5

1.8K 222 18
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        _*Al’kaluman marubata*_

  _*KUNGIYAR:-*_
_*HASKE WRITERS ASSOCIATION*_
_(home of expert and perfect writers)_

_TARE DA AL KALAMIN_

*_MAMUH GEE_*

_BABI NA GOMA SHA SHIDDA_

*YIWA KAI*

*5*

Hankalinsu sosai yatafi ga kallon lokacin uncle shamsu yashigo Yana cewa"

Yau aminai uku sun hadu Allah ya rufa mana asiri dacin qonannen abinci Dan kuwa yau Babu sauqi.

Batareda zun juyo sun kallesaba maman sadeeq tace"

Uncle shamsu kaidai kawai karka tsaya dogon zance idan kallon zakayi zauna kayi.

Girgiza Kai kawai yayi Yana dariyar shirmensu ya fice Yana cewa"

Kudai da jarabawar ta sama saiku bada himma kuyitayi.

Fitarsa ko mintuna ashirin baiyiba yadawo ya kalli Maryam dako talla batason aje yace"

Tou qaramarsu babbarsu manager yadawo Yana waje Yana kiranki yakira wayarki baki dagaba.

Harya juya yaga alamar ba yanzun zata tasoba yasake juyowa yace"

Kamarfa Kiran gaggawane naga kamar hankalinsa baa kwance ba.

Jin haka duk Suka juyo Suka kallesa
Maryam din tayi saurin miqewa tana cewa"

Wlh na tsani kallon maimaici nafison na ringa kallonsu da zafinsu musamman yau danaso kallon auren shivangi da rockyy.

Gyalanta ta Zara da wayarta data saka silent gudun damuwa ta nufi qofa tana cewa"

Qila nadawo idan naji menene qila Kuma Saidai gobe Kuma.

Hafsat tace"

Allah dai yasa yabarki kidawo Dan wlh yau akwai case a wannan auren nasu Rocky Dan sesha bazata yarda ba kisa zata ringa yi.

Maman sadeeq tace"

Tayi abanza ma bare anrabata da Rocky.

Ganin tafara shawarar fasa tafiya yasa  uncle shamsu cewa"

Muje hajjaju Yana can Yana jira.

Wucewa tayi tana tsakin takaicinsa nadawowama da wuri Dan bai Saba dawowa ba irin wannan lokacin.

Yana ganin fitowarta gate yaqaraso cikin sauri yace"

For good sake Maryam magrib ta gabato bazaki zauna a gidanki....

Katsesa tayi cikin 'yar murya da cewa"

Wuta fa aka dauke nazo kallon episode daya dama yanxu nake shirin komawa gida.

Muje gidan sauri nakeyi jakar dazu Dana shigo da ita na ajiye a daki Zaki bani ana banki ana jirana asubar farko Lagos zamu wani aiki zamu kwana yi a bankin yanxu.

Wucewa sukayi suna shiga dakinsa suka wuce yace"

Yi sauri kiban anacan ana jirana.

Kallonsa tayi tana aje gyalenta tace"

Ina ka aje to?

Cikin zaquwa yace"

A wardrobe na aje dazu Dana kawo Ina nasan Ina kika maidata Dana sani zan tsaya Bata lokacina zuwa nemanki ne.

Kallonsa tayi tace"

Ni banma ga jakarba bare na canza mata guri.

Wardrobe din tabude ta dudduba tajuyo tace Bata cikin nan.

KUNDIN HASKE💡Onde histórias criam vida. Descubra agora