7

1K 105 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *Al-K'aluman* *Marubuta*

    KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

      *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

   *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN.........*

  _Tareda Alk'alamin_

   *Ayshat D'ansabo* *lemu* 🖊

                  0⃣7⃣

A hankali maganganu ke zagaye anguwan nasu Ruk'ayyah gameda irin kayan da aka sauke kawai nasaka ranan aure , bama na lefe ba duk makwabta da sauran dangi nata zuwa ummah na bud'e musu kaya suna gani , masu fatan alkhairy nayi masu akasin haka ma nayi yauma kaman kullum wata makwabciyan su ce tazo ganin kayan , Nadeeya itace take bubbud'emata tana gani matan me suna karima byn tagama ganinkomi tas ta dubi Umma da Nadeeya tana fad'in

"To Ummansu Nadee kayafa gasunan duk wanda yagani yasan badaga k'aramin gd  suka fitoba , don kuwa kaf garin nan babu wanda baisan waye Alhaji Alqasim Nakowa ba , sai dai muyi fatan Allah yasa Ruk'ayyah ta shiga asa'a yasa kuma da zuciya d'aya aka k'ulla wannan aure bawai don kwad'ayin arziki ba , najima ance ita Rukyn bataso kune kuka dage akan hakan , to kada dai ayi abnd bazai k'arko ba azo ana danasani don so dayawa KWAD'AYIN WASU IYAYEN.......Kansa sujefa yaransu cikin wani hali sbd son duniya daga karshe azo kwalliya bata biya kud'in sabulu ba . "

Takare mgn tana tashi tsaye dama tayi alwashin dolene saita yi ma Umman su Ruk'ayyah jurwaye mai kaman wanka, sbd kaf anguwan surutun su akeyi ana cewa auren KWAD'AYIN abn duniya zasuyi ma Ruky , mayafinta ta gyara akan kafad'unta tana sake kallon Ummah wacce tayi wik'i-wik'i da idanu mgn da Karima tayi ta mugun b'ata mata rai , karimance tayi mgn tana fad'in

"Zan wuce Allah sa albarka yasa zamukai lokaci ance duka sati hud'u aka sanya bikin ko ? "

Ummah ce ta amsa da fad'in "Eh kwarai haka aka saka ngd Karimatu da kika shigo domin yadamin mgn , dama ance baka sanin masoyanka na gsky sai irin haka yafaru kake ganin masu nuna maka hassadansu afili , to aure dai babu fashi kuma babu abnd zaifaru sai alkhairy ehe . "

Tak'are  mgn tana shigewa bedroom d'inta tabar Karima atsaye , Nadeeya ma tashi tayi tana duban Karima take fad'in

"Anty Karima sai anjima .

Ko kad'an Nadeeya bataji zafin mgn da Anty karima tayi ba domin tasani dole ne jama'an gary suyi dasu , musamman da kusan duka mak'wabtan su suka san da zaman soyayyan Ahmad da Ruk'ayyah yadda yake kara kaina a anguwan , sannan ace lokaci guda iyayensu sun dakatar dashi tareda juya masa baya akan kyakykyawan manufansa na auren Ruk'ayyah dole ne duniya suyi tir da KWAD'AYIN iyayensu , mgn da karima tayi ya dawo da Nadeeya daga zancen zucin data tafi tana fad'in

"To Nadiya Allah yasa albarka yakawo naki kema muzo musha kallo. "

Karima ta furta tana me ficewa d'aga d'akin tabar gdn tana jinjinan wannan lamari , koda Nadeeya tashiga d'akin su Ruk'ayyah na zaune tana duba wani littafi ne na Addu'o'i , kallo d'aya taima Nadeeya ta maida kanta akan littafin itama Nadeeya bata ce uffan ba tanufi bathroom domin yin wanka

Waya Ruk'ayyah takai hannu tad'auka wanda ke ringing , kallon screen d'in tayi taga bak'in nambobi ne barkatai ke yawo hakan yasa tacigaba da kallon wayan batare datayi yinkurin d'aga wayan ba harta tsinke , aje wayan tayi ta tashi domin maida littafin inda yake tadawo tazauna bakin kafitar tana sanye ne cikin doguwar riga ta material wanda yai matuk'ar amsar jikinta , kalan maroon and milk ne material d'in hakan yasa ya amshi farar fatarta kanta babu d'ankwali sai gashinta datayi fakin d'insa jelan yasauka har kusan kafad'unta , fuskanta yayi fayau babu ko d'igin kwalliya sai tozalin data saka ma fararen idanunta wanda a kwanakin nan gaba d'aya suka rine zuwa launin ja sbd kukan daya zama aboki gareta

Wani kiran ne yasake shigowa akaro na biyu hakan yasata d'auka bakinta d'auke da sallama, Muryan mutumin datafi tsana aduniya ayanzu taji ya bugi kunnuwanta hakan yasata saurin rintse idanunta tareda saurin kashe kiran, ahankali tabi katifar ta kwanta tanajin wani sabon b'acin rai nasake mamaye zuciyan ta , tsanan Kamal Alqasim me zafin gske kesake mamaye ilahirin jinin jikinta tana cikin wannan yanayin Nadee ta fito daga wanka akuma lokacin wayan Ruk'ayyah yasake d'aukan sabon ringing amma ko gezau batayiba , hakan yasa ya Nadeeya ta d'auki wayan tana kallon number's d'in da daga gani kasan na wajene, kallon Ruk'ayyah tayi tana fad'in

"Ruky amshi wayan inaga kamal ne fa daga UK ke kira don naga kaman numba d'in wajene . "

Tak'are mgn tana mik'ama Ruk'ayyah wayan byn tayi receiving don karya yanke baa d'aga ba , hannu Ruky takai ta amshi wayan tareda karashi akunni

"Hello baby na kina jina ?"

