3

1.5K 192 9
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        *_Al’kaluman marubata_*

   *KUNGIYAR:-*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(home of expert and perfect writers)_

_TARE DA AL KALAMIN_

*_MAMUH GEE_*

_BABI NA GOMA SHA SHIDDA_

*YIWA KAI*

*3*

Qarfe takwas Kamal yagama komai ya fice office nan ta zauna tayi breakfast tana cikin ci maman sadeeq tashigo riqeda sadeeq Dan kimanin shekara uku.

Maman sadeeq wlh yanxu nake cewa Dana gama nashigo gurinki.

Dariya tayi tana zama tareda cire hijabinta tana cewa"

Wlh baqi nayi jiya bayan fitarku Kuma nepa sukayi mana tsiya yanxu Kuma Ina dubawa wlh natashi a Rashin sa'a naga subscription din receiver Dina ya qare ai Ina ganin fitar baban amal na taho.

Ai Nima jiya jajen qaninsa da aka sacewa mashin mukace Kuma wlh sai guraren Tara muka dawo ban kallaba saiyanzu nake nutsuwa naga ya za'a qarqare musamman fire and ice inason sanin shin Anita zatai nasara kuwa Dan wlh inason auren kunj da twinkle.

Ahankali suke kallon suna fira dukkanin hankalinsu nakan kallon sai ihun sadeeq sukaji da sauri Suka kalla sukaga harya Kai dining ya janyo cokali mai yatsu ya tura abakinsa shine ya sokesa a maqoshi.

Da sauri hafsat ta janyosa tana lallashinsa tana basa haquri tareda miqawa mamansa shi ta karbesa.

Ganin yanason asake sakinsa yasa tasakesa ya sake komawa gurin dining din wannan karon qarar fashewar plate sukaji daya jawo harya Dan yankesa a qafa Amma baiyi kukaba nan mamansa tasake janyosa,

Hafsat tace"

Karki sakesa yakoma gurin glass dinnan fa zaiji masa ciwo kafin mugama saina share.

Qin zama yayi ala dole sai ansakesa ita Kuma taqi sakinsa hakan yasa yafara rigima yanason rikice mata ta daka masa tsawa zatai masa fada saiga uncle shamsu yashigo Yana cewa"

Kai maman sadeeq soldier kikewa tsawa haka.

Yauwa uncle shamsu Dan Allah miqaminshi gurin nuhu kokuma mai gadi kafin nafito.

Karbarsa yayi Yana masa wasa Yana jefasa sama Suka fice.

Kallonta hafsat tayi tareda maida hankali kan tv tace"

Maman sadeeq meyasa kike bada sadeeq koyaushe gurin nuhu ko mai gadi bakya gudun ko basuda lfy su saka masa wani ciwo hardai mai gadinnan naki kullum Yana riqeda buta gurin zagayawa shikuma nuhu kina ganin ba'a raba almajirai da qananun quraje koyaushe duk da dai shi naga ya girma ya kile har dinkuna naga yanayi.

Dariya maman sadeeq tayi tana cewa"

Kai banason sharri hafsat
Ke kuwa babu komai ai sbd sadeeq din na namiji ne nake Basu shi inda mace ne mezai kaini akaini abaro,
Amma shi Kinga namijine Dan uwansu.

Eh to hakane Kuma ai wlh ni mai mace Saida ta tsantsan shiyasa ko family house dinsu babanta cewa yakeyi kar avari samarin nan na fita da ita waje.

Amal ce ta fito daga daki tana mitsitsika idanuwa tana qananan kukan Kiran babanta.

Kafin hafsat ta tashi ta dauketa uncle shamsu yadawo palon tana ganinsa tayi gurinsa tana miqa masa hannu.

Yauwa uncle shamsu tunda abinci zakaci kuci tare Dan yanxu danace nixan Bata kuka banxa zataitamin.

Daukarta yayi Yana cewa"

Dole tayi kuka anty sbd rabin hankalinki baya tareda Bata abincin ne matuqar akwai nepa.

Dibar abincin yayi yace"

Munje muci abincinmu Dan nan damunmu zakuyi da hayaniyarku.

Yana isa dakinsa ya sanya key duk da dai yasan idan suna wannan jarabar kallon haryayi abinda zaiyi yagama yasan basuji Basu gani.

Abincinsu sukaci Suka qoshi kafin ya mimmiqe kan katifa ya jawota ya saka mata Yana cewa"

Amal zoki Sha sweet dinki mai dadi kinji.

