Shafi na 4&5

5K 282 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al K'ALUMAN Marubatan HASKE_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
           *NANA DISO*

*DARAJAR MUTUNCIN MU.....*
       _('yan zamani)_

     
BABI NA DAYA
    Shafi Na Hudu da Na biyar...

Walida walida wai wannan kukan na menene? Ace kusan sati biyu baki da aiki sai kuka kinason kashe kanki ne?

    " Dole nayi kuka ummata dole nayi najawa kaina abun dariya na jawa kaina fushin Allah,yanzu wanda nake tunanin zai aure ne ya gudu innalillahi yakukeso nayi kullum neman gafarar Allah nakeyi...

   " ki daina damun kanki acikin kaddarar da Allah yaso wannan rayuwar taki ki dauketa a matsayin jarabawa kuma kiyi fatan kinci tunda har kika tuba kika gane hanyar gaskiya...

    " hajjaju tabbas nasan da haka Amma fa abun takaicin na kyamace abunda Allah kadai ke durawa bayinsa na kyamace talauci nayi babban kuskure domin nafadi maganganu akansa nakuma dauki iyayena bakomai ba yaa Allah ka yafemin..

    " yanzu dai ba wannan ba kitashi kije ki dora abinci kikuma cigaba da neman yafeyar Allah...

Wasu yanmata ne suka saka dariya acikin layin ku in baku labari mana ai walida ta daina fita fa ta shiryu taje taji bariki ba abar so bace ba..

    " To daman ai ita takai kanta ba dole tashiga cikin tashin hankali ba yanzu fa sama da wata 4 babu inda take zuwa...

    " Daman mu muke batawa iyayen mu suna ai garin kwadayi..

   " aa wallahi iyayen ma suna batawa yaransu suna kiga sun kafe yarinya bazata aure talaka ba gasu fa acikin talaucin Amma su kai yaransu inda baa ganin mutuncin su kuma daga karshe asamu matsala ai shi arzuki rabone duk yadda kakai da binsa naka kawai zakaci..

   " tabbas kawata Allah ya shiryemu...

 
  Matar muazzam ce tafito daga kitchen dauke da wasu plate masu abinci aciki tace gaskiya maganar auren nan tana damuna yaya zaayi kakawo mana wata tazo ta hanamu kwanciysr hankali yakamata kayi tunani akai ni menene bana yimaka .....

  " Tabbas babu abunda bakiyimin kuma shi aure duk dadin danamiji yakeji yanaso yakara wani ai..

   " Ai ni shawara nabaka bakomai ba..

   " kuma fa da kamshin gaskiya ashawarar ki...

   Tunda yaje office yake juya kujera anan ya dau wayarsa ya rubuta..

  " Walida gaskiya maganar aure tsakanin mu bazata yihu ba domin banason rabuwar kan iyalina Allah yabaki wani ina miki fatan mafificin alheri.."

  Muazzam shi kansa daya rubuta baiji dadi ba haka dai yayi shiru yana juya wayar anya zan iya rayuwa babu walida gaskiya i cant..

Walida dake zaune tana gyara wake fatima tana yanka salad taji wayarta tayi kara dubawar da zatayi taga text din kafin takarasa karantawa hawaye ya cigaka fuskar ta acikin sauti kadan kadan tafara kiran innalillahi wainna illahirrajiun adduoi babu wanda bata jaba...

   " yaya walida wannan kukanfa? " bakomai fati, lokaci guda taji jire yana ibarta daki ta shiga ta rufe koma kuka kawai takeyi tana inasonka muazzam ko kaini karshen talauci sai dana saba dakai kai ka koyamin sonka yanzu kenan bazan aure ba ya yaudareni yacuceni anan bacci ya kwashe...

  " tun lokacin da yayi mata text yarasa tunanin sa hankalinsa yatashi bai taba jin yana son walida haka ba washegari ya dinga neman numberta akashe textbya turamata amma shiru babu reply..

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now