Shafi na hudu

1.6K 143 1
                                    

*KUNDIN HASKE:-*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

*K'UNGIYAR:-*
  *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*💡
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
*Zaynab bawa (Zeeyybawa)*
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA HUD'U*

  Tunda umma ta shiga gida take sak'e-sak'e akan abubuwanda suka gudana yanzu tsakaninta da malam yahya,

  Bata boyewa humaira ba ta shaida mata komai, sosai humaira ta nuna farin cikinta akan wananan al'amari ta goyi bayan mahaifiyarta tayi aure kodan kare daraja da martabarsu,

  Umma ta fara jin hankalinta yafara kwanciya da wannan al'amarin domin taga yarinyarta tayi na'am sosai, abu d'aya zata jira shine tasanarda manyanta suma tajina bakinsu,

Duban humaira tayi tace" humaira d'aukomin tuwo kizubamin miya,

Dasauri humaira tamiqe tanufi kitchen a plate dasakowa umma tuwo had'eda miya,

Wanke hannu umma tayi, sanann tayi bismillah tahaucin tuwon,

Sai bayan tagama tayi hamdala ta wanke hannunta sannan ta dubi humaira tace" humaira dama
Mlm yahuza dayazo yau ya sanar dake wani abunne?"

Gydakai humaira tayi tace" eh umma yafad'a mun cewa zai rabu dani, amma bason ransa bane,

Meyasa baki fad'a munba humaira?"

Umma banaso hankalinki yatashine shiyasa, bbu wani hankali dazan d'aga humaira komai kikaga yafaru da mutum wannan rayuwar mukaddarine daga ubangiji,

Allah yaza6a miki mafi alkairi saiki cigaba da addu'a,

A rayuwar nan komai zaka nema ka nemi alkairinsa yafi,

Hakane umma nima addu'arda nakeyi kenan,

Allah yayi miki albarka yaci gabada kareki daga sharrin kowacce irin halitta,

Zankuma qara fad'a miki bawai don kinrasa saurayi d'aya saiki ballaga zantarda kankiba, kokum kid'auki wata dabi'arda batakiba, kina zaunenki akamile Allah zai aiko miki saurayi mai cikeda kamala,
Allah yana sane dake baikuma manta dakeba,
Allah shine mahukunci akan bawansa,

In sha Allah umma zan qara kokari dakuma qaimi wajan ganin nariqe mutumcina,

Toh Allah yayi miki albarka, maza mikomin ruwa na kuskure baki nayi sallan shafa'i wutirin idanna tashi sallan dare sai nayi,

Umma kitasheni dan Allah nima inaso nayi koyida halayenki inaso naringa sallaahn dare, (qiyamul lail) sannan kuma inason naringa yin Walha da hantsi,

Sai ki dage aii humaira, kina zaune halirarki zaki tashiki gyara,

Duk wanda aduniyarnan kika ganshi yanada damuwa amma baitashi yayi qiyamul lail ba gaskiya wannan damuwa bata can-can ci a kirata damuba,

Idan kanada damuwa hana idanuwa bacci akeyi kazauna gaban uban gijinka da daddare kahana idanuwanki bacci,

Kai kobaki da damuwa yakamata kikasance mai tashi cikin dare kina mai kusan tuwada ubangijinki,

Allah shine kad'ai mai yaye miki damuwa, idan kikaga kinyi addu'a kina ganin kamar bata kar6uba wannan kuskurene, bbu wani mumini dazai zauna gaban ubangijinsa yad'aga hannu yaroqeshi bai amsa masa buqatar saba batareda yasauke hannuwansaba,

Ita add'ua kowacce kar6a66iyace takanyi jinkirine wani lokacin,  wani lokacin kuma ubangijinmu wanda ya haliccemu yafimuson kanmu da fiyeda yanda mukeson kanmu, yafimu sanin kanmu, saiya canja mana da abunda yaga yafi zaman mana alkairi,

Humaira yakamata kidage yanda y'ay'anki zasu tashi suyi koyida kyawawan halayyarki, kisani uwa itace 99% na tarbiyar yaronta wannan 1% shine aka barwa mahaifi,

Kekuma bakida mahaifi watakila kin rasa wannan 1% d'inne hartakaiga kin aurenki matsayin na wacce y'a mace ta raina kuma tabawa tarbiya,

Ankasa duba wannan 99% na tarbiya wacce kike da ita daga wajan uwa,

Humaira zanyi aure kodan farantawa rayuwarki, zanyi aure domin yazama bautar ubangiji, zanyi aure domin son samun rahamar ubangiji,

Gobe zan shiga wajansu baffana zan sanar dasu naji cewarsu,

Miqewa tayi tashige d'akk ta shimfid'a sallaya tahu yin sallah."

