💖💫RUDANI💖💫 87

45 24 69
                                    



Aameer sun dawo lafiya danshi Allah ya gani baiyi niyyan dawowa ba, shi ya tattara ya tafi kenan saidai yana zuwa visiting en uwa a Nigeria, amma yanzu ya zama dole ya dawo saboda ayi komai ya wuce, ganin Anwaar ya iso ya sake gyara zama "Man you can't believe what Captain is gonna tell you" Aameer ya sanar dashi "Na mene?" Ya tambaya ah nitse bayan ya zauna "Anyi tracing number'n da akayi messaging Captain, kuma anan Abuja aka turo message in" shi dama yana ji ah jikinsa ah Abuja ne amma wa? "Toh meya faru?" Anwaar ya tambaya curiously "Captain fada masa" ciro waya Aameen yayi sannan ya nuna ma Anwaar location in wajen "What do you mean?" Ya tambaya da sauri yana kallon su "Gidan su Fatima ne fa" ya fada ah dame "Yes, daga gidan akayi" Aameer ya amsa "Whatt!?" Yayi exclaiming "We were shocked too" Aameen ya fada kaman a dame dai haka "Then who purposely texted that?" Ya tambaye su ah hankali "That must be Fatima, but why could she do that? That woman is her Mum" ya amsa abunsa "Whatever, sunan su duka yana court yanzu haka" Aameer ya amsa dan yanzu yasa rai wa abun sosai "When za'a sake zama?" Anwaar ya fara calculating dan baisan zuwa yasan dole this time suje dan duk sunan su na wajen "In 4days" Aameer ya bashi direct amsa "You mean dole fa muje this time around" Aameen ya tambaya "Of course" yace "Allah ya kaimu", "Amin" suka amsa both kafin Aameer ya amsa kiran Yaa Humainah "Yes we are home, sai kin shigo" ya fada sannan ya ajiye, shifa ya zata ita kadai zata zo kawae ta kwaso musu mutane "Yaa Hummy, mey Xeenerh da Ilhaam zasuyi anan?" Aameen ya tambaya da mamakin ganin su "We of course need Ilhaam, zataje court saboda Mufeed ya bukaci hakan" Aameer ya bashi amsa, ware ido tayi dan ita yanzu takejin maganan fa "Ilhaam kuma?" Ashphert da fitowan ta kenan ta amsa "Ni bazanje ba, I can't" ta fada tana girgiza kai "Ilhaam you have to, please" Anwaar yasa baki, har wani zufa ta fara dan Ilhaam matsoraciya ce na karshe "Erm.. ina Nihaal?" Ta tambayi Ashphert dan so take ta gudu a wajen "Tana daki, follow me please" ba musu ta tashi ta bita Xeenerh ma tabi bayan su "I need to meet Fatima right away" saurin tsaida sa Aameer yayi "You can't do that, her Mum is home. She is your wife so call her here" he suggested "Yes Aameer is right, she won't open up comfortably at home" shiru dakin yayi kafin Humainah tace "Toh wae meyasa bazaka dawo da ita ba? Anwaar in sakin yarinyan nan kayi ka fito fili kawae ka fada amma ban gane da auren ta kanka tana gida ba" nan fa two men suka amsa "Abunda kullum muke fada masa kenan, you punished her, then forgive her" Aameen ya amsa dan bai ga dalilin barinta gida ba "You can't convinced me more, yarinyan nan batayi hankali ba, duk abunda nace kar tayi shi takeyi. She is Fadel's Mum and I respect her for that so please stay outta it, duk sanda tayi hankali her father will let me know, and I ain't calling her back home or here, I will go in taga dama kar ta fadi abunda takesan fada. She is still under my punishment for trying to hurt Ilhaam" dan karamin tsaki Aameer yayi "Shin kai kana adalci wa matan ka kuwa?" Aameer daya kasa haquri ya tambaya jin wae duk abun saboda Ilhaam yakeyi "Ae ba wanda yake adalci daman, kwatantawa nake yi, yes inda Ilhaam zatayi wani abu irin haka I will punish her too, ina hukunci sosai wa Ilhaam kawae baku sani ne. But I can't love them equally Barrister Aameer, I love Ilhaam and her more" ya fada musu gaskiya ma tun kafin a fara wani zancen "Leave all this please" Yaa Humainah tasa baki "Shknn, I will take my leave" yana fada ya tashi ya fita zuwa gidan su Fatimah. Tashi Yaa Humainah tayi itama zuwa wajen su Ash dan ce musu zata tafi "Yaa Hummy, ni damuwa na yanzu shine a samarwa Mami adalci, I don't care whether it was Teemerh's Mom or Teemerh herself" Xeenerh ta fadi abunda ke ranta "Allah ya tabbatar, nizan wuce" Yaa Humainah ta amsa "Ya kamata but I still I can't believe Teemerh's Mom can do this. It's terrifying" Ashphert shook her head in disbelief "Toh yanzu dai Anwaar yace zaije wajen Fatima, she might tell him what he suppose to know earlier" kallon juna duk sukayi kawae ba wanda ya amsa.




