💖💫RUDANI💖💫 55

89 25 33
                                    


Asibiti direct suka wuce harda Aunty Sham uwar en shishigi da rashin san zaman lafiya, ita so ma takeyi Ilhaam in ta mutu dan yanda Anwaar ya dauko ta kaman ba rai ah jikinta, ah hospital premises ya hadu da Aameer dan ya gaji da jiransa sa zai tafi, ganinsa da Ilhaam yayi saurin karasawa wajen saidai ya lura Anwaar in ma hankalin sa bayi jikinsa, ER aka wuce da ita direct sannan Anwaar ya dawo reception ya zauna ba tare da yama kowa magana ba, he's a doctor amma bayi tunanin zai iya wani abu yau, Aameer ne yayi saurin biyo sa da Teemerh, Aunty Sham biye da ita "What happened to her?" Ya tambayi Teemerh da ta samu waje kusa da Anwaar ta zauna, girgiza kai tayi alaman bata sani ba "If you can't take good care of our girl, then send her back home, zamu kula da ita yanda ya kamata" Aunty Sham naji taji ranta yayi fari dan yanda Aameer yayi maganan tasan Anwaar bazai barsa ba, little did she know that in ransa ya baci bayi amsawa, to her surprise kuwa baice komai ba, zai tashi Aameer yasa hanu ya rike sa "Sakeni" ya fada ah tsawace hakan ya maida hankali mutane wajen, da sauri Teemerh ta tashi "People are watching" tayi whispering "Let them watch" Aameer yelled "Anwaar ka shirya kulawa da Ilhaam kuwa?" Kallon mamaki ya masa kafin yayi faking murmushi "Cameras off please" yayi pleading wasu mutane da yaga sun fara daga waya, zai wuce Aameer ya sake tsaida sa, shi he don't care as he's over the internet dama "Ban shirya ba, zaifi kyau in ka koya mun" yana fada ya wuce ya barsu tsaye wajen, nan fa Aunty Sham ta matso "Kayi haquri ae kasan halinsa" kallon da taga Aameer ya bita dashi ne yasa tadan matsa baya sanin ba jituwa zasuyi ba, saurin bin Anwaar yayi saidai kafin ya tsaidasa ya shige Emergency Room in, ta window ya duba yanda ya ganta kwance, Doctor Hafeez na kokarin sata under the life supporting machine Shareef ya hanasa, Anwaar na gefe bayi komai "Wait for us outside" Shareef calmly said to Anwaar, mamaki Aameer yayi though baiji abunda Shareef yace ba amma ya lura he wants Anwaar out, bayan yasan Anwaar is a Doctor also, baiyi wani jayya ba ya fita, Aameer na ganinsa ya karasa wajen. Back to Aunty Sham, ganin shiru kuma Teemerh na wajen ta jawota "Wawiyan banza, ki fara kuka sannan kije ki samesa" kallon rashin fahimta ta mata "Kuka zaki fara ki gwada amsa kin damu da ita" bata rai tayi, akan wani dalili zata wahalar da hawayenta kan Ilhaam "Zaki wuce koh Aa?" Ganin dagaske Aunty Sham keyi yasa tayi saurin barni wajen ta fara neman Anwaar, suna tsaye both jikin window hakan yasa ta karasawa ta rike hanunsa, juyowa yayi ah nitse jin wani soft hands ya rikesa "Zata samu sauki" ta fada hakan yasa Aameer ma juyowa "Ina yini" ta fada tana miqa masa hanu alamun su gaisa, kafin ya bada hanu Anwaar ya rike "Fatima is my wife" jin abunda ya fada yasa ta kallesa da sauri, shi kuma ya sake hanun nata, the first time if she could remember yayi addressing nata haka, ita kanta tasan batajin maganan dan this is not the first time ya hanata wannan shirmen, kafin tayi aure she find it normal, but after marrying Anwaar ya hana duk wani shirme da shiririta, she happens to have one paternal cousin who visited her after a long time, and she ended of hugging him da aurenta, Anwaar warned her sai gashi ta maimaita "Go back home, sannan ki ware lokaci na ba aure mahimmanci" jin yanda yayi maganan ah nitse tayi mamakin dan ta zaci fada zaiyi, baice komai ba ya koma EM dan ya kasa haqura, komawa wajen Aunty Sham tayi ta fada mata hukuncin Anwaar amma tace baza su tafi ba, gwada masa zasuyi sun damu da Ilhaam kaman yanda ya damu da ita