Kamal Alqasim yayi mgn yana sauraran jin cwt voice d'inta , tunda ya dira garin UK tunaninta yahanashi sukuni yarasa meyasa bayajin haka akan dukkanin matan dayake taredasu sai akan Ruk'ayyah , sosai tashiga zuciyansa jin tayi batada niyyan mgn yasashi kashe kiran ya don yakira ta vedio call

Jin yakashe kiran yasa Ruk'ayyah kashe wayanta baki d'aya tayi wurgi dashi bisa katifar tareda maida kanta ta kwantar, tunanin Ahmad takeyi wanda kwanaki biyar kenan raban dataji koda muryansa takirashi yafi sau babu adadi amma amsar gudace shine layin yadaina aiki , ta tabbatar yabar garin Kano zuwa Lagos d'in dayace ne tareda sake line wasu hawaye masu mugun Zafine suka shiga kaikawo a kumatunta sam batadamu data sharesu ba , har Nadiya tagama shirin ta tafice Ruk'ayyah batasani ba tanacan ta lula duniyar tunanin ta yadda zata iya gwada yin rayuwan aure da wani ba Ahmad ba

*
A UK kuwa Kamal Alqasim ne kwance bisa katafaren gadon dake d'akin shahararran hotel din daya sauka , wanda hotel d'in tana cikin manyan hotel's d'in da akeji dasu akasar me d'auke da manyan guraren hutawa masu d'ebe kewa , yana sanye da farar singlet ne da bak'in wando treequeter kiran line d'in Ruk'ayyah yaci gaba dayi ana sake tabbatar masa wayan arufe take , hakan yasa ransa yayi masifan b'aci domin zuciyansa babu abnd take kwad'ayin son ji irin muryanta koda ace zaginsa zatai tayi , kaman yadda idanuwansa sukaso ganin kyakykyawar fuskanta , tunda momy ta masa albishir dacewa ansaka lokacin biki yakejin tamkar ana sake fusgar zuciyansane ga Ruky , kullum wani sabon shauk'in son kasancewa da itane yake sake mamaye ruhinsa , ya k'osa ya mallaketa gaba d'ayanta yayi yadda yakeso da ità sake mirginawa yayi bisa gadon yana me jifa da wayan cikeda b'acin rai yake fad'in

"Kin kusa zuwa hannu yarinya zakisan cewa Kamal baya d'aukan raini agurin mace mitsuww..... "

Yaja wani dogon tsaki yana me sakkowa daga bed d'in ya nufi madaidaicin frige d'in dake d'akin wanda cike yake da lemuka da ruwa zuwa duk wani abu dayake buk'ata nasha dai akwaishi aciki , wani lemu yaciro wanda kwalban zaiyi maka kama data kwalaben barasa ne sai dai sam ba hakan takeba lemu ne med'ankaran dad'i , domin shi Kamal duk wani iskancinsa da shagalan sa abnd bai tab'a sha'awan jefa kansa aciki ba kenan wato harkan shaye-shaye sam shi nashi salon sharholiyan na fannin fasik'anci da matane kawai sai rashin tsaida addininsa da uwa uba miskilanci da girman kai , yakan kwantar dakai ne kurum idn yakai matuk'a da son mallakan abu amma daga zaran yasamu shikenan , shiyasa ko mata dayafiso akan komi dazaran yasamu biyan buk'atuwansa to suda banza duk d'aya suke ,

Salmah ce kawai macen dayake mora kuma yak'ara sbd itama tanada wani baiwane na d'and'ano me mugun dad'in datake bashi nutsuwa , sai dai duk da hakan bata tsira ba idn yatashi shareta har sai tabishi da kanta tayi magiya kafin ya saurareta

Lemun sa yakai baki yana kurb'a ahankali sanyin lemun ke ratsa zuciyansa tareda rage masa rad'ad'in takaicin da Ruk'ayyah ta kunsa masa na rufe wayanta datayi ,

***
Anan kuwa kwanaki uku dasaka ranan auren Ruk'ayyah da Kamal Alqasim iyayen Aliyu suma suka zo aka sanya ranan Nadeeya itama ,sun kawo duk wani abu da ake kawowa na al'ada cikeda harkan girma da nuna arziki kwatankwacin yadda aka kawo na Ruky domin shima Honorable Kasheem Matawalle ba  bayabane wajen arziki , domin ko yarik'e madafan iko da dama ayanzu ahakan ma  d'an majalisan jihace anan kano , gashi kuma babban D'an kasuwa agefe guda duk da cewan harkan kasuwancin baki d'aya  Aliyu ya d'aura akai kasancewansa babban d'ansa namiji daya mallaka

Kaman yadda lbryn kawo kayan saka ranan Ruky da Kamal yazageye anguwa haka na Nadeeya da Aliyu yazagaya masu son ganin kwaf suka cigaba da tururuwan zuwa kallo , yayinda a gefe guda mutane keta cigaba da fad'in albarkacin bakunan su wasu suyi fatan alkhairy wasu kuma akasin hakan mafiya yawa naganin wannan aure na zallan KWAD'AYIN iyayensu Ruky ne zai jagoranci ayi wasu kuma gani suke Allah ne yaciyar da yaran gaba tareda tarfa ma garinsu nono zai kaisu gdn arziki
 

Muje zuwa dai don ganin yadda zata kaya .........

*Aysha D'ansabo ce*

KUNDIN HASKE💡Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