Shafi na takwas

1.3K 108 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*
  *shafi na takwas*

Kukan sadiya bakaramin tadawa Abubakar hankali yayi ba domin a yanzun babu abinda ya tsana a rayuwarsa sama da abinda zai taba Masa sadiya domin gani yakeyi dik duniya yanzun tafi kowa kaunarsa a yadda take nuna Masa ta canja halayentq da yasani a baya da kyar Abubakar ya lallashi sadiya ya samu tayi shiru sanan suka cigaba da magana,
Abubakar ya kalli sadiya cikin tsananin damuwa yace "yanzun sadiya saboda nakawo shawarar mutashi a gidan Nan yasa kike kuka haka tamkar zaa zare Miki Rai bayan kece nakeso inyiwa gata?,kina gani fa yau abinda ya faru wallahi yadda na zuciya da mama ta kyaleni saina nakassa yarinyar can shukra Akan me zata rainamun mata?Ina sonki na auroki Kuma kema ai kinada iyaye ba daga sama Kika fadoba sanan bazan so a wulakantakiba tunda Nina kawoki"

Wani sanyin dadine ya lullubeta ta Dade Tana jiran wannan ranan da zatazo Abubakar ya juyawa kowa baya Sai ita saidai bataso subar gidan Bata Dan danawa mamansa da kannensa takaici ba hakan shikadai ne zatayi ta Rama abubuwan da sukai mata a baya....

  Kwantar da Kai tayi a jikinsa sanan ta dago idanuwanta ta saukesu a kan fuskarsa Shima kallonta yakeyi da wani irin kallo Mai tattare da shaukin kaunar junansu sadiya ta CE "gaskiya Abubakar bazan goyi bayanka da mubar gidan Nan ba domin ai uwa uwa ce komenene bazanso ka gujesu saboda niba sanan mama Nima mahaifiyata CE hakuri zamuyi mu cigaba da Zama da ita nayi maka alkawarin yi mata biyayya a dik ko wani Hali"

  Rungumeta yayi sosai ya matseta a jikinsa Yana shafa bayanta Yana Mai Jin dadin kalamanta zuwa yanzun ya Gama yarda da sadiya ta canja halayenta na kishi da takeyi a baya da mahaifiyarsa,

  Kiss ya manna mata a goshi sanan yakai hannu kasan mararta Tana shafawa Yana murmushi yayinda ta boye kanta cikin kirjinsa Tana Mai Jin kunyarsa,

  "Nagode halimatu saadiyya Allah yayi Miki albarka kinji nagode matata"

  Murmushi tayi sanan tace "Ina alfahari dakai mijina"

"Wancan kayan dana kawo jaka biyu tamu daya CE tasu mama daya saiki dauki daya ki Mika musu daya bari inje masallaci"

  Mikewa yayi ya shiga toilet ya dauro  alawala sanan ya fita zuwa masallaci kamar jira takeyi ya fita ta Mike tayi tsalle ta yi juyi ta rarumo wayarta da sauri tayi dialing number mahaifiyarta bugu daya ta dauka

  "Assalamualaikum"

"Waalaikissalam mama Ina yini?"

  "Lafiya kalau sadiya ya gida ya Mai gidan naki?da surukarki?"

  "Dik suna lafiya,dama Zan gaishekine infada Miki gobe ki Aiko a karbar Miki sako kinji naso zuwa Amma bana Jin dadin jikina"

  "To Allah ya Kara lafiya,ki gaida surukar taki"

   "Zasuji Tana daki a gaidasu yaayah"

Sukai sallama ta kashe wayar mikewa tayi ta bubbude kayan da Abubakar ya kawo ko wace jakka shake take da kayan azumi damginsu kayan tea da sauransu harda gero, shiru tayi Tana tunanin yadda zata kasafta kayan wani tunanine ya Fado mata ta kwashe kayan tea da su kwai da komi ta je ta bude drawer da Bata amfani dashi tasa ta boye ta kinkimi gero da sugar  ta zura hijabinta tayi dakin mama Tana yatsinar fuska.

   Babu ko sallama tadan daga labulen Tana shinshine shinshine kamar taji warin tusa ta dire musu jakar kayan a ciki ciki tace "ga kayan azuminki inji danki"

  Mama da faraarta tace "Masha Allah,nagode Allah yayi mishi albarka ya Kara arziki"

  "Ameeen" sadiya tace a takaice ta fice a dakin Tana shakar kamshi....

