💖💫RUDANI💖💫 98

36 20 128
                                    




Epilogue 1



*****5 YEARS LEAP*******





~_Kuje Prisons_

Teemerh, Daddy, Yaa Xee, Auntie Sham, Habeey, Mallah, and Sadeeq, sai Aunty Benazir, suna tsaye suna jiran fitowan Mummy dan kuwa ta cika 5yrs nata. Fitowa tayi cike da nutsuwa wanda har Teemerh da Xee sun fara kuka, suna ganinta sukaje da gudu sukayi hugging nata itama sai kuka, har tayi duhu dan kuwa fara ce sosai kuma ta rama, bawani wahala ma take sha ba amma abu in ba ah gidan ka kake ba. Kuka suka tsaya sunayi tsakanin su da Allah "I..- I missed you Mum" Teemerh tayi stuttering tana kuka "I missed you all Fatima. Allah yayi muku albarka" ta fada sannan tayi breaking hug in ta karasa wajen Daddy, kokarin tsugunawa tayi ya riketa "Aa Malika dan Allah karki kunyata ni, na yafe miki duniya da lahira, burina ki yafe wa yaran" tace "Na yafe musu Alhaji nima ki yafemun Zainab, Shamsiyya kema ki yafe mun" hugging nata da sauri Sham tayi tana kokarin wiping tears nata "I love and missed you Yaya" tace "I missed you too Sham and I love you more. Nasan nayi kuskure amma dan Allah ki yafemun na tuba yanzu kam" Shamsiyya tace "Yaya nima na bada contribution gashi ke kadai kikeyi serving punishment" tace "Aa ni kadai nayi laifi na kuma ni kadai nayi serving punishment, suma gidan Albaaz in inaso naje na basu haquri. Yasu Mama achan Chad? Tasan abunda ya faru koh?" Kallonta duk sukayi, hawayen da Shamsiyya ta share wasu suka sake saukowa "Yanzu dai duk ba wannan ba muje gida ki huta kici abinci tukunna" Daddy ya fada sannan ya kama hanunta sukayi mota. Gida suka koma bayan tayita musu wasu koke-kokenta saboda Aunty Sham ta kasa haquri ta fada mata Maman su ta rasu. Duk kansu suna zaune a katon palon Daddy suka ga Mummy ta fito bayan tayi wanka taci abinci kadan haka dan farin cikin fitowan ta bazai barta taci da kyau ba, samun waje tayi ta zauna kusa da Teemerh ta jawota jikinta "Nasan na miki laifi-" girgiza kai Teemerh tayi "Mum nice nayi miki laifi ba keba please" tayi saurin tsareta "Waye wannan kuma?" Tayi nuni da matan Daddy "Sabuwar matan Daddy ne" Xee ta amsa da fara'a fuskanta dan mugun shiri sukeyi da matan sam bata musu wani hali, wani hawaye Mummy taji ya sauka mata dan tasan inda bataje prison ba mijinta bazai mata kishiya ba amma it was for the good. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Benazir kaman yanda na fada miki dama kafin na aure ki inada aure kuma kema kinsan da haka, gashi yau Allah yayi haduwan ku" ya fada looking at his second wife "Hakane Alhaji, Allah ya kara mana zaman lafiya. Ina yini Yaya" ta gaishe da Mummy "Lafiya qlau Benazir, Allah ya dafa mana" Amin duk suka amsa "Ga Habeebah kaman yanda kika gani haryanzu batada aure, Habeebah ta samu mijin auren amma tace a jira fitowan ki tukunna, sannan Fatima ta maida hankali kan karatun ta kuma Allah ya taimaka ta kammala" murmushi Mummy tayi tace "Habeebah nagode da karamcin da kika nuna mun. Allah yasa ayi ah sa'a" Sadeeq da sauran suka amsa da Amin, kallon yaron dake hanun Benazir tayi, sosai yaron yake kama da Fatima which she's sure yaron tane, tanaso tayi tambaya saidai tana tsoron ace ba gidan Anwaar kaman yanda takeso ta koma ba, saurin barin tunanin tayi tace "Ke takwara yaushe ne auren naki?" Mummy ta tambayi Mallah "Ae Mallah tayi aure Yaya, amarya ce" Shamsiyya ta amsa "Maa Shaa Allah. Allah Ya sanya alkhairi" Daddy yace "Ita kuma Shamsiyya tsohon mijinta da yaranta sun yafe dukkanin abubuwan ta sannan abokina Alhaji Garba shine wanda zai aureta, ae kinsan shi koh?" Gyad'a kai Mummy tayi tana "Masha'Allah, Allah ya sanya alkhairi a rayuwan mu gabadaya" ta fada bayan ta gama jin bayanan. Daddy dai sai Alhamdulillah yake maimaita wa Malika ta shiryu tana magana ah nitse "Zanje bada haquri-" kafin Mummy ta karasa Teemerh tace "Mummy sun yafe miki wlh" girgiza kai Mummy tayi "Ae koh sun yafe mun dole naje dakai na. Yasu Ilhaam da Fadel?" Murmushi tayi danko dazu sunyi waya ta fada mata zasuje dauko Mummy, tayi missing su Ilhaam "Tace a gaishe ki, Fadel ya girma sosai" murmushi duk sukayi jin haka. Life has been better nah? Life has been better, better than ever. Ilhaam, Ash, Leemerh, da itama Teemerh duk sunyi graduating. Xeenerh da Yesmin sun cigaba da karatu, Xeenerh kam ma is pregnant with her second child saidai cikin karami ne. Ashphert kuma dagaske ne dai kaman maganan bazata sake haihuwan ba. It's only love, love, and nothing but love and tranquillity. Kowa yana farin ciki, yeah it supposed to be happy nah? Waiting for me to mention the guys? They are fineeeee. Anwaar and his guys are the best husbands and Fathers. Anwaar wants Babies? Yes, he still love Babies amma shida kansa yace Ilhaam ta nutsu tayi karatu, she did that and make him proud, her health is good dan ba sosai ranta yake baci ba. Aameer is now a SAN, and Aameen is next to take after the Albaaz Enterprises as the CEO. Bayan an gama en bayanai da wasu tadi kowa ya nutsu Teemerh tabi Mummy daki, yau batajin zata iya bacci bayan fitowan Mummy "Fatima shin Anwaar ne ya sake auren ki?" Mummy tayi mata unexpected question, saurin sunkuyar dakai tayi kawae tayi murmushi, sai hawaye daya biyo bayan haka "You cursed me that day Mummy, blessing went the right way and I went to the left" kallonta Mummy tayi dan haushi taji ta tsine mata amma tayi nadama "Toh yanzu mey kike nufi Fatima?" Murmushin kadai ta sake tareda share hawayen ta tashi da sauri tabar dakin dan yanzu ta gane dalilin kukan Ilhaam kullum da.



💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now