace "Are you coming to see Ilhaam, Ash or Yesmin?" Shiru yayi gane wa'innan biyun sun hadu kenan zasu masa trap "Toh have some sleep, make sure you pray Subh before sleeping gashi an fara kira" ok ta amsa sukayi sallama.


Washegari duk suka shigo duba jikin Ilhaam, harta fara sabawa da two women in dan yanda suke mata "Nikam ina Abbas ne?" Ammaah ta tambaya ganin duk abunda akeyi bai shigo koh sau daya ba "Sunyi tafiya tareda Daddy, wai zaman shi haka ya fara yawa" Leemerh ta amsa da sauri "Kun takura wa Abbas dai" Ammaah ta fada ita a dole backing Abbas take, Anwaar ganin wajen an fara yawa kowa da irin surutun sa ya tashi ya basu waje, shi kawae ya fiso ya gansa shi kadai sai kuma wanda ya zaba, ganin ya tashi Yesmin ta bisa suka karasa garden in "Anwaar I want to befriend her amma bata kulani" tana fada ya gane Ilhaam ne "It won't last long, zamu koma Abuja" ya mata bayani "Eh zamu koma muma, dama saboda Babane, tunda bayi raye zamu cigaba da zama a Abuja" murmushi kadai yayi yasan Ilhaam da Yesmin can never be friends in ba wani ikon Allah ba, ita fa Yesmin ba wanda ya iyane sai ita, ita kuma Ilhaam bamey gane mata sai Allah "Anwaar amma-" bata karasa ba taga Teemerh tayi shiru "Anwaar zamu koma yau ba? Nifa koh gidan Kakata dake nan ban samu naje ba" ta fada tana bin Yesmin da harara ganin Anwaar wajen, Yesmin batace mata komai ba dan ta riga ta rufe chapter'n Teemerh ta bude wani "I will check my schedule" ya bata amsa "Excuse us, magana mukeyi fa" Yesmin ta fada kawae Teemerh ta bude baki saboda mamaki, tana magana da mijin nata kuma ace wae ta excusing nasu "Lalle Yesmin bakida kunya, mijin nawa-" Anwaar cuts her off "Calm down" yana fada ya tashi yabar wajen danshi abu da tashin hankali baso yakeyi ba, ganin Anwaar ya bar wajen Teemerh tayi saurin bin bayansa kafin a barta daga ita sai Yesmin, tasan ta mata ba dai-dai dole ta kira en uwanta, tana shiga taga Aameer yazo, shi da ake shirin tafiya yana wani shirin zuwa, she forced herself to wear a smile kafin ta karasa wajen ganin Ash "Wai fa yau ake ta shirin komawa sai gaka yau" he has to check on Ilhaam, toh ae dole yazo, Billy na gefe tana cire masa pictures yanda zatayi neman tsokanan Leemerh dakyau dan kuwa tanada lectures ta tafi, saboda mugunta irin na Billy Yesmin fa tace mata Aameer zaizo amma taki fadawa Leemerh tasan inda tasan zaizo koh makarantan ba dubawa zatayi ba, ita wani dariya ma takeyi ah ranta tuna kadan Leemerh ta gani, one thing she noticed about the guy is that tunda yazo, yayi gaisuwa dai amma banda wannan bai sake yiwa kowa magana ba har shi wancan Anwaar mey shegen girman kai da baya yiwa kowa magana sai an masa kuma yaki amsawa, ita ta rasa miye abun so ah jikinsa da har Yesmin zatace wai Anwaar ya rabu da ita harda rashin lafiya, shigowan su dazu fa ta gaishesa wai dan kar ace taga mutum batayi gaisuwa ba amma da ikon Allah koh kallonta bayi ba which she is sure yaji amsawa ne bazai yi ba, biting finger tayi tunawa da tayi tana ce da bata gaishesa ba "Yaa Aameer Ammaah na neman ka" Xeenerh ta fito ta fada masa sakon Ammaah, kallonta yayi sai kuma ya sake sauke ido kasa, kaman ya tuna wani abu ya sake kallonta jin yanda tayi maganan harda bata rai kaman batasan aikan "Xeenerh I don't know how you end up giving birth to a cute baby" yana fada ta bata rai, shi fa Aameer da wuya ta masa magana bai kare mata tanadi