Halimah ta fita hanyan Aameer, Abbas ke mata dariya kullum dan baida aikin da yafi wannan, Asma'u still the same girl, attitudes kam saidai abunda ya karu, kawae dai yanzu ana samun saukin lamari ne saboda mey amsata Bilqis ne kuma tayi aure "Halimah yaushe zaki karbo transcript?" Abbas ya tambaye ta dan tun dawowan su Abuja koh fita batayi balle tayi maganan karatu, ita yanzu tafi san zaman Maiduguri kan Abujan nan, kullum taje gidan Maāmaa koh su Ilhaam suka zo sai Aameer ya kirata, she hates his voice, she can't say she hates him tunda duk ita ta jawa kanta komai amma, she can't change to English Education again da kuwa tayi hakan "Halimahhh" ya fada snapping her outta her thoughts "Koh yaushe ma" ta fada ah hankali dan yanzu Law ya mugun fita ranta, gani take in ta zama Barrister kaman itama girman kan zata fara kuma bataso "Yaa Abbas inaga zan cigaba a Unimaid, in anyi hutu sai ina dawowa" ta fada ah hankali "Halimah bakida ra'ayi guda daya? Karatun nan fa ba dole bane sai kiyi aure mu huta" Asma'u da tazo wuce wa saboda neman magana ta fada "Mijin kine mara ra'ayi tunda ya yarda da aurenki" ta bata amsa da harara, haushin irin shishigin da Asma'u keyi kullum take "Take things easy, please. Mummy Khalifah kiyi haquri" Abbas ya bata haquri ganin ranta ya baci, kallon Halimah tayi ta girgiza kai irin zamu hadu kafin ta wuce "Meyasa kake bata haquri? She's a trouble herself" Halimah ta fada masa "Haleemah that woman is Yaa Najeeb's wife and she's good, rashin kunya kuke mata fa. How do you expect her to react?" Leemerh tace "Amma tana shiga abunda ba ruwanta, dan ita zata dawo Baze University sai kowa ya dawo? Mijinta ke biye mata ae" ta fada cike da bacin rai da regretting rashin nutsuwa ta karasa karatun ta chan Columbia "Asma'u tanada kirki sosai kawae baku fahimta bane, so takeyi ki nutsu kiyi karatu shiyasa tace haka. Baku shiri sosai shiyasa bazata zauna ta baki shawara ba" ya mata bayani "Ba wanda baisan bata san mu ba, dakai kadai take shiri saboda kaima tasan kai namiji ne, haushi takeji saboda mu mata ne, banda jahilci inda auren namu zaiyi sai an jirata ne? Kishin banza da wofi" ta fada rai bace dan mugun 6ata mata rai Asmah keyi "Chill, am going to the office. Sai na dawo" yana fada ya tashi "Yaa Abbas office koh gidan Maāmaa wajen Ilhaam?" Ta tambaya dan tasan bawani san zuwa aiki yake ba, wae shi a dole shi zai zama next CEO "That girl is my relative, laifi ne in naje wajen nata? Learn to mind your business Halimah" shiru tayi ganin kaman zai fara fada "Kayi haquri, my regards to them all" tabar maganan ah haka, koh kulata baiyi ba ya fita, shiru tayi ta fara tunanin ta cigaba da chan Unimaid koh ta dawo Abuja, ita duk karatun ya fita ranta yanzu, dan karamin tsaki tayi tuna wancan Aameer ne yaja mata komai, waya ta dauka kawae taga yayi sabon post, hoton sane da Ilhaam though tasha lullubi zallan face nata ne ya fito da captain "Meeting Baby after a long time" tsaki tayi kafin tayi liking hoton kuma, ta lura bai wa Ilhaam girman kai ae watam ita ya raina, har tayi typing comment ta goge ta ajiye wayan gefe, tashi tayi zata wajen Mummy dan shawara akan karatun ta kawae taga Abbas ya dawo "Yaa Abbas?" Ita ta zata yabar gidan fa "Ilhaam tace tana hanya" yana fada ya wuce, rolling eyes tayi ta wuce wajen Mummy kafin Ilhaam in tazo, kullum tazo fa sai sunyi da Asmah kuma tasan yau ma za'ayi. Abbas kam daki yaje yasha baccin sa dan ba wani aikin da zaije, saida ya gama baccin sa ya fito zashi masallaci kafin yaga