6

1K 102 2
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Al-Kaluman Marubuta*

KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home_ _of expert and perfect_ _writer's)_

     *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

    
      *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN.......*

      _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

             0⃣6⃣

Fita yayi yabar mum d'in dabin bayansa da kallo , koda ya sakko k'asa salmah nanan yadda yabarta jin takunsa yasata mik'ewa zaune daga kwancen datake , tana binsa da mayen kallo sosai shigan jikinsa yaimata kyau ganin zai fice batare dayasake kallon inda take ba yasata mik'ewa cikin sauri tasha gabansa tana fad'in

"Hey my cwt miye hakan wai menayi mane kake shareni kwana biyu? I miss u ya Kamal. "

Takare mgn tana kokarin kusanta jikinta danashi , shikuma idanunsa akan kirjinta yake wanda suke matuk'ar burgesa domin duk a halittan jikin mace babu abnd ke saurin tada masa hankali irin gurin nan, hannu yasa yashafo gurin batare daya saki fuska ko yasata ajikinsa kaman yadda take so ba yaciri murya yana fad'in

"Kinfi kowa sanin nibana lallab'a mace ai , kwana biyu ke kika gujeni so kike inta binki don kawai kina bani abnki ina mora? "

Yakare mgn yana kawar da fuskansa daga gareta, yafara cigaba da tafiya hakan yasata rik'o hannuwansa tana fad'in

"Sorry my cwty wlh nayi missn d'inka plxx komi yawuce naji laifinane , anjima zamu shirya to nayi ma alqawarin faranta ranka sosai . "

"Dakin kyauta baby sakeni zan fitane inaso inbiya inga babyna , don anjima zan wuce UK bye saina dawo . "

Kamal yayi mgn yana me zare hannunsa daga rikon da salmah tai masa yai ficewansa , ya barta tsaye tanajin wani kishi da haushin Ruky nasake mamaye ranta , ta tsani yarinyar tunma ba'a kaiga auren ba ahankali takoma ta kwanta zuciyanta namata zafi

Koda kamal ya fita gdn wani abokinsa umar ya nufa ya d'aukesa suka wuce gdn su Ruk'ayyah, kaman koyaushe kamal yayi kiran wayan Ruk'ayyah bata amsaba, yana kok'arin kiran line d'in umman sune saiga Nadeeya tafito daga gdn zata unguwa, hakan yasa kamal ya fito cikin isa da jin kansa yake mata mgn tareda sanar mata yakira Ruk'ayyah bata d'aga ba, batare da Nadeeya tace dashi komi ba tajuya takoma cikin gdn domin sanarma qanwarta zuwan kamal d'in

Fitowan Ruky daga wanka kenan tana shafa Nadeeya tai sallama tashigo d'akin , Ruky ta amsa sallamn tana fad'in

"Ya Nadee baki tafiba ne ? "

Nadeeya taja tsaki kad'an tana cewa

"Wlh ina fita naci karo da mutuminki Kamal yazo , gashican shida abokinsa yace yakira baki d'aga ba ashema wanka kika shiga , so saiki shirya kifita tun kafin yakira umma tazo tana miki masifa ni kinga tafiyata . "

Takare mgn tana ficewa yayinda Ruky tacigaba da shafanta cikeda b'acin ,ko sunan kamal aka anbata ranta baci yake  ayanzu batada mak'iyi aduniya sai shi dayake so yazama silan rabata da farin cikin ta kotace yama zama d'in, agurguje tagama shafan ta zura Riga da skat ajikinta powder kawai tashafa sai kwalli ta zari hijab ta fice ranta ab'ace fuskannan ahad'e tamkar bata san wani abu waishi dariya ba aduniya , shikam gogan naku tunda tafito idonsa nakanta sam bayi k'aunar ganinta da hijab amma babu yadda zaiyi yasani yarinyar bata sonsa sai dai shi hakan badamuwansa bane tunda yaci alwashin saiya aureta ahakan so zai daure harta zamo abn ikonsa daga lokacin zai kalleta aduk ta sigan dayaga dama abnd yake rayawa aransa kenan harta kariso gurin motar

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now