Babi na 22_ Rahma Nalele

372 46 1
                                    

☆“☆ª☆_☾'☆•'☆´-'☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** '☆´-'☆´-
Fasahar Rahma Muh'md Rufa'i Nalele... *Wattpad @rahamanalele*

*HASKE  WRITER'S ASSOCIATION 💡*
Home of expert and perfect writers

Kadda me karatu ya shagala, wannan labari kajeran labari ne, a page goma nake san gamasa, ko qasa da haka, ma'ana kwana goma😀.

” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 01☆.

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU 22*

*Kwana na d'aya* 1.

Kwalliya takeyi sosai irin ta yara yaran mata masu kyau da aji, kyakkyawa ce ta qarshe, fara ce tas me dogwan hanci had'e da yala yalan gashin kai, doguwa ce me matsakaicin jiki, daga dukkan alamu zatayi fara'a Sannan baza ta cika surutu ba....
Yafa gyalanta tayi da fashe jikinta da turare, kana ta Saka takalminta me tudu ta d'auki wata qaramar jakarta me d'auke da wayarta da kayan tarkacen kwalliya irin namu na mata masu wayo idan zasu unguwa...

Haka tafito daga gidan nata wanda kallo d'aya zakama gidan kasan akwai rufun asiri daidai gwargwado..

Duk da cewar dare ne dan a lokacin tara da rabi ne na daran, amma hakan bai hanata tafiya a nutse ba...

"Sannu barwar Allah, ina za'a kaiki..
Wani me adaidaita sahu ya tambayeta ganin da alama leman abin hawa take, dan ganin sai warge warge takeyi akan titin layin nasu..
Ad'an tsorace ta kallesa dan bata san dashi a wajen ba, Ashe ta wuccesa dake hankalinta yana can inda take san zuwa...
"BSW nake san zuwa, "ok, shiga na kai ki.
Haka ta shiga yaja adaidaitan nasa, aiko bai direta a ko ina d'in ba sai a inda ta umarcesa..
Babban hotel ne, wanda ya amsa sunan sa, yana kyau sosai wanda baka isa kamai kallo d'aya ka wucce ba, manyan mutanan mu ne masu hannu da shud'i suka fiya zuwa wajen..
Dubu d'aya ta zaro a jakar tata ta miqa masa.. Nan ya karb'a da niyar nema mata canji a d'an cikin wannan ma'a danar tasu ta adaidaitan.. 

"No fah, kabarshi na bar maka canjin.. Aiko da murmushi akan fuskarsa ya kalleta da zuba mata godiya kana yaja adaidaitan nasa..

Sam bata motsa daga inda ya barta ba, saima kallan agogwan hannunta da tayi, tad'an ja tsaki da fara danna wayarta..
Kan ta cinma burinta akan wayar saiko ga wata zazzafar mota ta faka a gabanta, wata mata ce y'ar gaye haka kamarta, itama fara ce Sol tafito daga motar tana murmushi da cewa, Kiyi hakuri  MATAR KAMAL, wallahi na tsaya lallab'a Salim ne yayi bacci..
Ta ce "Ya zanyi dake  Safina, muyi ciki kawai dan sanyi ya fara takura min, takaicina d'aya nayi mantuwar suwaita. "Ba damuwa ai, tunda Oga yana nan saiya baki tashi, Safina ta bata amsa da fad'in, ta ce "Kumafa haka ne..
Nan suka shige cikin motar  da shiga cikin Hotel d'in.
Can ciki Safina tayi parking motar, inda ba me takura mata da batun tazo ta gyara parking,, kana suka fitto da nufar wajen ma'aikatan wajen..
Dake sun san su mukullai kawai suka basu, da tabbatar musu matanansu suna d'akunan, duk da sun gaya muku hakan bai Saka su sun maida musu da mukullan da suka basu ba, haka suka haura saman inda d'akunan suke, waƴanda suke kallan juna, amma kafin su rabu sanda suka sumbaci junansu alamar sai da safe..

Yanda JAMILAH wato wacce Safina ta kira da MATAR KAMAL taga ogan nata kwance a kan gado haka itama Safina ayanzun taga nata kwance akan gadon..
Alamar jiransu kawai suke..