Ilhaam wae ahaka bata dade da zuwa ba, ita da sukayi waya tace masa tana hanya "Ilhaam shiririta, tun dazu a hanya kika maqale?" Girgiza kai tayi "Maāmaa tace bazan zo ba da, sai da Bilal ya kawoni" ta masa bayani "Zani Masjid, barin dawo" yana fada ya fita "Muje ki gaida Yaa Najeeb" Leemerh ta fada tana kokarin kama hanunta ta kwace "Ni bacci zanyi" ta tashi zata wajen Mummy dan ita tsoron Asmah take, tanada mutunci indai bata ga ana wa Najeeb magana ba amma batada mutunci koh kadan ta gansa da wata "Kawae kice mun tsoron matan sa kike" Leemerh data gane ta fada, shiru ta mata ta wuce dan ana zaman lafiya bazata nema wa kanta tashin hankali ba, binta da sauri Leemerh tayi zuwa wajen Mummy'n dake Kitchen "Mummy zansha, har kin gama?" Leemerh ta fada ganin Mummy ta gama hadawa Najeeb kunun gyad'a "Ki zuba naki dana Ilhaam sai ki kai masa" tun daga jin haka Ilhaam ta juya zata fita Leemerh ta tsareta "Ki tsaya mu kai masa" girgiza kai tayi "Ku kai masa Ilhaam, kina exercise kema" Ilhaam tace "Ita fa?" Mummy tace "Asma'u ta fita anguwa dazu tamun sallama ae" ana fada taji ranta yayi sanyi akabar Leemerh da mata dariya "Dama nasan tsoron ta kike ae" Mummy tace "Toh ae ba laifi bane in mutum yaki tashin hankali" nan fa ta supporting Ilhaam "Kunu da yamma?" Ilhaam ta tambayi Leemerh bayan Mummy ta fita "Ana fada miki halin guy in ae baki wani yarda saboda kinga ke bayi miki komai, kuma Mummy ke kara daure masa ae kina ga da kanta ta masa fa bayan yanada mata, wae in tayi yafi dadi" shiru Ilhaam ta mata dan har zata amsa Abbas ya shigo hakan yasa ta manta mey zatace "Yasu Maāmaa?" Ya tambaya "Suna lafiya" ta amsa ah hankali "Wae zaku shiga court koh?" Girgiza kai ta fara "Nifa banso, amma Anwaar yace-" kafin ta karasa Leemerh ta chapke "Keda Yesmin kunji jiki, ke komai Anwaar ita komai Rafeeq kaman kap duniya ba maza sai su kadai. Haba ku bari mu huta mana, da wasu mazajen ku masu shegen girman kai ma" dariya Abbas ya fara "Sai ki nemo miji kiyi aure ki daina jin haushi. I am missing that Yesmin, barin kirata" yana fada ya fita "Muje" Halimah bayan ta gama hadawa tayi maganan "Wae Yesmin bazata dawo ba?" Ta sake tambayan Ilhaam "Zata dawo, kinsan za'a fara zaman case in and Rafeeq want to attend" Ilhaam ta fara bata labari suna tafiya part in su Najeeb "Dazu naga pic naki da Aameer" murmushi Ilhaam tayi tuna yanda ya dage sai anyi hoton chan "Munyi kyau ba?" Tace "Kinyi kyau dai, shi bai mun kyau ba" Ilhaam tace "Allah ya shirye ki, Aameer is one of my favorite humans, yanada kirki sosai" dan karamin tsaki Leemerh ta fara dan bata wani bukatan bayanan Ilhaam "Yesmin showed me his house the other day, meyasa yake zaune anan?" Dan shiru Leemerh tayi kafin ta gane wae Najeeb Ilhaam ke nufi fa, bata kiran sunan nasa koh meyasa oho "Barin fada miki gaskiya shi Yaa Najeeb is more than obedient itself. Yanada biyayya sosai shiyasa komai ba'a tambayan shawaran sa kawae saidai ah yanke hukunci ansan bazai ce Aa ba. Daddy ne ya dage wae saidai ya zauna anan ya fisan su zauna waje daya, amma wlh Yaa Najeeb baisan zaman, inda Yaa Abbas ne bazai yarda ba" shiru Ilhaam tayi dan harta fara sympathizing Najeeb, wani lokaci aka lura kanada biyayya anfi matsa maka "Kuma kinga baisan zama Policeman amma Daddy ya nuna interest kawae yace toh. Da yanzu shine CEO na company'n Daddy" Ilhaam tace "This is terrible" sai kuma tayi saurin rike baki, ashe Najeeb is hiding so many pains, shiru kawae yakeyi saboda ba wanda ya damu yasan damuwan sa. Shiru duk sukayi