Babi Na 15-Aysher d'ansabo

2.6K 163 8
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Al-k'aluman* *Marubuta*

KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert _and_ perfect writer's_ )

*BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

*KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN* ....

_Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo* *lemu* 🖊

0⃣1⃣

Zaune take bisa katifar d'akinsu wanda yake mallakinsu ne su biyu, itada yayarta ta zabga uban tagumi kai kace anturo mata da sakon mutuwace, ahankali kuma wasu zafafan hawaye suka shiga kaikawo a fuskan nata .

Sallama akayi abakin kofar d'akin nasu , hakan yasa matashiyar budurwan tai saurin mik'ewa tana share hawayen fuskanta , jin muryan qawarta zee ce ke doka sallaman , cikin hanzari tanufeta tana mai k'ak'alo murmushi bisa kyakykyawar fuskan tata tana fad'in
"Oyoyo zee saukar yaushe agari babu ko lbry. "

Ta karisa mgn tana rungume zainab wacce itama murmushi d'auke afuskar tata, zee bata samun daman mgn ba har suka karisa bakin katifar suka zauna.

Kafin ta dubi k'awar tata tana fadin
"Wlh jiya da yamma nadawo Ruky, kinko ga yadda kullum kike sake kyau, jikin ki nawani glowing tamakar sabuwar amarya. "

Takare mgn tana dariya k'asa-k'asa yayin da Ruk'ayyah ta tab'e baki , fuskan ta na nuna tsananin damuwan da zuciyanta ke ciki kwanakin nan,ahankali cikin sanyin muryarta me dad'in amo take fad'in

"Bazaki gane ba Zainab Zubairu , dakinsan halin damuwan danake ciki ayanzu dakin tausayamin. "

Hawayen da Zee Zubair taga Ruky nayi ne yasa jikinta yin sanyi , cikin nuna kulawa take tambayar k'awar tata

"Meke faruwane Ruky haka ? "

Wasu hawayen ne suka k'arisa biyo fuskan Ruky tana cewa
"Zainab Za'a rabani da masoyina Ahmad , bansan aibunsa ba zee bansan miye laifinsa don kawai yafito daga gdn talakawa , alhali Allah yabashi rufin asiry dai-dai gwargwado. "

Takare mgn tana sakin kukan daya taho mata , sosai zuciyanta ke zafi tanajin matuk'ar tausayin halinda zata shiga idn aka rabata da masoyinta , wanda takejin so da k'aunarsa har cikin jinin jikinta .

Sosai mgn Ruky ya girgiza Zee Zubairu, domin ko itad'in shaidace akan irin son da Ruk'ayya Turaki da Ahmad sukewa juna ,
Kuma itama bata tab'a ganin aibun Ahmad ko rashin dacewan su da k'awar tataba , domin Ahmad natsatstsan saurayine me riko da addini da sanin yakamata.

Kafad'an Ruky ta dafa tana sake kwantar da murya alamun nuna rarrashin kafin tafara fad'in

"Calm down Turaki babu me rabaki da Ahmad insha Allah , domin ko kun dace da juna kuma Ahmad bashida wata aibu da za'a kafa HUJJA dashi wajen raba tsaftatacciyar soyayyan da kuka ginata tsayin shekaru uku. "

Ahankali Ruky take rage sautin kukan datake , sai dai har lokacin zuciyan ta k'una take cikin raunin murya tadubi Zee din tana fad'in

"Zee kenan wlh umma da Abba da gske suke nuna k'in amincewan su da aurena da Ahmad , Nadiya ce kawai da sauran 'yan uwan Abba suke nuna amincewan su , Zee KWAD'AYIN IYAYENA ne kawai zaisa suce lallai saina aury Kamal Alqasim , sbd kawai yana yaron attajirai shikuma Ahmad ya fito daga gdn talakawa , wlh Zee idn ban aury Ahmad ba mutuwa zanyi , sam natsani Kamal tsana me tsanani kisanar dani yazanyi? su Abba sugane bazan iya rayuwa dawani namiji ba sai Ahmad. "

Takare mgn wasu hawaye masu zafi nasake zirarowa daga fuskan ta , sosai jikin Zainab Zubair yai sanyi , tanajin tausayin Ruky nasake kamata sbd batin yau tariga tagano halin iyayen k'awarta masu kwadayi bane , cikin sanyin jiki take sake rarrashin Ruk'ayya tana fad'in

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now