Safina matar Aure ce, dan tana da yaranta biyu,  mijinta Soja ne, Sam baya tafiya da ita wajen aikinsu, gashi ita ta kasance mace ce me matuƙar sha'awa, shi kuma yana iban wata biyu ko uku acan wajen aikin nasu kafin ya dawo, hakan yasa data had'u da wata qawarta sai ta bata shawarar karta tsaya b'ata quruciyarta, kawai ta dinga lafewa da wasu mazen, tana samun biyan muqatarta. Da farko Safina taqi yarda amma daga baya da shed'an ya buga mata ganga saita yarda,  yawancin mutananmu masu aji da dajin nera Safina ta san su, dan wannan dai qawar tata ita ce ta had'ata dasu, dama tana da y'ar aiki agidanta, wata Baba tsohuwa, tsohuwar banza ce, tunda tasan me Safinan take aikatawa amma bata tab'a tsawatar mata ba, tunda ta fuskanci ta qara mata albashi me yawa, itace dai take kula da yaran Safinan cikin dare tunda kwana takeyi agidan, shiyasa Safinan bata sharin kwana ako ina dan tasan Yaran nata na samun kulawa musamman da safe yayin zuwa skull..

Safina Y'ar gaye ce ta ƙarshe, tana da kyau daidai nata, mace ce wacce abinta bai rufe mata ido ba, tana da kirki sosai, dan daga danginta harna mijinta ƙaunarta suke, danta kasance me miqawa, ga ibada akan lokaci. Kawai dai ita matsalarta wannan harka dai ta takeyi, kuma tana jin tad'in harkar, bara mugu shin wannan jin daɗin nata zai d'aure kuwa...
Wannan shine labarin safina

Haka ayanzu taje ta rungume Alhajin nata, tana basa hakuri wai sanda ta tsaya Salim yayi bacci (wato qaramin yaranta) wannan ne yasata dad'ewa.
Shidai qara matseta yayi a jikinsa, dan Yasan ko tafi haka dad'ewa bazai damu ba, tunda yana samun yanda yake so..


JAMILAH ko yar da jakarta da wayarta gefe tayi, ogan nata ya tashi da farin ciki ya rungumeta yana me cewa, "sannu da zuwa MATAR KAMAL, meya dad'ar min dake ne haka..
Tace "kwalliya na tsaya yi maka. Ta kai qarshen zancen damar fari da ido wanda nan take yasashi yadasu akan wannan gado yana bata amsa da cewa, "Gashi ko kinyi kyau sosai, dole na biya wannan wankan..
Zata mai magana wayarta tahau ruri, sanda ta yatsina fuska dan gane me kiran, kana ta d'auka da cewa.. "Luvly, lefin me nayi yau kwata kwata baka kirani ba, bayan kasan ina a halin missing d'in komai da yake naka..
Acan b'an garan me kiran yace "Baby kiyi hakuri yau aiki ne yamin yawa, Sam kobi takan wayar tawa banbi ba, harna fara tunanin qila ko kinta kirana baki jini ba, Saidai kuma dana duba Miss call d'in dana samu na mutane babu naki a ciki..
"Tace haka ne Luvly, ban kiraka ba, yau dai rana d'aya nace bara na barka ka huta.. Danna fahimci kamar ina takura maka wajen yawan kiran naka da nakeyi.
Ya ce "Ba haka bane Baby, aiki ne yake mana yawa, kar kiyi fushi akan hakan, ta ce "Hmmm, zan kwanta Luvly bacci ya kusanto ni, yace "Dama muna tare da juna a daidai wannan lokacin, da kinyi min maganin gajiyar dana dawo da ita,.
Tayi murmushi da cewa, "karka damu zanyi maka maganinta ranar daka dawo, yace "Toh kidai kulamin da kanki, tace "yanda ka barni haka zaka dawo.ka sameni.
Yace "Toh Allah yasa, " Ameen.. tace 
Daga hakan sukayi sallama..

Ogan nata ya kalleta rai b'ace yace "Yaushe zai dawo, tatab'e baki tace "jibi mana, me yasa kake mantawa ne, yace "Wallahi bani san dawowarsa, dan yana takura min..
Murmushi tayi da maida hankalinta gabaki d'aya kansa, ta Saka dukkan hannuwanta a kafaɗarsa suna masu kallan juna irin na waƴanda suka dad'e da sanin sirrin juna tace dashi, "nima yana takura min, ba yanda zanyi ne kaga ina maka shuru, amma yaci ace hakan ya dena damun ka, tunda ka fisa more duk wata albarka da Allah yayi min..
Jin hakan yasa shi sakin murmushi, da neman rabata da kayanta yana cewa, "Bakiyi qarya ba MATAR KAMAL...

Nan ko suka fad'a aikata aiki mummuna,  wanda Allah yay hani dashi wanda zai zame musu dana sani anan gidan duniya dama can gidan lahira.

Sun b'atama juna tunani awannan dare kamar baza subar junan nasu ba, amma haka dai sukayi hakuri saboda bacci baya sallama..

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now