Shafi na shida

1.6K 143 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

*K'UNGIYAR:-*
   *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
Zaynab bawa (zeeyybawa)
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA  SHIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

  Murmushi mai kyau mlm yahya yayi irinnasu na manya wanda sukasan mesukeyi shiru yayu baice komaiba yazuba mata idanuwa kawai tana magana,

Sanda yabari tagama duk wani abunda zatayi sannan yadubeta cikin nutsuwa yace" banda abunkiba aisha menene aibu danna auri macenda mijinta yarasu?"

Menene aibun danna auri macenda akaki auren d'iyarta domin batada aure?"

Menene aibuna wajan gyaran 6arna?"

Menene aibuna dan inason toshe baraka?"
Menene aibu danna nemi zamawa yarinyarda mahaifinta yarasu uba?"
Menene aibu akan neman zamawa marainiyar yarinya jigo?"

Aisha idan mutum zaiga 6arna baiyi qoqarin gyarata ya gujeta inaso kisani wannan ba koyarwar annabinmu bane,
Annabi muhammad tsairada amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa, idan kaga 6arna kayi qoqarin gyarata tukunna da hannunka da kalamanka iya gwargwadon iyawarka idan wannan 6arna taki gyarsuwa shine yace kai ka gujeta har zuciyarka,

Aisha idan za' samu malamai cikin al'umma sannan kuma suga wata baraka batareda sun nemi toshetaba mai hakan yake nufi kenan?"

Idan za'aki auren d'iya mace domin batada mahaifi mahaifinta yarasu waye sukeda laipy awannan al'umma?"
Malamai Aisha yabata amsa cikin nutsuwa,

Har indai maza zasu rage yawan matanda suke zaune da y'ay'ansu da wannan abu bai kai hakaba,

Da babu wata wacce zata fito kokuma wanda zai fito yace shi y'arsa bazata auri y'ar mace kokuma d'an maceba,

Inaso kisani dukanmu nan da kika ganmu y'ay'an matane, domin matane suka haifemu, meyasa mutane zasu ringa amfani da wannan kalma suna 6ata sunan iyayenmu mata?"
Mai yasa za'ana qauntatawa mahaifanku mata da wannan kalma?" maiyasa wannan kalma tazama abunki cikin al'umma?"
Mai yasa za'ana fad'in y'ar mace ko d'an mace bayan kowama y'ar macence kuma d'an macenne domin sune suka kawomu duniya,

Anan amfani da kalmar y'ay'an mace ne wajan macenda mahaifin yaranta yarasu sannan kuma tarsaya tsayin daka wajan ganin rayuwar yaranta sun inganta,

Kisani cewa mafi yawanci matanda ake kiransu da haka mazajensu rasuwa sukayi,
Mutuwafa tanakan kowa, watakil nima da kike gani na mutu nabarki da yaran,

Shikenan kuma sai'ace baza'a auri d'iyarkiba domin y'ay'an matane?"
Habawa Aisha,

Niyanzu zan auri khadija domin Allah,

Zan auretane domin inaso y'ay'anta sudawo y'ay'an mace dana miji,

Wasu matan mafi yawancinsu suna qinyin aurene saboda y'ay'ansu,

Ahalin ynzu bakowani namiju bane zau aureki sannan kuma yariqe miki yaranki marayuba, dalilin wannan yasa mata dayawa suke gujewa yin aure bayan mutuwar mazajensu  saboda tunanin halinda yaranzu zasu shiga,

Sun kwammaci su zauna suyi fad'i tashi wajan ganin sun nemawa yaransu rayuwa mai yauki,

Ayanzu ba'a taimakawa marayu taimakon marayu yayi qaranci, kina tunanin idan uwa batayi fad'i tashi wajan nemawa yarnta abuba yaya zasuyi?"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now