Babi na 16-Mamuh Gee

2.4K 222 26
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        _*Al’kaluman marubata*_

  _*KUNGIYAR:-*_
_*HASKE WRITERS ASSOCIATION*_
_(home of expert and perfect writers)_

_TARE DA AL KALAMIN_

*_MAMUH GEE_*

_BABI NA GOMA SHA SHIDDA_

*YIWA KAI*

*1*

Bismillahhi rahmanir Raheem.

Sauri sauri take aikin hada masa tea din dake gabansa tana gama hadawa ta dauki plate da sauri ta zuba masa soyayyen dankalin turawa da soyayyan kwai fari tas babu ko albasa ta tura masa gabansa tareda dauko ruwa ta ajiye masa.

Dagowa tayi ta kellesa taga ita yaqurawa ido Yana binta da kallon mamaki da takaicin halinda ta jefa kanta Wanda yayi iyawarsa takasa canzawa,

Plate din gabansa yakalla yaga yanda qwan yake fari tas dashi alamar tsabar saurin datake tagama aikin taje tayi kallo ko karatu yasa ko 'yar albasa ta gagara yankawa aciki bare 'yar jitta da tafarnuwa ko tattasai dazai qarawa qwai galmi,

Dankalin yakalla yagansa shima tas tashi alamar bai gama soyuwa yanda yakamataba ya girgiza Kai bayan ya sauke numfashi sbd Sam abin yafi qarfin duk inda yake tunani.

Cup din tea din data gama hada masa ya dauka yakai baki tareda Bismillah ya kurba ahankali sbd zafi Amma ga mamakinsa ruwan Sam basuda zafi sai dumi.

Kallonta yayi da sauri sangaye da cup din ahannunsa
Tayi saurin washe fuska tana murmushin qarfin hali sbd tasan ta kwafsa sai gskia batason tasake missing episode din jiya na KULFI KUMAR BAJEWALA a starlife dakuma episode din FIRE AND ICE a zeeworld gakuma wasu episodes din datai missing kamarsu, GAME OF THRONES,MADE FOR EACH OTHER, GEET, THE ORIGINALS, THE 100 gakuma WILDFLOWER da MY HEART BEAT FOR LOLA,,

Shiyasa take sauri Dan tama gama matsuwa daya gama ya fice tasamu tayi abinta tun kafin amal ta tashi daga bacci ta hanata kallon cikin nutsuwa da shegen rigimarta na kuka.

Ganin tana kame kame ga matsuwar ya fice a tattare da ita sai kawai ya aje cup din ya miqe tsaye tareda takowa yadawo tsakiyar palon ya dauki wayoyinsa da jakar laptop dinsa ya juyo yakalleta tasaki murmushi tareda gyara masa necktie dinsa tana kallon cikin idonsa da sigar Jan hankali tace,

Tou babe saika dawo Allah ya tsaremin Kai.

Ahankali ya furta Amin saina dawo take care of yourself and my angel,
And idan ta tashi call me.

Daga masa Kai tayi tareda rakasa har jikin motarsa inda Suka tararda shamsu yadawo daga morning jogging ya qarasa gabansu Yana share gumin wuyansa yace,

Yaya kamal Ina kwana?

Kallonsa yayi yaga yanda wandon jikinsa yakamasa gashi jikinsa duk rabi a bayyane sai yaji baiji dadiba sbd Sam baya shaawar irin wannan rayuwar.
Numfashi yasauke ya kallesa yace"
Lafiya klau.

Kallonta yayi ahankali ya furta natafi ki koma ciki kawai.

Tou tace tareda juyawa sbd dama a matse take dason komawa sbd qarfe Tara takusa koda suka fito tasan yanzuma Tara din ta buga qilama harda mintuna.

Kallon shamsu yayi yace"

Natafi saina dawo.

Ya fada motarsa yaja ya fice zuwa gurin aikinsa.

Shima shamsun juyawa yayi ya shige sashensa dayake anan gidan yayan nasa yake zama kasancewarsu uwa daya uba daya.

Da himmarta ta isa palon ta kunna socket tadauko breakfast din dayaqi ci ta zauna tafara kallonta hankali kwance tanacin abincinta.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now