The next day

Yaa Sabeerah, Ashphert, and Aunty Aisha ke zaune dakin da Ilhaam take, tana kwance har ah lokacin saidai this time around bacci take, Anwaar na gefe dan dama shi ah asibiti ya kwana abunsa, no way zai koma gida yabar Ilhaam, yasan for sure laifin sane dan it's been a year Ilhaam batashan magani, kuma jiya ya fada mata labarin da batayi expecting ba "Wai mey ke damunta ne?" Aunty Aisha ta tambaya, kafin ya amsa Ashphert ta rigasa "Teemerh ne kesan kashe mun er uwa" girgiza kai Sabeerah tayi jin yanda Ash tayi maganan "Anwaar go and have some rest please" Sabeerah ta roqesa "I can't, I caused it all" kallon sa Ashphert tayi tanaso taji mey yama Ilhaam "Mey yafaru?" Aunty Aisha ta ari bakinta "Fatima is pregnant, and I told her" Ashphert exclaimed "Whattttt?" Har kusan fadi daga yanda take zaune tayi kaman ta hada miji da Teemerh "Ni ae nasan dole tayi nadama, bata zauna shan maganin hana haihuwa ba? Ya mata kyau" Yaa Sabeerah ta fada tana kallon Ilhaam dake kwance, sai yanzu karyan da sukayi ya dawo wa Anwaar, yanzu kuma za'a fara blaming Ilhaam da wannan, Ashphert that was in shocked kasa magana tayi "Enlight me" Aunty Aisha ta fada hakan yasa Sabeerah bata labari tas "Allah ya shiryi Ilhaam, ni zan koma" nan ta tashi tadau jakkanta dan abun ya bata mata rai, dan ita tanasan Ilhaam jinin su ya hadu "Muje toh" Sabeerah ma ta tashi nan aka bar Anwaar da maras kunyan qanwarsa, so take tace an cuce su, amma ganin daga ita sai shi Ilhaam in ma bacci take balle ta hanasa yi mata wani abun taja baki tayi shiru, sunkai 10mins suna zaune ba wanda ya yama wani magana cikin su dan shi haka kawae bayi magana mey tsayi da Ashphert, ah hankali Ilhaam ta bude ido "Ummi bata zo ba?" Tayi tambayan tana kallon su duka, kallon Anwaar Ashphert in ma tayi sannan back to Ilhaam "Kinsan bazata zo ba, jiya ta dawo daga damuwanta" kallonta kadai Anwaar yayi, Ashphert tana rashin ji, amma this time around tanada gaskiya, ya kamata Ummi tazo koh bazata dade ba, her and Ilhaam are suffering from the same illness after all. "Anwaar mu tafi" ta fada bayan ta zauna "Sure" ya amsa kawae bawae hankalin sa nakan abunda take fada ba, she's under Shareef's care toh dole ya jira Shareef yace ta tafi tukunna. Fita yayi ya samu Shareef ya discharging nasu, amma ya kafa wa Anwaar dokoki kaman wanda baisan aikin sa ba, kuma kaman ya manta Anwaar is Ilhaam's husband, nan ma yace ya bari ta kara hutawa sai zuwa anjima ta tafi, badai yanda ya iya yace toh dan he's not in good term with Shareef 2 days saboda matsalan Ilhaam in, Teemerh kuwa yanda ta gwada masa ta damu ma shi bai damu haka ba dan kiransa take duk bayan 30mins taji ya jikin Ilhaam. Da rabon Maa Sahla zata zo ta samesu dan tunda taji Ilhaam in ba lafiya tace zatazo, ita Ilhaam Ummi ta kesan gani amma duk itace ba batazo ba, har Yaa Abu a very busy man ya visiting nata tun cikin dare jiya dan Aameer bai bar komai ya wuce ba saida ya shaida wa kowa Ilhaam batada lafiya. "Ya jikin?" Maa Sahla ta fada bayan ta rike ta "Da sauki" ta amsa, riketa tayi tana mata sannu dan Anwaar bayi nan lokacin, Ashphert na gefe dasu tana kan shafawa Xeenerh labarin Ilhaam ba lafiya saidai ta manta batace mata Teemerh nada ciki ba, ganin Maa Sahla ta zauna Ilhaam tadau waya dan kiran Ummi, bai jima yana ringing ba kuwa ta dauka "Ummi bakizo ba" ta fada bayan Ummi tayi sallama "Ke Aya kin cika raki, yanzu wa rashin lafiyan kike haka? Toh Allah ya kara sauki dan bazan iya fitowa yau ba, Sahla tazo koh Aa?" Kallon Maa Sahla tayi da ita ma kallon nata ta keyi kafin tace Eh, nan fa Ummi ta fara wasu surutun ta kafin ta kashe "I missed Mami, the only person that cared about us" Ashphert ta fada tana biting finger "Ki kula da abunda kike fada, ita ta haifeki fa" Maa Sahla ta tuna mata "There's a difference between giving birth to someone and being a mother to somone, she gave birth