2

151 19 0
                                    

*KUNDIN HASKE*💡
*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)
   
*ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*
   
*NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)
                        *2*
Banda kukan tsuntsaye ba ka jin komai a ɗajin, miƙewa ta yi ta fara tafiya a hankali cike da fargaba da kuma tsoro sai da ta yi tafiya mai nisan gaske ta ga wasu yara  su uku suna zaune kusa da wani katon rafi ba za su wuce ƴan shekara goma sha biyu a duniya, abinda ya ba ta mamaki da kuma tsoro yadda yaran suƙe kama da ita tamkar an tsaga ƙara farare ne tas gashin ƙansu baƙiƙirin har baya an tifqeshi da wani jan qyale suna sanye da baƙin abaya sai gyalen abayar da aka naɗe musu ƙansu kayan sunyi das a jikinsu tamkar ƴaƴan larabawa. kura musu idanu ta yi ƙaunar yaran ya ɗarsu a zuciyata farat ɗaya, murmushi suka yi mata  suka shiga zagayeta suna wani Yaren da ba ta gane me suke cewa, wani gugguwa ne ya turnuƙe wajen zuwa wani lokaci ya tsaya sai ga wannan saurayin ya sake bayyana a gabana ya bude bakinshi ya ce "Maryam... Kinga yaranmu ko? Kinga yaran da kika haifamin ki dawo garemu muna bukatar kulawarki ki rabu da Almustapha Ni ne nan Ɗangam mijinki masoyinki Ki dawo! Ki dawo!!! Ki dawo!!!..." Rintse idanunta ta yi da karfi ta shiga ihu ta na girgiza kanta hawaye yana bin kuncinta, wannan wace irin jarabawa ce? Me ya sa yake neman zautar dani da kuma sakani cikin tashin hankali, yaushe muka yi auren da zai wani ce ni matar shi ce. Ki Adana du wa'innan tambayoyin naki zaki samu amsarsu watarana yana gama faɗin haka ya bace bat.
Almustapha ne ya shigo ɗakin ya hau gadon da sauri ya shiga tofa mata addu'o'i kamar yadda ya saba duk lokacin da ta shiga wannan halin, ta yi lamo a jikinshi ta na sauke ajiyar zuciya ajere.
"Mari!" Almustapha ya kira sunanta a hankali, ban amsa mishi ba shi ɗin ma bai jira na amsa ɗin ya cigaba da cewa "Don Allah don darajar ma'aiki ki fada min gaskiya Mari gaskiya kawai nake bukatar ji ɗaga bakinki, me ya sa kika aure ni Alhalin baki sona?" Ya karashe maganarshi tare da rufe idanunshi saboda ƙunar da zuciyarsa ta ke mishi.  Hawayen da suke zuba bisa fuskata shi ya fahimtar dani kuka ya ke, to ni ta ya ya zan fahimtar dashi ba laifi na bane? Yaushe zai gane ya fahimci cewa bana cikin natsuwata? Wai me ya sa Almustapha da iyayena sun ƙasa fahimtar halin da na tsinci ƙaina aciki? Wayyo ni Maryam na shiga uku! Tsawar da Almustapha  ya daka mata shi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta lulla, wai zaki bani amsa ko sai na tattakaki a wajen nan? Na gaji da wannan iskancin naki yau kimanin sati biyu kenan da daura mana aure kullum cikin tashin hankali nake ciki, da fargaba, ko wane Angon yana farinciki a daren su na farko amma ni daren ya zo min da qunci da bala'i daren ya zo min da fargaba da tashin hankali daren da na sha burin da addu'ar zuwanshi sai gashi ya zo min da wani ƁOYAYYEN SIRRI, wanda duk iyya tunanina da nazarina na ƙasa gano musa6a6in abun, shi ya sa na zo wajen ki don Allah ba dan na isa ba ki taimaki rayuwata ki sanar dani abinda kike nufi... Tamkar a mafarki yaga ta mike tsaye ta fashe da wata irin muguwar dariya wanda saida ya haddasa mishi faduwar gaba, sai da ta yi mai isarta ta yi shiru ta haɗe fuskarta tamau ta kara komawa bisa gado nan da nan barcin wahala yayi awan gaba da ita, takaici da bakinciki shi ne ya turnuƙe Almustapha wato ta ma ɗauke shi mahaukaci ko? Yayi kwafa ya bar daƙin cikin kunar rai. Dakinshi ya nufa ya shiga toillet yayi wanka tare da yin alwala ya na fitowa ya buɗe wadrob dinshi ya dauko farar jalabiya tare da wandon shi ya saka da sauri saboda ana tada sallah a masallacin kofar gidanshi ya dauki dadduma yayi waje, suna gamawa ya zauna jiran sallar Isha'i haka dabi'arshi ta ke baya dawowa gida sai yayi   Isha'i.
