Na goma

1.4K 125 6
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*
  *shafi na goma*

     *KASHE*➡

Koda sadiya ta dawo batabi takan mama ba da kannen Abubakar daki ta shiga saboda Tana cikin tsananin zumudi da murnar gobe tayi bintu tazo gidan ta kawo Mata makamin yaki,

  Gab da kiran sallah Abubakar ya shigo gidan hannunsa rike da Leda na Kaya da ya canjowa sadiya gudun fitina lokacin sadiya na kofar dakinta Tana yankan salad,

  Da sallamarsa ya shigo be Lura da sadiya dake kofar dakiba hankalinsa ya maida kofar daki mama,har ya wuce ya dawo ya daga labule ya yi sallama ya shige,sadiya tsayawa tayi galala Tana kallonsa kamar ta Mike ta shakosa,

  "Mama barka da yamma ya ibadah?"

Mama cikeda faraa tace "ibadah alhamdulullahi ya kasuwar?"

  "Alhamdulullahi mama"....ya maida kallonsa ga waazin da mama ke kallo a TV.


  Sadiya kuwa minti minti take maida kallonta ga kofar dakin ko zai fito taji shiru,a zuciye ta Mike ta nufi kofar dakin babu ko sallama ta bankade labule ta shiga ledar hannun Abubakar ta fincike ta fice tace "saika taho"tayi waje abunta ko a jikinta,galala sukayi Baki bude suna kallonta cike da mamaki,shiko Abubakar kunya CE ta lullubesa ya kasa ko motsin kirki ji yakeyi tamkar kasa ta bude ya shiga,shin yaushe sadiya zatayi hankali?....yafi minti biyar a zaune kamar an dasashi sanan ya Mike jiki a sanyaye yace "mama asha ruwa lafiya"

Mama tace"Allah yasa"....ya fice ,

  Shukra ta kalli mama tace"Allah ya kawo karshen wanan matar mama,bakin cikine saboda taga Yaya yafara dawowa hankalinsa"

Murmushi mama tayi tace"tsakanin da' da mahaifi Sai Allah kullum inayi mata adduar shiriya Allah ya shiryeta"

  Shukra ta tabe Baki tace"idan me shiryuwa CE"....



  Koda ya shiga daki bece da ita komiba itama batace dashi komiba Sai wani haushinsa da takeji shi kuwa yasa Mata Ido yagani ko zatayi magana Akan abinda ta aikata?...batace komiba har akasha ruwa dare yayi kowa ya nemi wajen kwanciyarsa,juya Masa baya tayi ya kyaleta ,

  Babban burinta da tunaninta be wuce Allah ya kaimu safiya ba takosa gari ya waye Dan ta dokanta da abinda bintu tace Mata,

  Shi kuwa tunani yakeyi kala kala Akan halayen sadiya besan ranan da zata shiryuba ga wani irin sonta da yakeyi.....

******Mama kuwa kwana tayi Tana fadawa Allah damuwarta Akan surukarta Allah ya karkato Mata hankalin danta ita Kuma Allah ya shiryeta....

*******
Washe gari tunda safe Abubakar ya shirya yayi ficewarsa bayan ya Bata kudin cefane yanayi Mata magana Tana kyaleshi.....

  Karfe Sha dayan Rana bintu ta diro gidan,tun daga kofar shigowa gidan take shewa "assalamualaikum masu gida kawata sadiya don gida nakine komi dadewa Sai gida ya Zama naki ranan da Kika haife abinda ke cikinki Dole ya gaji ubansa"

  A guje sadiya ta fito daki ta amsa "barka da zuwa kawata masoyiyata nakosa kizo inji Dadi Dan kece kawai Zaki kawomin karshen wanan ciwo dake damuna a zuciya"

  "A hayye aibazaki taba daina ciwon zuciyaba matukar kina zaune da ulcer,kina tare da ciwo "

  Dik maganganun da sukeyi mama na daki Tana jinsu shukra na makaranta balle ta tanka,

Kujerar tsakar gida sadiya ta fito dashi suka zazzauna suka cigaba da zazzaga rashin kunya ,

Bintu tace cikin daga murya"Wai nikam sadiya ya kike Zama da ulcer ne?"