har suka karasa wajensu Najeeb, zai fita wajen su kenan suka shigo hakan yasa ya koma "Ina yini?" Ilhaam ta gaishe sa "Lafiya" ya amsa a nitse "Zaka aiki?" Ta sake tambaya "Aa, zanje dubo Halimah ne dama" ya bata amsa kafin Halimah ta ajiye masa flask nasa, dauka yayi ya bude sai ganin kunu yayi, shi baisan wasu aljanu ke yawo kan Halimah lokacin daya bata aikan ba "Halimah I asked for coffee" ya fada da takaici, shifa dan sauri yake ae daya hada abun sa "Innalillahi" ta fara biting finger, ae kuwa abunda yace kenan fa "I can make some" Ilhaam ta tashi da sauri "No don't worry and don't stress yourself please, you deserve rest" ya fada sannan shima ya tashi dan zai fita kawae "Please let me, am used to making different types of coffee for Anwaar" tayi insisting hakan yasa Leemerh kallonta "Ilhaam you can't do that please, zan fita yanzu" Halimah tace "Haba Yaa Najeeb, I can help her" shiru yadan yi kafin ya amsa, aprons ya dauko ya basu shima zaisa suka ce ya bari kawae "What will you like to have? Latte, Black, or cold?" Ilhaam ta tambaya "Flat white can do" toh tace sannan ta koma, in less than 15min ta kawo masa ta koma dan hada masa dinner saboda rawan kai, basu wani dau lokaci ba Najeeb yayi joining nasu, simple dish sukayi making, Halimah ta gudu tana kama baya dan batasan aiki, ita Ilhaam kullum taga yanda Halimah ke qin aiki sai tace ta daure tanayi dan yanda tayi learning komai the hard way bataso kowa yayi, ita Leemerh taci sa'a ta iya ma amma bazatayi ba, ita kam lokacin da bata iya girki ba ae tasha wuya Allah yaso Anwaar is helping "Yaa Najeeb inace zamu koma Maiduguri dai?" Halimah ta sake tambaya dan batada abunda yafi wannan "Yoo, at the end ae dole mu koma tunda hometown kenan" Abbas daya shigo ya fada, kallon sa kawae Najeeb yayi ganin ya shigo ba sallama "Sorry Bro" ya fada gane dalilin kallon "Bakasan zuwa aiki koh? Nasan tun safe ba yanda kaje" Najeeb ya fada yana rating abincin sa da Ilhaam, dan sa hanu akai Abbas yayi kafin ya zauna "Ilhaam cooked this, and am sure about it. Serve me please" yaja kujera ya zauna, ba musu Ilhaam ta tashi ta zuba masa dan bata aikin komai wajen Maāmaa kullum saidai exercise, it was supposed to be dinner amma da dukkan alamu zasu cinye abunsu "When are you resigning the police work?" Kallonta Najeeb yayi gane dashi take, inda sabo ya saba da bata kiran sunan, kawae dai cewa yake hala dan bayi wani kiran sunanta yasa bata kiran nasa "Why? It's my profession" ya bata amsa "It suits not an introverted someone like you" ta sake fada "Yeah Dad wants it to happen, and Yaa Najeeb said Yes" Abbas ya fada mata, ita already dazu Leemerh ta fada mata ae shiyasa take so yabar abunda bayiso zuwa wanda yakeso, he's not a child and it's high time Daddyn nasu ya gane haka "You were forced to?" Kallonta kawae yayi baice komai ba, shi baisan magana mey tsayi da wannan yarinyan dan anjima kadan zata fara masa kuka, and Mummy will blame him "I would like to see you improve, life is too short to be-" Leemerh ta chapke kafin ta karasa "Ilhaam improve yourself first, keda Yaa Najeeb in ae kusan daya kuke, kefa har wa Teemerh ya kama kiyi kuka yi kikeyi" murguda mata baki tayi kafin ta tashi dan dama spoons baifi uku ba tayi tun zaman ta wajen sai surutu kaman danshi tazo duniya. Saida duk suka gama kafin suka sameta livingroom in, tadi suka sha har Najeeb ya manta zai fita, saida Ilhaam ta lura Asmah ta kusa dawowa kafin ta gudu ta barsu.




💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now