Shafi na uku

1.4K 107 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TASKAR: Khadija Ahmad*😊

*RAYUWAR NI 'YA SU*
   
    Babi na goma sha d'aya

3)
Wayata dake hannun khady ta shiga vibrating naso sharewa sedai jin tace mami ke kira yasa nayi saurin 'kagawa a kunne, tunkan nakai ga yin sallama naji muryarta cikin kuka
"Mamana wai dagaske Aliyu ya tafi ya barmu?" Lumshe ido nayi kan naja hanci cikin dasashshiyar murya nace "hakane mami"
Salati taja kan naji wayar d'if ta d'auke, kallon khady nayi kan na fad'a' jikinta ta rungumeni nashiga kuka tun 'karfi wanda bazan iya cewa ga lokacin dana d'auka inayi ba  sedai tashi nayi na jini jikin wata wacce  Khadija ba a hankali na bud'e idona inda na sauke su cikin na wata wacce badan ba mudubi kusa dani ba da se nace nice dan carbon copy d'ina ce Sak sede wannan manyance daya fara zuwar mata, kallon nake Ina dad'a zurfafa kaina cikin duniyar tunanin wacece naji ta dafa goshina
  "Mamana kin tashi"
  "Mami?"
Ta girgiza kai "na'am" dad'a 'kan'kameta nayi muka fashe da kuka   mutane se bamu baki ake dakyar mukayi shiru ranar haka muka wuni cur tare da juna ko nan da can na'ki matsawa wlh ranar baccina 'kalilan ne Ina ta makaki wai yau nice tare da mamana tamkar yanda nake ganin wasu haka zalika tamkar yanda nake mafarki sede kash cikin mafarkina tare muke da Aliyu Amma yanzu a zahirance mu biyu ne kawai. Haka muka kasance har na tsawon kwana uku inda daganan su mami sukayi sallama suka tafi wanda da kukana harda majina muka rabu bayan tayi min alkawarin zatake kirana akai akai.

Tundaga wannan ranar na zama isolated ji nake tamkar nima mutuwar zanyi dakyar nayi regaining consciousness d'ina.

Bayan kwana arba'in da bakwai Ina zaune gaban mirror ina taje kai naji 'karar wayata sunan Aminu na gani da kamar Karna d'auk se kuwa garin ture wayar na danna bansani ba se kuwa jinsa nayi yana cewa
  "Gimbiyata kina gida ne?"
  "Eh,"
  " To ganinan" yace tare dayin hanging wayar.
  
"Yanzu raheena  danuwanki ya rasu amma baki fad'amin ba har anyi arba'in"
Saddam kai nayi nashiga yin wasa da yatsu na dan ha'ki'kanin gaskiya nasan ban kyauta ba"
Murmusawa yayi " bakomai Allah yayi masa rahma ubangiji yasa bakin wahalar kenan"
  "Ameen"
Shiru ya biyo baya, zuwa can yace "Zan iya yiwa Su Inna gaisuwa"
Wata kunyar ce ta kamani jin ya rigani fad'a', yasa hannu ya shafo fuskarshi dacewa "sorry na takura ki ko"
"Da sauri nace um um Bismillah na take masa baya har ciki bayan yafito ya Kuma yi min gaisuwa sannan ya tafi.

Bayan shekara biyu rayuwa tacigaba yau da dad'i gobe akasin haka yanzu kusan kullum se na kaiwa mami ziyara gidan ta, ta 'bangaren karatuna kuwa Alhamdulillah dan mun shiga final year har mun fara project.

Zuwa wannan lokaci tuni aunty farida tayi aure yanzu saura ni da haule se 'yan uwan mu maza.

Yau muka tashi inna zata tafi cairo dan Duba lafiyarta kasancewar tana da  cutar breast cancer before anyi mata aiki ta samu lafiya kusan shekaru goma da suka wuce se kwanakin nan kuma da take jin wani abu cikin nonon shiyasa ta shirya komawa haka ta tafi ta barmu da kewa dan ma kaka rabi na nan . Kwanan ta 39 ta dawo aikuwa ranar na dawo daga makaranta kenan na tarar da ita sosai na tsinci kaina da farinciki bayan ta huta ta rarraba mana tsarabobin mu kwana biyu da dawowarta fad'ime ta d'auka ma'ana ta haihu zokuga murna aikuwa Inna tace na shirya naje na tayata zama haka kuwa akayi ranar suna yaro yaci sunan Umar Faruk inda Akasha shagalin a gidanmu bayan suna da kwana  ashirin Inna ta fara rashin lafiya lokacin muna tsaka da exam ranar wata litinin da daddare mijin fad'ime ya kawomu muka duba ta se kusan d'ayan dare muka tafi haka na kwana ranar ina karatu saboda test din goma da nake da ita bansamu na kwanta ba se kusan takwas bacci yana fara d'aukana naji karar wayata Ina d'agawa naji muryar fadila na fad'in
"Rahinatu maza ku taho kuzo Inna jiki yayi tsamari wuyanta har ya karye"
Salati naja wanda ya tashi fad'ime dake bacci gefena Dede lokacin da akayi knocking 'kofar d'akin fad'ime ta bud'e mijinta ne tsaye ya kama hannunta tare da kallona yace rahinatu shirya Faruk kema ki kintsa zamu fita gyad'a kai nayi da sauri na shiga shirya Shi nima na zira abaya bayan na tashi tsohuwar dake wa fad'ime wanka ta kintsa suka sauko muka fice.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now