Shafi na uku

1.3K 101 0
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*
  *shafi na uku*

  Bintu na gama fadin haka suka kyalkyale da dariyar mugunta suka tafa, sadiya neman bakin cikin da take ciki tayi ta rasa, nan da nan ta tsinci kanta cikin farin ciki tabbas wanan shawarar ita ya kamata tayi tun farko da abubakar da mahaifiyarsa basu nemi sa mata hawan jiniba....

"bintu ni bari inkoma yadda ake ciki kizo jibi dan allah saboda yanzun ma besan zan fito ba shiyasa ma zan koma gidan da wuri"

"to shikenan kawata sai nazo jibin"..sadiya ta mike ta yafa gyalenta bintu ta rakata har kofar gida, a kofar gidan ma ta kara kitsawa sadiya abubuwan da zatayiwa mahaifiyar mijinta da kannensa...

   

  Shukra kanwar abubakar na zaune itada kawarta maryam abokiyar karatunta ta kawo musu ziyara suna hirar sadik saurayin shukrar saiga sadiya ta shigo da sallamarta cikin faraa kamar ba ita ta fita ko kallonsu batayiba, maryam  ce ta amsa sallamar amma shukra ko kallon sadiya batayiba, sadiya ta lura da hakan saita karaso inda suke tace "shukra yau maryam ce ta kawo mana ziyara? "wani haushi ne ya turnike shukra uffan batace ma sadiya ba sai maryam ce cikin faraa tace "ehh nice anty sadiya tun dazun nazo ai naga bakyanan, barka da zuwa"

  "yauwa maryam sannu da hutawa"...sadiya ta wuce dakin mama ta dan daga labule tace "mama sannu da gida na dawo"

  Mama wacce ke zaune kan dadduma ta idar da sallahr azahar mamaki ne ya kasheta na yadda sadiya ta sauya kamar ba ita bace ta fita kamar kububuwa, dakyar mama ta saisaita kanta ta kakalo faraa ta amsa "ah ah sadiya harkin dawo? "

"ehh mama dama gidanmu na leka mamanmu da bataji dadi ba tace a gaisheku"

"allah sarki ya jikin nata? "

  "taji sauki dama dan zazzabine"

  "allah sarki allah ya karo lafiya"

   "ameen mama"

Sadiya ta juya tayi dakinta, itadai maman abubakar abin ya daure mata kai rabon da sadiya tayi mata faramfaram irin haka tun satin farko da aurensu, kodai fada akayi mata a gida? To allah yasa haka.... Tunanin da mama ketayi kenan...

  Sadiya na shiga dakinta ta cire gyalenta ta ajiye a wardrobe kamar bata fita ba takara kimtsa dakin ta kunna turaren wuta sanan ta zauna a kujera tana kallo amma rabin kallon ya tafi ne akan yadda zata juya abubakar ta azabtar da mamansa da kannensa sai yadda tayi dasu musamman shukra yadda tayi mata yau a gaban kawarta kamar wata saarta saboda taga ta musu lakwa lakwa hmmmm shukra zatasha mamaki dan har makarantar datake takama da ita zatasa abubakar ya cireta.....murmushi tayi ta kara gyara zama tana kisimma abubuwan kissa da makirci da zatayi a gidan....

    Misalin karfe uku na rana maryam kawar shukra tayi mata sallama zata tafi gida "kai maryam na dauka yini zaki mana"

  "kiyi hakuri besty zan dawo saboda ummah na batanan ni zanyi mana abincin dare, sanan ina kara tuna miki gobe munada class karfe takwas na safe kifito da wuri kinsan halin malamin"

  "insha allah kawata"....shukra ta mike suka fita da maryam don tayi mata rakiya, dik hirar da sukeyi sadiya na tsaye jikin windownta tana kallonsu....

   Bayan shukra ta raka maryam allah allah takeyi ta shiga dakin mama saboda magana dake cinta suyi, kujera ta zauna ta sassauta murya tace "mama kinga matar nan mai abun mamaki ta fita ta dawo ta saki fuska da fira kamar ba ita bace jiya ta ciwa yayanmu mutunci akanki? Yau kuma da safe tayi fitarta ko sallama batayi ba"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now