12

1.1K 115 2
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *Al-K'aluman* *Marubuta*

   KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

         *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

   *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN.......*

         _Tareda_ _Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo* *Lemu* 🖊

                    1⃣2⃣

Yini guda tayi a gdn su Kamal d'in sai dai sam babu wata sakewa datasamu , sbd momy bata nuna mata sakin fuska da kulawan dazataji ajikinta lallai tana murna da shigowanta rayuwan d'an nata ba , abnd yasake dugunzuma zuciyan Ruk'ayya tana tunanin wani irin rayuwa zatayi kenan acikin familyn su Kamal ga dukkan alamu momy tana cikin sahun matan masu arziki da sukafi sha'awan had'a zuriya da mutane irin su , sai gashi ita k'addara da KWAD'AYIN iyayenta ya shigo da ita cikin su

Sai dare yazo d'aukan ta suka koma gdn,tana shiga ciki sama ta haura kaitsaye zuwa bedroom d'inta , wanka tayi tafito d'aure da alwala tai shafa'i da wuturi rigan bacci tasaka masu kaury tahaye bisa bed domin batajin yinwa bare tanemi komi

Chart takeyi da frnds d'in ta Zee da Aysha suna sake kwantar mata da hankali domin bata iya boye musu damuwanta , sunriga sun zame mata aminan kwarai dake bata shawaran arziki akan damuwanta ,sam bataji shigowansa ba illah jikawai tayi anfisge wayan hannunta tareda jifa dashi can karshen gadon,  kiris yarage wayan tayi k'asa ta tarwatse

Baijira komiba ya d'auketa zuwa bedroom d'insa , kobai mata mgn ba tasan kwanan zancen hakan yasa hawaye suka fara wanke fuskanta na bak'in ciki da tsanan sa shikenan ita bazata samu irin soyayya da tarairaya daga mijin aureba sai dai duk sanda yaga dama zaiyi kwanciyan aure da ita yanuna mata gadara yayi yadda yaso , tun tanamasa gardama taga ita Kecin wuya har tazabi bada kai cikin lumana  , wassanni yafarayi da ita yadda yakeso tareda bata umurnin maida masa martani kaman yadda yake buk'ata , sosai yake bida ita cikeda kwarewa gaba d'aya ya gama rud'a lissafin Ruky,  nidai bansake jin d'uriyan komiba domin cikin sauri na rufo musu kofar ina zare idanu domin lamarin azimun ne lol.....

*Bayan wata d'aya*

Ruk'ayya ce durkushe acikin toilet d'in d'akin Kamal tana kwara amai tamkar zata amayar da kayan cikinta, tayi biji-biji tafita hayyacinta , gogan nadaga bakin kofar toilet d'in ya hard'e hannunsa akirji tareda tsura mata idanunsa , harta gama ta wanke fuskanta da bakin tazo tarab'e ta gefensa ta fice daga d'akin baki d'aya , kafin yataka yakoma bakin bed d'in yazauna yana dafe kansa tareda tunanin mekuma kedamunta ? Wani firgicine ya ziyarci ransa alokacin da zuciyansa yaraya masa kardai Ruky ciki tasamu tun baigama lale amarcinsa ba .....

Koda takoma d'akinta kwanciya tayi tareda sakin marayan kuka tana addu'a Allah yasa ba cikine da itaba , domin bata fatan had'a zuriya da Kamal Alqasim sosai hankalinta yake atashe

Turo kofa da shigowansa ne yasata sake rintse idanunta , tareda kai hannu ta toshe hancinta domin bata son jin qamshinsa ko kad'an , abakin gadon ya zauna tareda had'e face tamkar baitab'a sanin miye dariya ba

Kafin cikin dakiya yayi mgn yana fad'in "keh! Tashi zaune mgn zamuyi "

Ko motsi Ruky batayiba hakan yasashi fisgota da karfi ta fad'o kirjinsa , wani kuka tasaki tana sa hannu bisa hancinta sbd yadda kanta kesarawa turarensa na hawa bisa kanta , zuciyanta ne yashiga hautsinawa wani aman nataso mata da kyar tayi mgn

"Kamal kasakeni don Allah kafita bani k'aunar ganinka bare jin qamshinka "

Ruky tayi mgn tana kwace jikinta tasake komawa ta kwanta , binta da kallo yayi yatashi yabar d'akin waya yayi yakira family Doctor d'insu yasanar dashi address na gdn sa , tareda bashi lokaci kalilan yazo ya duba masa meke damun Ruk'ayya ,ba'a rufa cikakkun 40minutes ba Dr. Rayyan yazo gdn afalon k'asa yai masauki Kamal d'in ne  suka sakko tareda Ruky wacce tasanya hijab asaman kayan jikinta , duk wasu tambayoyi daya kama Dr. Rayyan yai mata yayi takuma bashi amsa daga karshe ya buk'aci fitsari tareda jan jininta domin yin gwaji .......

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now