"Ai kawata bazaki ganeba wanan munafukar tsohuwar ta kanainaye komi konaja raayin danta saita shiga ta fita taje wajen malaminta ya dawo Mata dashi,yau ma saboda uwarsa tun safe yabar gidan Nan ko sallama babu"

  "Kada kiga laifinsa sadiya laifin asirine ai dik Wanda zai zauna da uwar miji Sai yayi hakuri"

  

   Tunda Abubakar ya doso hanyar shiga gidan ya farajin hayaniya don Yana tsayawa da mashin bintu na shigowa Sai ya nemi bayan kofa ya tsaya Yana sauraron dibar albarkar da akewa uwarsa,ya tsaya yaji karshensu Amma jikinsa rawa yakeyi ya kasa jurewa a guje ya fada gidan...

  Sadiya na ganinsa ta Mike tsaye da sauri,

  Kallon tsana yake jifanta dashi cikin daga murya ya Soma magana,sadiya dama dibar albarkar da kikeyiwa mahaifiyata kenan?sadiya Ashe bakida tarbiyya bakida mutunci?"

  "Wallahi Abu...ba...

Ya daga hannu ya wanketa da kyakkyawan Mari tasa hannu ta Dafe wajen ya Kara Mata wani yace "me zakicemun muna fuka?bakida sauran kalmar da zakiyi Amfani da ita yaudararki ta Kare a wajena munafukar banza muna fukar wofi na sakeki saki daya,Kuma ki tattara naki ya naki kibarmun gida"

  Ya waiga ya kalli bintu da jikinta ke rawa Tana rabe a bango yayi kanta ta runtuma a kuje tayi hanyar kofar gida aikuwa ta xame a sumunti ai a guje ta Mike ta fice da gudu a zaure ta hankade shukra da tayi mantuwa ta dawo,

  Batayi mamakiba ganin abinda ke faruwa farin cikine ya lullubeta na adduarsu da Allah ya karba....

  Watso kayan sadiya Abubakar keyi mama ta fito tace "kul da watso Mata Kaya Abubakar ka barta ta dibi abinta da kanta babu kyau namiji ya saki mace Kuma ya watso Mata Kaya kaji?Sai Allah ya kamaka"

  Dukar da Kai kawai yayi ya fice a gidan gaba daya ita kuwa tanata rusa kuka Mai cike da danasanin abinda ta aikata....hakanan ta tattara kayanta tayi gida.

*******
"Sadiya kome Abubakar yayi ke kika jawo ke Kika siya da kudinki sonkai da son zuciya irin naki yaja Miki kina zaune da surukarki Mai kirki da hakuri Kika kasa iya zama da ita Kika tsuro da halaye marasa kyau Wanda Ni bani kikaga inayiba ba ninasakiba gashinan yanzun kina danasani Mara anfani yanzun Kinga idan kikayi wani auren sai ki koyi Zama da surukarki,ba lallai bane Allah ya Kara hadaki da suruka ta gari *rashin iya zama da suruka* ya jaki da aikata son zuciya da danasani Mara anfani yanzun saimu zauna a gidan kici uwar da zakici"

"Wallahi....

Yayantane yakai Mata duka yace "wallahi me?ai babu abinda Zaki fada Mana mu yarda kawarkiba?takaiki ta baro saiki zauna abinda mukaci kici Kinga wanan ya zame Miki darasi a gaba yadda idan kikasamu wata surukar Zaki riketa hannu biyu biyu ku zauna lafiya wannan batada hakkinkine asirinki ya tonu"

  Sadiya ta Dora hannu akai Tana famar rusa kuka kamar ranta zai fita ,

  Mamanta kuwa shigewa daki tayi tabarta Nan Tana faman kuka Babu me lallashinta,Sai danasani Mara anfani......

*******
GA DAI YADDA KARSHEN SADIYA YA ZAMA ,GAREKU MATA MASU IRIN HALINTA KUKAN KURCIYA JAWABI NE AKACE MAI HANKALI KE GANEWA ALLAH YA BAMU IKON AIKATA ALHERI.....




*SLIMZY CE✍🏻*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now