   Allah Allah shukra take sadiya ta fita ta bude taga meye a ciki Koda ta janyo jakar daidai Nan Abubakar ya dawo masallaci ya Dan daga labulen dakin yace "sannun ku da gida"

  Mama ta gyara Zama da faraarta tace "Ashe kadawo"

  Fuska a daure ya amsa a takaice "ehh"

"Ga sako sadiya ta kawo mungode Allah ya saka da alheri ya Kara arziki da budi"

  "Ameen Saida safe"ya juya be jira me zatace ba.....

   Girgiza Kai kawai mama tayi ta furta a fili "Allah ya shiryar da Kai yasa ka gane gaskiya Abubakar Allah ya kareka daga sharrin mace"

   "Ameeen"biebie tace,ita kuwa shukra tabe baki kawai tayi domin yanzun idan akwai Wanda takejin haushi duniya to yayan ta ne.

********

  Washe gari mahaifiyar sadiya ta samu Yar makociyarsu matashiyar budurwa ta aikota gidansu sadiya ,

  Aiko sadiya ta hada Sha Tara na arziki na kayan azumi ta loda a jaka harda kudi tabawa yarinyar ta rakota Saida sukazo daidai kofar dakin mama sadiya ta daga murya tace "ki gaidamun mama kice ga kayan azumi Nan daga yarta data haifa tayi azumi lafiya wannan kudi Kuma surukinta ya bada tayi cefane"

  Ta juyo Tana karkade karkade,kasantuwar yau ne farkom azumi yamma nayi bayan laasar sadiya ta shiga kitchen ta hau girke girke kamshi kawai ke tashi a cikin gidan wajen karfe shida ta kammala komi Yar pepesoup na kayan ciki tayi tasa a kuloli a gabansu mama tayi daki dasu,

  Tanayi Tana fadan maganganu da shukra ta zaburo zatayi magana mahaifiyarsu ke hanata da kalamai na nasiha Akan tayi hakuri dik abinda sadiya tayi komi nada iyaka.

   Ana kiraye kirayen magriba Abubakar ya shigo gidan a gaggauce ya daura alwala yayi masallaci,bayan an idar da sallah ya dawo ko kallon dakinsu mama beyiba balle yayi mata barka da Shan ruwa,

  Sadiya ta gabatar Masa da abincin da ta giggirka Tana ci Tana ya tsuna fuska Wai batason kamshin abincin haka dai yake lallashi ta tanaci Tana Bata fuska ,bayan sun kammala ne yace "Wai nikam sadiya kin zubawa su mama nasu romon naman?"

  Bataji dadin tambayarta da yayi ba wato har yanzun dai suna nan a ransa kenan,cije lips dinta tayi ta daure ta ce"haba Abubakar ko bayan babu ranka bazan iyacin Abu in hanasu mama ba da take a matsayin mahaifiyar mijina Kuma mahaifiyata ballantana da ranka ,Ina gamawa su nafara zubawa sanan nasanya Mana namu"

  Ajiyar zuciya yayi yace "naji Dadi halimatu Allah yayi Miki albarka"

Murmushi kawai tayi ta lafe a jikinsa ya Kara rungumeta Yana Mai Jin sonta yana ratsa sassan jikinsa.....

*A gurguje*

A kwana a tashi haka sadiya keyin wulakanci kala kala Tana zubawa Abubakar makirci game da mahaifiyarsa yayinda mama ita Kuma batayi kasa a gwiwaba cikin zubawa Dan nata addua a cikin wata Mai tsarki kullum adduarta baya wuce Allah ya karkato da hankalinshi ya gane gaskiya ya shiryar mata dashi ya karesa daga sharrin mace tasan komi Daren dadewa Abubakar gaskiya zatayi halinta....

*******
Ashirin ga watan azumi Abubakar ya kawo kayan sallah yadda yadda yadda ya Saba siyawa mama leshi da atamfa ya dunka mata hijabi haka yayi wannan sallahr kannensa ma Kaya yake Basu kala uku uku da kudin dinki sadiya Tasha mamakin yo siyayar da Abubakar yayi dik a tunaninta baxai musu kayan sallah ba bakin ciki tamkar ya kasheta kasantuwar da kansa ya kaiwa mama kayan har daki taso ace ita yabawa da wallahi bazata badasuba tunda abin nasa haka ne haka taita cizon Dan yatsa ganin leshin da ya siyawa mama yafi nata tsada hakanan ta kudurawa kanta anzo final zaayita ta Kare ita kadai tasan abinda zata kulla musu gara ta rabasu ta huta tunda taga kamar ya Fara dawowa hayyacinsa

  Yana fita ta janyo waya ta Kira bintu a waya ta sanar mata da tana nemanta da gaggawa akan wata matsala dake Shirin taso mata don taga kamar saka takeyi Yana warwarewa......





*SLIMZY😍*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now