2

1.3K 119 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*K'UNGIYAR HASKE WRITER'S ASSOCIATED*💡
(Home of expert & perfect writer's).

*Tare da:-*
      *Alk'alamin*

*MARYAM IBRAHEEM*
(Ummu Hanan).

*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

*SHAFI NA BIYU*

    *SATAR FITA*
          (Halayyar wasu matan)

Washegari bayan husna ta tafi makaranta Ahmad ma ya fita, ji tayi zaman gidan duk ya dameta dan itakam indai bata fitaba tofa batajin dad'i.

   
   Mayafinta ta zara ta fito ta rufe gidan ta tafi gidan wata kawarta dake can karshen layin, yar kasuwa ce sosai duk wasu kayayyaki na amfanin mata tana siyarwa hakan yasa gidan sam baya rabo da matan unguwar da kuma wasu daga wurare daban daban.

   Kamar ko yaushe gidan cike yake da mata an baje haja kowa na zab'ar abinda yake so, shewa da surutai kawai ke tashi.

    Shiga tayi itama aka fara da ita, kasancewar ita ba siya zatayi ba yasa saidai ta taya masu siyan zab'e.

    Hira tayi dad'i harta manta da lokacin tashin su husna daga makaranta ya wuce, sai data dubi agogo ta lura da hakan.

   Sallama tayi musu ta bar gidan da sauri.

   Tana fita aka dasa gulmarta yadda take fita ba iznin mijinta da yadda take da shegen yawo.
   Wasu na zaginta wasu kuma masu hali irin nata suna kareta (kunsan dai yadda halinmu na mata yake😢🤣).

    Kai tsaye gidan zainab ta shiga,dan tasan husnan can zata shiga idan ta dawo ta tarar bata nan.

  
Ilai kuwa tana shiga gidan ta samesu a tsakar gida suna cin abinci ita waleed, zainab kuma na bakin famfo tana wanke wanke.

   Kujera yar tsugunno taja ta zauna tana fad'in

   "Dama nasan kina nan ai".

    Cikeda takaicin mak'ociyar tata zainab ke kallonta tace

   "Saboda Allah maman husna wace irin rayuwa ce wannan?, Kinsan yarinya na makaranta kuma kin tashi kin fice ace yarinyar nan ta dawo ga yunwa ga gajiya amma ta dawo bata sameki a gida ba".

   "Kai maman waleed yanzun data dawo bata sameni ba me ya kamata?, Kuma ba gashi ta shigo gidanki ba meya sameta..?"

   "Toh yanxu alal misali ace nima bana nan fa ya kikeso tayi...?"
Zainab ta jefo mata tambayar tana sharce gurin da tayi wanke wanken.

   Sanin bata da amsar bayarwa yasa tacewa husnan tayi sauri ta gama su tafi.

   Tana gamawa tasa takalmin ta ta dauki jakarta suka fita bayan tayi mata sallama.

   Girgiza kai kawai tayi ta cigaba da aikinta, taga alamun maman husna tayi nisa sam batajin kira.

    

   ★★★. *After Two days*

Zaune take a tsakar gidan bayan ta gama abinda zatayi.

   "Kwana biyu fa ban fita ba k'afata k'aik'ayi take wlhy".
Cikin ranta take mgnr gami da janyo wayarta dake kusa da ita tayi dialing number Bushra bata jima tana ringing akayi picking.

   Gaisawa sukayi kafin Rabi'a tace

   "Yane k'awata babu wani dan bikine ko suna kwana biyu ban fitaba k'afata k'aik'ayi take".

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now