Mlm yahya kuwa yagama yin na'am da umma dakuma halayanta domin yanzu d'an tattaunawarda sukayi ya fahimci wasu daga cikin halayenta."

GIDANSU SUWAIBA."

Kamar kullum yanda tasaba tad'auki tallanta takai sako da lungu bayan tafito wani d'an tsohone wanda zaikai 60yrs yana zaune gefe sigari yake sha daga ganinsa ba tsohon kirki bane,

Me talla yakwala mata kira Na'am ta amsa da sauri hartana cin tuntu6e ta isa gareshi, mekike talla?"
Ya tambayeta

Amarauce tafad'a tana washe baki, ajiyarmun ta yobe anan jiki yana rawa tad'auki gyadar  hamsin ta ajiye masa yawwa, hungo wannan dari biyu ya miqa mata,

Laaah aikuwa banida canji bari naje yanzu na nemo, A'a barshi kawai y'an mata jeki dashi, duka?" tafad'a cikin al'ajabi

eh duka nakine,
Gobema kidawo  anan zaki sameni iwar haka zansiya ok ngd sosai tafad'a tana tsalle,

Ai babu komai saikin dawo goben, toh Allah yakaimu tafad'i tana qulle kud'in qasan zaninta,

Saida tasiyarda tallan duka kafinnan ta nufi hanyar gida, kota taje bata nunawa mamarta anbata kud'inba ta noqeshi,

Washe garima haka taje tasameshi yabata 200 a haka tasamu wajan zuwa kullum saitaje shikuma dai-dai dana rana d'aya bai ta6a missing wajan bata kudinba."

Ummma tasamu y'an uwanta ta sanardasu zancen ta da malm yahya, kowa yaji wannan zancen sai yayi mata murna domin m yahya babban malmine wanda yacikada ilimn addini,

Yanada abun hannunsa domin d'an kasuwane sosai,

Duk wajan wanda take ta babu wanda baiyi na'am da zancenba, har qannen babansu humaira ta sanardasu, suma aunyi mata murna sosai amma sun bukaci akan tabasu humaira tadawo zama wajansu,

Domin basusan shid'in kozai yarda yakar6i diyarba kokuma akasin haka, sudai bazasu bar d'iyarsu ta wulakantaba, domin tun farko sunso kar6anta  ita umma ce taqi basu ita."

Takira waya tasanarda yaranta cewa suzo tana nemansu,

Aranar duka suka hallara cikin gidan, takai wata 1 bata sanyasu a idanuwantaba, duk da kasancewar suna gari d'aya,

Tafad'a musu abunda ya sanyata kiransu,

Tashi d'aya suka tada rikici akansu mahaifiyarsu baza tayi aurena saidai tazauna ahaka,

Idan wani abunne take buqata su zasuna mata zasuna siya mata sabulai abinci daduk wani abunda take buqata amma basu yarda tayi wani aurenba,

Batarai sosai umma tayi tana fad'in aure bbu fashi kuma bbu mai hanani cikinku, bankuma haifeku domin kusaya min sabuluba, tunda baya bakusanda basuluba sai ynzu, kada naji kada nagani nice na haifeku bakune kuka haifeniba, aure kuma bbu fashi don haka kutashi kubani, waje,

Jiki asanyaye suka miqe suka fice daga gidan,
( wannan babban kuskurene da yara muke aikatawa yanzu domin iyayenmu maza sun rasu sai muce wai bazamubar iyayenmu mata suqara yin wani auranba, haba wannan da al'ada bace bakuma addini bane, aure bautace ta ubangijinmu bakuma haramun bane don mahifinmu yarasu munbar  mahaifanmu mata sunqara yin wani aure, ba abun fad'uwa bane sannan kuma ba'abun kunya bane, bautar uabgijine fad'in Allah ne da manzonsa, sunnar Annabi muhammad S A W, danme bazamubar mahaifansu sucika sunnar Allah da manzonsaba?"
Wasu iyayen kuma sunada babban laipy sune masu biyewa yaran, kamata yayi kinuna 6acin ranki sannan kima kigwada musu ko yaya zasuyi saikinyi auranki)

Washe gari, mlm yahya jira yakeyi kawai lokaci yayi yazo yaji amsa daga bakin umma, aikuwa lokaci yanayi ya shirya ya nufi gidan domin jin amsarsa."

To be continued

Urs zaynab Alabura

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now