5

1.7K 174 16
                                    

KUNDIN HASKE

ALKALUMAN MARUBUTA🤝

*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*

*Wattpad :-AyusherMohd*

TARE DA ALKALAMIN

*Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*MENENE MATSALAR?*

*Babi na Ashirin*

Domin neman Kundin Haske daga na 1 zuwa na 20 ziyarci https://my.w.tt/psg00vI7a5. Ko wani babi yana kushe da labarinsa ne, ba cigaba bane ba kuma a hade suke ba.

Last Page

Duk yanda taso tao bacci ta kasa, tana zaune tana juye in baby ta motsa ta dauketa, Abdul ma na falo ganin karfe daya na dare yasa bayan baby ta koma bacci ta mike ta turo kofar dakin.

Kwance ta ganshi ya daura hannunsa akan goshinsa, jin motsinta ne yasa ya dan juyo kadan, hawayenta ta maida ta tsaya kusa dashi, mikewa yai ya zauna yana kallanta.

Fitilar wayarta data kunna ta ajiye a gefe sannan tai murmushin karfin hali tare da zama kusa dashi.

Shiru ne yadan ratsa a tsakaninsu kafin ta daure tace “nayi laifi a tunanina kaine zakace muje gidan Umma sannan a nawa shirmen gani nake ni kadaice a cikin damuwa.”

Shiru yai bai tanka mata ba, murmushi ta sakeyi wanda yai sanadiyyar gangarowar hawaye tace “me kake gani in naje gida? A matsayin wanka?”

Kallanta yai sai dai baice komai ba, tace “kila in muka rabu na dan wani lokaci zafin juna da muke ji zai tafi, sannan laifin juna da muke gani zai ragu.”

Kallanta yai yace “bakya tsoron kafin ki dawo wani abun ya faru?”

Kallansa tai idanunta sun ciciko tace “ya kake so nayi? Na rasa daga ina matsalar ta fara? Daga waje ne ko daga ciki ne? Laifinane ko naka? Taya zamu zauna muna ganin laifin juna ga jaririyar da take bukatar kulawarmu?”

Bata jira yace komai ba tace “meyasa sanda nama laifi baka fadamin ba? Ina ji da duk abin bai kaimu haka ba.”

“Ke kin fadamin? Ba rikeni kikai a ranki ba? Sai ma karata da kikai gun yayarki?”

Inalilahi wa ina ilaihi raji’un abinda take fada kenan a kasan ranta.

Sunyi shiru kafin yace “bana san maganar zuwa gidanku dan maganar gaskiya........”

Kallansa tai tace “baka san tarbiyyar gidanmu?”

Yace “eh, dan na tabbatar shine ya jawo mana halin da muke ciki yanzu.”

Kallansa tai tace “Abba ya bamu tarbiyya matuka, dukanmu sai da mukai sauka kafin mu gama secondary sannan kulawa da ladabi muna dashi.”

“Amma lokaci daya suka ruguzashi, na sanki macece mai ilimi da ladabi meyasa sanda nazo da kazamar magana baki hukuntani ba? Karshe ma sai amincewa kikai dani? Kin manta kin fadamin a sakonki akan matsa miki akan aure da ake a gidanku? Wanda na tabbatar hakan ne ya ja?”

Shiru tai dan tasan hakane.

(Meyasa iyaye bazasuwa ‘ya’yansu addu’ar miji na gari ba sai dai su sasu a gaba da kyara da hantara akan rashin aure? Wanda hakan ba karamin cigaba gun lalata rayuwar ‘ya’ya mata bane a wannan lokacin? Wasu ‘yan mata wannan dalilin ke jefa rayuwarsu ga halaka domin neman mijin aure, wasu wannan ke sa su shiga rayuwar bin malamai dan ganin sun samu mijin da sukesi ya auresu? Dan Allah iyaye a ma ‘ya’ya addu’ar miji na gari wanda zai kula dasu, sannan ke ko ni in bazakiwa ‘yar uwarki mace dabatai aure ba addu’a ba to ki kama bakinki kiyi shiru, duk macen data fada halaka saboda bakinki karki manta a kods yaushe kina da kaso a ciki laifin data tafka. Allah yasa mu dace Ameen)

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now