5

1.1K 112 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

   *Al-K'aluman* *Marubuta*

  KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home_ _of expert and perfect_ _writer's_ )

     *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

   *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN........*

  _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

                 0⃣5⃣

Washegarin ranan misalin karfe d'aya na rana Ruk'ayyah ta isa gdn su Zee Zubair ba tayi zaman mintina sha biyar ba Ahmad ya iso , Zainab ce takaisa d'akin da suke sauke baki na gdn tareda wadatashi da lemuka da snack's kafin gimbiyar tasa ta fito

Ruky cikin takunta ahankali wanda tunda ta tinkaro d'akin jikinta yasake yin sanyi , wani irin k'aunarsa takeji nasake mamaye ilahirin jinin jikinta , hakan yasake saka take tafiya tamkar wacce aka zarewa lakkan jikinta , sallama tayi ahankali cikin muryan ta dako cikin bacci Ahmad yaji yake sake samun natsuwa , amsa mata sallaman yayi idanunsa nakanta tana sanye ne cikin doguwar riga wanda yakamata daga sama , daga kasa kuma abude yake ta yane kanta da mayafi wanda  yadace da shigan jikinta sosai tai kyau sbd Allah yabata baiwan kyawun da dirin jiki me kyau , babu wata kwalliya akan fuskanta inka d'auke kwalli da lips stick da tagoga a lab'b'anta , harta tasamu guri tazauna a kujeran dake kusa dashi baidaina kallon taba , hakan yasata sakin masa k'ayataccen murmushin ta kafin ta ciri murya tana fad'in

"Barka da zuwa masoyina da fatan ka iso lfy? "

Shima murmushin ya maida mata har kuma zuwa lokacin bai d'auke idanunsa akanta ba , sosai yaga yau d'in kaman an k'ara mata wani mugun kyaune , da kyar ya iya bud'e baki ya bata amsa da fad'in

"Lfy lau na iso gimbiyar mata my rabin raina wannan kuma raman ta mecece ? "

Yakarisa mgn yana sake tsareta da idanunsa tuni zuciyan Ruky yasake karyewa hawaye suka fara taruwa acikin idanunta , cikin rawar murya take fad'in "My habibi raman halin da akeso ajefa zukatanmu ne aciki,  wlh bana sonsa na tsaneshi kaina keso Ahmad kaine kafi dacewa kazama mijin aurena bashi ba , meyasa iyayena basu duba so da shak'uwan dake tsakaninmu ba sukeso suraba soyayyan da aka ginata cikin aminci ? Ahmad kasama mana mafita wlh idn ban aurekaba rayuwata tana cikin gagari. "

Takare mgn tana sakin kuka ahankali wanda atake ya sake jefa zuciyan Ahmad cikin kunci da tsananin tausayinta , yana tsananin k'aunarta yasani son da suke ma juna dole su shiga cikin mawuyacin hali idn akayi anfani da karfin iko aka raba tsakaninsu, sai dai a yadda idanuwan iyayenta suka rufe da KWAD'AYIN abn duniya zaiyi wiya su cinma burinsu , cikin k'arfin hali yafara rarrashinta da fad'in

"Ruk'ayyah mafita guda d'aya ce kaman yadda nasanar dake jiya shine mucigaba da gayawa Allah , domin a yadda idanun iyayenki ya rufe da k'iyayyata zaiyi matukar wahala mucimma burinmu ,ina sonki Ruky son da bakina bazai iya misaltawa ba ke kad'aice macen danake rayuwa da matsananciyar k'aunarta azuciyana bayan mahaifiyata, sai dai duk irin yadda nake jinki araina bazan iya baki daman kibijerewa iyayenki akan kudirinsu ba , kiyi hakury kimusu biyayya ni kuma kimin addu'a domin rayuwata nima tana cikin wani hali , nazo ne inmiki nasiha tareda miki albishir nasamun aikin danake nema a lagos ya samu , bazan iya sake kwanaki uku agarin nan ba domin zuciyata bazata cigaba da juran ganin anyi baikon ki dawanina ba , ina miki fatan alkhairy da samun kyakykyawan rayuwa a gdn aurenki '
Sai dai ina miki albishir dacewa har yabada zuciyan Ahmad zata cigaba da rayuwane akan sonki da k'aunarki Ruk'ayyahhh.... "

Shirune yaratsa d'akin bayan mgn sa tayanke sakamakon wasu hawaye da suka fara zuba daga idanunsa, bazai tab'a iya cigaba da mgn ba domin shikad'ai yasan irin zafi da rad'ad'in da zuciyansa kemasa,sautin kukan Ruky ne ke fitowa ahankali yake ratsa zuciya da gangar jikinsa , wanda hakan ke sake hautsina nutsuwa da lissafinsa sun d'auki tsayin mintuna ahaka kafin yayi karfin halin kama hannuwanta karo nafarko da yayi hakan atare da ita , bata janyeba kotayi yinkurin hanashi hakan yabashi daman fara murza yatsun ta ahankali idanunsa da suka sauya launi ya tsareta dasu , batareda da d'ayansu yasake yinkurin cewa komiba illah zuciyoyinsu dake raba sak'wanni atsakaninsu, kukanta ne yafara raguwa harya d'auke sai ajiyan zuciya da take saukewa ahankali hakan yasashi sakin hannunta batareda ya d'auke idanunsa akan taba

KUNDIN HASKE💡Donde viven las historias. Descúbrelo ahora