Maryam
Barcinta ta ke sha hankali kwance wani irin dad'i take ji yadda ake sarafata sai mimmikewa ta ke ta na jin daɗin abinda ake mata tana nishi da maida martani tana, wani irin daɗin wasar da ake mata ta ke ji bata ma san yadda zata mitsaltashi  ya na shirin nemo hanya ta janye jikinta da sauri ta na girgiza mishi kai  duk cikin barcin, da sauri ta bude idanunta ai ba shiri ta rufe ganin wannan macijin a bisa kanta yana lasarta miyau yana zuba a jikinta ta bude baki ta saki kara tare da kiren sunan Almu... shigowar shi kenan gidan ya ja wani dogon tsaki ya wuce dakinshi sosai ya ke jin Haushinta, ba ta da aiki sai ihu kamar wata marar hankali badai mutum ya ji ta na addu'a yau dai ba zaije d'akin ba koma mene ne ya cinyeta ya ida maganarshi tare da shirin kwanciya yayi addu'o'in shi kamar yadda ya saba yaja bargo ya rufe ilahirin jikinshi can cikin barci ya kara jin ta kir sunanshi wannan karon sai ihu take tana kiran sunanshi tsaki ya kuma ja ya sauko ɗaga gadon ya wuce dakinta da sauri, yana buɗe ɗakin wani wari wari da kazani  ya bugi hancin shi dakin duhu baka ganin komai lalubar inda zai kunna wutar ya shigayi amma ya kasa gani ita kuma sai ihu take can yaji wani murya mai ban tsoro ya ce mishi " kada ka wani wahalar da kanka nine nan na kashe wutan kuma Kada ka matso nan Almustapha idan ka matso abakin ranka, ka juya ka fita kada ka katse min jindadina, banda niyar cutar da kai amma idan ka nuna min taurin kai zanyi maganin ka"
Cikin ƙaduwa Almustapha ya tsaya cak inda ya ke tamkar an ɗasa shi zufa na tsatsafo mishi ta ko ina addu'a ya shiga yi cikin zuciyarshi nan taƙe wani sanyi ya mamaye mai zuciya duk wannan tsoron ya kau, Baƙin shi ya bude dakyar ya fara magana cikin bacin rai "Waye kai? Me ya kawoka gidana? Meye haɗin ka da matat..." Buge mishi baƙin da aka yi shine ya sakashi yin shirin duk a cikin duhun jini na zuba ɗaga baƙin wani irin azaba da radaɗi ya saukar mishi "Ƙul Almustapha kada ka kara yin wannan kuskuren na kiran ilayina matarka idan kuma ka kara fushina zai tabbata a kanka, zan canza maka kamanni zan maidakai abin kwatance Maryam matata ce ni ƙadai an daura mana aure tun da jimawa har mun samu karuwar yara uku, yanzu haka da ka ganni nan hakina nazo tabani shine ta ke nuna min taurin kai kasancewa kullum cikin barci nake saduwa da ita ba ta fahimtar komai, nazo mata a bayyana ne a yau saboda ta ganni a zahiri ba abarci ba, ka yi kuskuren aure min mata Almustapha ya kece da wani uban dariya daƙin ya turnuƙe da wani hayaki Almustapha yayi yayi ya ɗaga kafarshi ya kasa bakin nashi tamkar an rufe shi sai zugi ya ke mishi tari ya shiga yi babu ƙwauƙwautawa ya kasa motsa komai na jinkinshi hankada shi aka yi kanshi ya buga da bango ya yi wani karan azaba ya faɗi a summe bai kara sanin abinda ya faru kuma.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now