Shafi na biyu

1.4K 150 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Haske Writer's Association*💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*RAYUWAR WASU MA'AURATA...*

*NA*

*UMMU BASHEER*

Babi na goma sha uku


Page 2






.....Zaune take ta sunkuyar da kanta. Yayin da wata Mata ke kan kujera sai shan fruits take.

Cikin sanyi murya Layla tace" Mami ina yini"

Cike da massifa matar ta dago Kai " naji ai ko sai kin fasa min kunne ne. Da kike tambaya na ina yini. To ban ganshi ba. Nace ban ganshi ba"

"Kiyi hakuri Dan Allah. ..."

"Rufe min baki. Anki ayi hakurin, ni tashi a gaba na. Kinzo kin wani sunkuyar da kai na munufurci. To Allah ya fiki "

Tashi tayi cikin sanyin jiki ta bar part din Mami.

Zama tayi kan kujera tare da tunanin irin matsalar da take fuskan ta .

Tunda Rayyan ya shigo yake faman sallama Amman Layla sam bata San da shigowar shi ba.

Zuwa yayi ta Bayan ta tare da rufe Mata ido. Ajiyar zuciya tayi. Tana cewa "My love "

Murmushi yayi tare da zagayowa ta gaban ta. "Mene ne ya samu princess dina hardware na shigo bata sani ba?"

Murmushi tayi ta Mike tana kokarin boye damuwar ta" My love i knew you're tired. Muje Kaci abinci Sai ka huta "

Murmushi yayi " wato kina son ki min wayau ko. Ba Zaki fad'a min mene ne ba"

"No ba haka bane, babu abinda ke damuna, please dear let's go "

Haka ya zauna kan kujera tayi serving nashi abinci. White rice and vegetables soup, sai juice din pineapple .

Yana ci Yana santi. Yana zuba Mata soyaya, a haka har ya gama. Sannan ya koma kan kujera ta zauna tana mishi massaging.

Kwatsam sai ji sukayi an bude kofa babu ko sallama.

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo.

Rayyan ranshi a bace yace " Ke Hanan baki da hankali ne Zaki shigo guri babu ko sallama "

"Kayi hakuri Ya Rayyan, Mami ce tace na Kira ka"

Tsaki yayi yace "I'll teach you a lesson"

Ya tashi tare da fita. Ita Kuma sai da ta watsa ma Layla harara sannan ta fita.

Layla idan da sabo ta riga ta saba da wannan halin na Hanan kanwar mijin ta.


Yana shiga ya samu mahaifiyar shi tana zaune a kujera tana kallon news.

Zama yayi tare da gaishe ta. Ta amsa fuska daure . An dauki lokaci kafin ta kashe news din ta juyo tare da cewa " Ya Maganar mu da kai? "

Dukar da kai yayi yace " Mami Dan Allah kiyi hakuri. Insha Allah komai Yana da lokacin shi..."

"To Ubana ai nasan da hakan. Komai lokaci ne. Amma ina son ka sani. Ni bazan sake daga maka kafa ba" ta katse shi da fadin hakan.


"Mami Dan Allah ina kara baki hakuri "

"Abinda zance maka shine ka tabbatar kaje ka ga yarinyar nan. Tashi ka bani guri "


KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now