Shafi na biyu

2K 162 4
                                    

  
*KUNDIN HASKE*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*.

*K'UNGIYAR:-*
   HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
*Zaynab bawa (zeeyybawa)*
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA BIYU*

بسم الله الرحمن الرحيم

   Gidansu malam yahuza

Duk yanda malam yahuza yaso yiwa mahaifiyarsa magana abun yaci tura domin taqi sauraransa,
 
Tagumi yayi jiya keyi kamar yayi kuka, baisan laifinda humaira tayiwa innarsaba kwata-kwata bata sonta,
  Shidai yasan duk wani qualitie na y'a mace humaira tanadashi uwa uba tarbiyada hankali, amma mahaifiyarsa taqi amincewa da'ita,

  Kamar mai shirin yin kuka yace" inna dan Allah kifad'amun laifinda Humaira tayi miki idan kika fad'a nida kaina zand'auki mataki akan abun,

Hararata wurga masa sannna tace' bbu wani laipy data yimun nidai kawai banaso ka auri y'ar macene,
Tun yaushe mahaifinta yarasu wajan mahaifiyarta tatashi taqi yin aure balle tabarwa yarinyarta tarbiya,

Haba inna wallhy humaira tanada tarbiya kokad'an itaba irin yarannan bane, tarbiyarta daban take,

A'a yahuza wace tarbiya za'a samu wajan yarinyada tatashi daga itasai mahaifiyarta?"

Wace tarbiya za'a samu wajan y'ar mace?"

Ita uwar keda laipy Kamata yayi tayi aure sannan takulada y'arta tabata tarbiyya, kokuma tad'auketa takaita dangin mahaifinta akwai yayyu dakuma qannen mahaifinta, saita bada ita suyi mata tarbiyanda ya dace,

  Haba innna wallhy humaira tanada tarbiya kokad'an batada hali irinnta wasu daga cikin y'an matan yanzu,
Innna idanke kina uwa mace zaki kyamaci tarbiyarda uwa mace zata bawa y'arta wakike tunanin zasu nuna amincewarsu awannan lamarin,

Inna danfa yarinya tagirma gaban maifiyarta bahakan yana nufin batada tarbiyaba, bakowace uwa bace zata bar  d'iyarta ta ta6ar6are,
Inna dan Allah kitaimaka wallhy humaira tanada tarbiya,
Inna kafin lokacinma nayarda kisanya ayi miki bincike akan halayenta,

Ban jiba  ban kuma aminceba yahuza kacanja matar aure kawai idan kanason farin cikina karabu da wannan yarinyar,

Idan kanta uwarta aure yakamata tayi, tabar zama cikin gida ita kad'ai, tanemi mutumci idon jama'a domin aynzu ko mutuwa tayi darajarta bad'aya da wacce tayi aureba,

Kanemi wata amma ba wannan yarinyarba,

Idankuma ba hakaba wallhy yahuza akan wannan yarinya zan'iya d'aga maka nono,

  Cikin tashin hankali yace" aa inna kiyi hakuri abun baikaiga hakaba in sha Allahu zanrabuda ita,

Dadai yafi maka inna ta bashi amsa,

Toh inna yanzu yaya Za'ayida baba?" bayan nafad'a masa zancen kuma yasanya nasanarda ita cewa zasuje wajan neman auran,
Bakada matsala da wannan nidai damuwata dama shine ka janye zancen auren tunda ka yarda ka janye komai yazo gidan sauki."

Allah yamaka albarka, zaka samu wanda tafita mata nawa awannan zamanin?" gasunan sai wanda kaza6a,

Uhmm inna kenan nasam akwai mata dayawa wannnan zamani amma kuma abunda mutanen basu ganeba shine nagari acikinsu sunyi kad'an,

Yahuza kenan bazaka ta6a gane mai nake nufiba, amma kuma nan gaba zaka fahimta, domin ance ta yaro kyauta keyi bata ta6a qarko, amma nan gaba zaka gane, maika kanka zaka fahimci abunda naguda yasanyani kin wannan lamarin,

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now