Tutture Kai tashiga yi tana janye fuska ya ciro wayarsa da chocolates yafara yimata wayo da dabara harya samu yanda yakeso.

Wanka yayo ya gyarata tareda fesa mata turarukansa masu qanshi tareda Bata sweet kala kala masu qamshin flavor daganan Suka hau game atake bacci ya dauketa.

Tashi yayi ya bude dakin ya nufi cikin gida da ita yakaita har lokacin suna sana'ar ya kwantar da ita yace musu ya futa.

Bayan tafiyar maman sadeeq tahau aikin gidan cikin farin ciki tana 'yan waqoqinta.

Itama maman sadeeq tana isa bakin  gate din gidanta daidai baba mai gadi na fitowa daga dakinsa riqeda hannun sadeeq Yana masa wasa.

Iyye baba harda rake kasiyawa mutumin naka.

Dariya baba maigadi yayi cikin girmamawa yace"

Ai mutumin nawa Yana son rake.

Ankuwa gode baba kana kulawa da mutumin naka sosai,
Yanzuma yayi zamansa agurinka nashiga na rage ayyukan gidan tukuna.

Da daddare bayan sun gama komai sunyi Shirin kwanciya kamal ya kalli amal dake jikinsa yace"

Meyasa jikin amal yanxu koyaushe da zafi kamar mai zazzabi?

Hawowa gadon tayi tana Jan bargo Dan rufe jikinta tace"

Wlh Nima naji Kuma kaga batada wani alamar batajin dadi ko wani Abu makamancin hakan kawai dai qila duk cikin yayen ne.

Shiru kawai yayi mata sbd yasan koda wani ciwon ne bazata maida hankali tasaniba yanda yakamata ace kowace uwa tasan damuwar yayanta.

Tsawon kwanaki da satittika daga zafin jiki ahankali Kamal yafara lurada yanda amal ke kumburi saiya alaqanta hakan da sanyin daya fara shigowa.

Hakama bangaren hafsat rayuwarta nanan yanda take saima wani kwanciyar hankali da farin cikin zaman uncle shamsu ataredasu datake sake ji sbd sosai yake kular mata da amal yanxu batada fargabar rigimarta data fara take kaita gurinsa kota kirasa yazo ya dauketa,

Maman sadeeq tuni Suka qara samun abokiyar firar dramominsu sbd sabuwar maqwafciyarsu itama tana kallon series din tuni Suka dinke Saidai ita Bata taba haihuwaba Kuma itama mijinta manajan banki ne Saidai ita Sam Bata iya zama gidanta ita daya tayi kallon Saidai tabaro mai aikinta gidan tazo ko gidan maman sadeeq ko hafsat suyi kallon suna firarsu hankali kwance.

Ranar wata jumaa sukaje gidansu hafsat din bayan masallaci Dan gaidasu.

Karbar amal hajjo mahaifiyar hafsat tayi tana mata wasa tace"

Ke 'yar yaye tunda kika koma gidanku sai yau kike zuwar mana har munsake samun wata 'yar yayen 'yar gidan Ahmad itama gatacan gurin Salma anakawo yaye.

Dagata sama tayi tana cewa"

Lala lallai yarinya me iyayen naki suke baki kikai wannan kumburin kumatu kamar ana saka miki iska.

Daria Kamal yayi yace"

Hajjo wlh gatanan sai kumburi takeyi ni cewa nayi kodai sanyin nan ne?

Kallonta hajjon tayi tace"

To ai sanyin bai shigo irin yanda za'ayi tunanin shineba.

Cikeda kulawa yace"

To kodai muje asibiti ne sbd harda zafi jikinta nayi musamman kwanakinnan.

Kallonta hajjon tasakeyi dakyau taga harda sake jikin amal din yayi babu qwari kamar dah
Ta juya ta kalli hafsat dake fira da Salma qanwarta dake bin ta tace"

Hafsat meke damun amal babanta yace tana fama da zafin jiki sosai Kuma wannan kumburin fa?

Kallon Kamal din tayi takalli hajjon tace"

Wlh Nima bansaniba hajjo Amma Bata wani ciwo fa kawai dai shi ya damune sbd Yana tunanin Wai sanyine.

Girgiza Kai hajjo tayi tana cewa"

Gskia Babu wani sanyi a tattareda yarinyar nan Amma dai ku riqa shafa mata man kade ku sirka kadan da rubb idan kumburin bai rageba kwana biyu gskia Kam dole aje asibiti sbd Nima kumburin bai bani nutsuwa ba gskia.
#mamuhgee

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now