to me amma ita bata taba damuwa da damuwan kowa cikin mu ba, yau tana Canada gobe tana India" kallonta Ilhaam tayi jin gaskia ta fadi, but Ummi leaving the country ae ba wani abu bane, she's a heart patient shiyasa take zuwan chan, amma ita bataso ta zama wanda zata fadawa Ashphert haka, itama Maa Sahla shiru tayi jin abunda Ashphert ta fada, bata isa mata fada ba tunda she has no right over them "Zakici abinci yanzu?" Ta chanja maganan ta hanyan tambayan Ilhaam, saurin girgiza kai tayi "Maa Sahla karki damu, zan kula da ita kafin na tafi" Ashphert tayi assuring nata hakan yasa tace toh, koh da aka salleme su Ashphert batayi tunanin raka Ilhaam gida ba, da Maa Sahla kadai Ilhaam ta koma gida kan Anwaar zai dawo anjima, he's having a busy day wajen Yaa Abu. Teemerh na zaune da both Sham da Habeey ah main living room su Ilhaam suka shiga, ganin ba tare da Anwaar take ba Aunty Sham batayi wani munapurcin tambayan ya jiki ba, haka su Teemerh, Maa Sahla ne ma ta gaidasu bayan sun zauna "Kije kiyi wanka kizo kici abinci" Maa Sahla ta umarce ta, kafin ta tashi Teemerh ta chapke "Ae bata ajiye baiwa mey mata abinci ba, tayi wanka tazo ta shiga kitchen" Habeey tace "Toh nima dai abunda nagani kenan, cook for yourself, kinsan dai ita Tee ciki gareta saboda haka ae she's not suppose to be stressing herself for you" uwar su Shamsiyya najin su kuma, kasa ma magana Ilhaam tayi dan tanayi zata fara kuka ita kuma she can't be weak gaban Teemerh, batace komai ba ta tashi amma ta rantse yau Teemerh sai tayi kuka kaman yanda tasa taji zafi aranta, ah karshe dai Maa Sahla ce ta mata abincin dan sun rantse she's not eating wanda sukayi. Tana cikin cin abincin Zoya tazo, basu mutunci sosai da Teemerh dama chan tun kafin aure, amma bayan Teemerh ta auri Anwaar Zoya tries amending things but Teemerh taqi, tace mata tabar kula Ilhaam indai tanasan suyi mutunci saboda she wants her people not Ilhaam's, ita kuma Zoya taki. Ita Zoya dama mutunci bai wani isheta ba yasa tana ganin su Teemerh taki musu magana ta wuce neman Ilhaam "Qutt, Allah Zoya zaki sha mamaki daga ke har ita mai daure mikin" kawae Teemerh ta tashi taja Habeey sukayi dining in dake sama, Maa Sahla na gefen Ilhaam sai Zoya da babyn ta dake hanun Ilhaam "Toh ki badata kici abincin" Maa Sahla tasa baki ganin tabar cin abincin tana karewa Sanaah kallo "Too cute" ta fada kafin ta bada ita wa Maa Sahla dan ita ta gama Zoya kuma ta fara cin abincin "Nifa ban gane kinzo kin wuceni nida er uwata ba sannu ba" Teemerh da shiganta wajen kenan koh sallama babu ta fara fada "Anqi ayi muku sallaman, wlh Teemerh zanyi maganin ki nikam" ta fada ba tareda koh kallonta tayi ba tacigaba da cin abincin ta "Toh kunji, then find your way out" Ilhaam tasa baki, harara suka bita dashi dan ita suka raina kuma dama da fushin ta "Kunga kuyi haquri duk ba abun tashin hankali anan, kuje ku" Maa Sahla tasa baki cikin nutsuwa "Ke kuma awa da zaki mun iyaka da gidan mijina?" Teemerh ta fada Habeey na goya mata baya "Anwaar dan gata, kowa tace mijinta, amma shi kadai yasan koh shi mijin waye" Zoya ta fada tana kallon Teemerh hakan yasa Habeey cewa "Waii, wlh karki yarda ta fada miki magana" Teemerh zata fara bala'i Ilhaam ta tsaidata "Girl, find your way out kafin nasa ah fitar mun dake, wawiya kawae wanda bata girmama manya" girgiza kai tayi taja Habeey suka fita da alqawarin dawowa in su Maa Sahla sun tafi dan suyi maganin Ilhaam "Lalle kina fama Ilhaam, wannan hauka har ina?" Zoya ta fadi tana tabe baki "Ku dunga haquri dan Allah, fadan bashi da amfani" Maa Sahla ta bata haquri, Ilhaam bata kulata ba ta tashi, kawae Anwaar ya nema wa kansa sauki ya maida Teemerh chan gidan nata daya daukota dan ita bata iyawa kuma, Sanaah dake bacci ta karba tayi daki da ita, Zoya kuwa bata wani jima ba ta tafi dan Shareef yace karta dade

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now