ba "Still prettier than Ash" ta bashi amsa harda murguda baki "No Ash is the cutest being" Ash dake gefe baji tayi bama dan bata sa ran sauraran conversation din ba "Yaa Aameer, she is waiting" ta maimaita kanta "Ohh yes" yana fada ya tashi "Kinada yaro?" Bilqis ta tambaya tana sake kallon Xeenerh, banda Teemerh da ta nemi waje ta zauna saboda kawae ta nemi Ashphert da fada Anwaar yaci mata mutunci, little did she know that itama mijin ta na nan ba bari zaiyi aci mutuncin matan sa ba "Yes Affan" Ashphert ta amsa mata "Seeeee" harda tashi ta karasa wajen Bilqis tana nuna pictures in Affan sai na Fadel kuma "Shi kuma wannan yaron waye?" Bilqis ta tambaya hakan yasa Yesmin dake gefe sa kai dan ganin wani yaro ne, kallon Teemerh Ashphert tayi ta harareta "Yaron Anwaar, karki tambaye ni Mamansa dan ba Ilhaam bane" tana fada Bilqis ta kalli Teemerh tasan itane tunda Ash taqi kiran suna, basu wani dade dasu ba amma ta gane su biyun basu shiri "Sai ki samar masa wata uwar ae tunda kinga namiji zai haifi yaro ae, just rephrase your words 'Yaron Anwaar ne' hypocrisy at it's peak, banda munafurci kina son Fadel kina san ubansa, har kishiyan uwan sa kina so amma baki san uwan sa" ta fada tana kad'a kai "Halin ki baida kyau shiyasa-" kafin Ashphert ta rufe baki Teemerh ta chapke "Ke halin naki kyau yake dashi ae, shiyasa ma Allah ya hanaki haihuwa saidai kiga na wasu ki changing musu iyaye da baki" da sauri duk suka kalli Teemerh sannan back to Ashphert data fara hawaye, she got a very sharp mouth but this is her weakness, har ita Teemerh zata ma gorin haihuwa koh bataga yawan gidan su bane "So nakeyi naga kina kuka, kuma haka rayuwan ki zai kare a kuka Ashphert" Xeenerh tace "Ah haka kikeso muyi welcoming naki cikin mu Teemerh? At least Yaa Aameer loves her so much but your love still has a question tag. Your husband loves someone else. Doesn't he?" Ta fadi haka itama dan ta batawa Teemerh rai gashi kuwa ran nata ya baci, saboda that someone da Xeenerh tayi mentioning tasan Ilhaam ne, tashi Teemerh tayi tun wuri tabar wajen ta fara neman Anwaar dan batada aikin da yafi wannan "Kiyi haquri Ash, in tana haukanta kubar kulata, tayama za'ayi ita tace haka" Yesmin ta bata haquri, ita Xeenerh kallon Ashphert takeyi amma jin Yesmin tayi magana tsaya mamaki, wato ta cire Teemerh a rayuwanta ma saboda bata dauketa da wani mahimmaci ba yasa tace in tana haukan ta abar kulata, itadai Yesmin in tana sanka toh zakuyi mutunci "Yess is right" Bilqis ma ta amsa, tashi tayi da sauri Xeenerh zata bita ta tsaidata "I want to be alone for now please" dakai Xeenerh ta amsa ta koma ta zauna, sunkai 30sc kafin Billy ta breaking silence in "Sorry to say amma wancan Anwaar in yanada jiji dakai, ya akayi ya auri mata biyu?" Yesmin tace "Billy bansan gulma, that too Anwaar is not arrogant kawae dai baki fahimce sa bane" ta defending Anwaar "Har yanzu kina san Anwaar ne?" Xeenerh ta tambaya ganin duk lokacin da aka kawo laifin Anwaar sai ta karesa, girgiza kai tayi alamun Aa, kallon juna kawae Bilqis da Xeenerh sukayi not knowing what is going on each other's mind, Yesmin is so innocent and she deserves love, beauty doesn't guarantee someone an everlasting love, inda kuwa hakane da Ilhaam da Yesmin basu wahala ba, kawae dai komai sa'a ne da kuma abunda Allah ya rubuta maka.


💖💫RUDANI💖💫Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu