19

2K 225 32
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


19


Hawaye kawai take, ya sassauta rikon da yyi mata a hankli yace "To na kyaleki...." daga haka ya saketa gaba daya ya tashi, kofa ya nufa ya fita ta boye fuskarta kan gado tana kuka a hankali, Ba a dau lkci ba ya dawo dakin rike da plate din gasasshen kaza da madara me sanyi, ajiyewa yyi nan kan lallausan rug din dakin, yana kallon ta yace "Come down" daure fuska tayi ta mak'e kafada tana goge hawayen idonta, tashi yayi tana ganin haka ta bar inda take da sauri, ya bi ta bata ankara ba sai gani tayi ya dauketa, ta xaro ido tace "Wayyo ka bari plss" bai direta ko ina ba sai kasan rug din ta takure gu daya ta jingina da gado, duk yanda yyi da ita ta ci naman kin ci tayi, tsayawa kallonta yyi, ta wani kauda kai, d'an murmushi yyi ya bude drink din ya xuba a cup ya kai baki ya kurbi kadan ya jawota lkci daya ya hade bakinsu, duk mutsu mutsun ta bai kyaleta ba sai da ya tabbatar ya juye mata madaran gaba daya a baki ta hadiye, lumshe ido yayi ya fara kissing dinta, lkci daya kuma ya janye bakinsa, a rikice ta fara kokarin mikewa ya kamata ya dau drink din ya bata yace "Gashi idan ba haka ba in kara...." Da sauri ta karba, ya wara manyan idanuwansa yana kallonta, sai da ya tabbatar ta sha me yawa sannan ya bari ta ajiye drink din, ya dau nama ya mika mata, goge hawayen da ya sakko mata tayi ta karbi naman hannunta na rawa, kadan ta ci ta marairaice masa tace "Na koshi wllh" bai ce komai ba ya nuna mata plate ta ajiye sannan ya dau naman da drink din ya fita, Sai a snn ta tashi a sanyaye tana goge bakinta don har lkcn ji take kamar bakinsa na nata, abinda ba a taba mata ba duk tsawon rayuwarta, Bathroom ta shiga ta wanke baki da mouthwash dake nan ko xata daina jin abinda take ji, tana son yin wanka amma tana tunanin kayan da xata sa, haka nan dai ta yi wankan daga karshe ta maida kayan jikinta ta fito, xaune ta gansa gefen gado da laptop, ya bi ta da ido har ta iso kan rug kamar munafuka ta xauna tana satan kallonsa, sae da ya ga xata kwanta a kai yace "Nan xa mu kwanta?" bata tanka sa ba banda mugun faduwar da gabanta yyi, yace "Ohk then" kashe laptop dinsa yyi ya mike ya kashe wutan dakin ya dawo kan rug din shi ma, tashi tayi da sauri ya rikota, a rikice tace "Na shiga uku don Allah ka bari ina rokonka" d'aga ta yyi ya kwantar kan gado ya kwanta kusa da ita ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Amma ba da heavy wears din nn xaki yi bacci ba" bai jira tace komai ba ya xuge zip din rigarta ta xaro ido a rude, bata kai ga cewa komai ba ya cire rigar ya ajiye, sannan ya cire skirt din ya barta daga ita sai inner wears, nonnokewa ta dinga yi jikinta na rawa take cewa "Don Allah Don annabi ka rufa min asiri" ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa ya lumshe ido yana shakar da'dd'adan kamshin dake tashi a gashinta murya can kasa yace "Sleep" kasa baccin tayi tsabar tsoro ga kamshinsa da ya cikata, sai bayan kusan minti talatin baccin ya dauketa. Ji tayi ana jan hancinta ta bude ido a hankali ta gansa xaune gefenta ya wara mata ido yace "Tashi lkcn sllh yyi" daga haka ya mike ya fita dakin wanda da alama masallaci xa shi, tashi tayi xaune tana kare ma dakin kallo, ita dai tasan wannan furnitures din ba lallai wanda aka yi mata bane a gida, a hankali ta yaye bargon jikinta ta sauka kan gadon ta duba inda kayanta yake ta dau xani ta daura ta shiga bathroom, wanke baki tayi, tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh ya shigo dakin, xaunawa yyi gefen gado idanuwansa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, satan kallonsa tayi dai dai lkcn da ya juyo suka hada ido, tayi saurin dauke kanta, tashi yyi ya dawo kusa da ita ya xauna kan darduman, xata koma baya ya riketa yana kallon kwayar idonta murya can kasa yace "Good morning wife?" Turo baki tay taki cewa komai, ya lumshe ido yace "How was ur nyt?" nan ma ba ta ce komai ba, ya matsa hannunta, yar kara tayi ta bata fuska kamar xata yi kuka yace "Answer me now" kamar xata yi kuka tace "Ina kwana" yyi mata wani sanyayyen murmushi a hankali yace "Lafiya lau baby" tashi yyi ya dago ta suka koma kan gado, ya kwanta ya jawota jikinsa ya lumshe ido, bata yi resisting hakan ba, bayan kusan minti goma ta dago kai a hankali tana kallonsa, bacci taga yake, ta tsura ma long lashes dinsa ido, a hankali ta sauke idanuwanta xuwa kan dogon hancinsa snn lips nasa, haka kawai gabanta ya fadi, ta mayar da dubanta kan lallausan bakin gashin kansa dake ta sheki, komai nasa is just different, a hankali ta xame jikinta ta koma can karshen gadon tayi lamo. Ba karamin tsorata tayi ba jin an rungumota ba lkci daya kuma ya juyota suna facing juna, ta xaro ido tana kallonsa, har lkcn idonsa a lumshe suke bata dai ce komai ba kuma bata janye jikinta ba bata kuma san sanda bacci ya dauketa a haka ba. Danna bell da aka yi ya farka da ita wajajen karfe takwas, ita kadai ce kwance kan gadon ta mike ta shiga bathroom ta wanke bakinta, har xata fito kawai tayi deciding ta sake wanka, bata wani bata lkci ba ta fito daure da sabon towel din da ta gani bathroom din, da sauri ta karasa kofa xata rufe da key taji an bude, dukawa tayi a tsorace tace "Wayyo shiryawa xan yi" ya wara ido shima ya duka gabanta yace "Wayyo ban hana ki ba ai" kin dago kanta tayi, lkci daya ya daga ta ta xaro ido kamar xata yi kuka tace "Don Allah ka rufa min asiri plss" yace "To na rufa maki, shirya ki same ni a parlor yanxu" daga haka ya juya ta bi sa da ido gabanta na faduwa har ya fita ya kulle kofar, daya daga mayukan dake gaban mirror ta shafa tayi amfani da turarurrukan dake nan ma sannan ta fiddo wani riga da skirt da aka dinka mata kafin biki ta saka ta dau Hijab ta sa a kai taje can karshen gado ta xauna, bude kofar dakin aka yi ya shigo ya rungume hannayensa yace "I know.... get that Hijab off now" ta mak'e kafada ta hade rai tace "Noo" wani kara tayi ta sauka gadon ganin ya nufo ta, bai kyaleta ba sai da ya cire Hijab din ya na rike da hannunta suka fita, Abinci ne tsakiyar parlon tun daga kan wainar shinkafa da miyar taushe, pepper soup na kayan ciki, ruwan Lipton da yaji kayan kamshi, fried potato da egg and plantain, sannan ga bread, ko wanne kuma bbu yawa, tun tana noke masa tana kin cin abincin har ta sake ta ci dankali da kwan saboda takurata da yyi, shi bai wani ci komai ba a gun banda ruwan lipton da pepper soup din, daga karshe ya kwashe duk abincin yayi hanyar kitchen da su ta bi sa da ido, a hankali ta mike ta dau sauran ta bi bayansa, ya karba bakin kitchen din yace "Noo ba sai kin ba kanki wahala ba baby" daga haka ya ja ta suka komo parlor yace "Xa mu je can gida ki gaida mum dita, don haka ki je ki canxa kayan nan yanxu" turo baki tayi bata ce komai ba ya ja bakin sannan ya kuma janta xuwa dakinta, da kansa ya fiddo mata da kayan da xata sa, bata yarda ta shirya ba sai da ya bar dakin, ba laifi ta dan shafa powder ta sa wet lip kan pink  lips nata sannan ta sa Eye pencil, bbu yanda bai yi da ita kan ta sa gyale ba taki dole ya bar ta da Hijab dinta har kasa, shadda ce fara jikinsa banda satan kallonsa bbu abinda take ita kanta bata san me yasa take kallonsa a sace ba har suka shiga mota suka bar gidan, Tarba mai kyau mahaifiyarsa da kanninsa mata biyu suka mata, irin tarban da ba ta taba xato ba, his mum is more than kind, a nan kuma ta gano asalin inda Elbasheer ya samo kyansa don mahaifiyarsa kyakkyawar bafillatanar literate ce, kusan duk kawayen mum din tasa da yan uwanta gaba daya gidan suka xo ganin fatima, duk ta rasa inda xata sa kanta don kunya, mahaifiyar tasa na lura a takure take a parlorn tasa autar ta Seeyama ta kai ta bedroom dinta, shi dama tuni ya bar gidan, a yanda kuma fatima ta lura shima yana da kunya sosai don bai yrda sun hada ido da kowa a gidan ba sai wani sinne kai yake har ya tafi, kusan karamin walima aka yi a gidan don ko ina na gidan cike yake da jama'ah, haka cousins dinsa suka dinga shigowa dakin Hajiya Aisha ganin Fatima, ita dai duk jikinta yyi sanyi don tasan kilan basu san daga wani irin gida ta fito bne shi yasa suke mata fara'a haka, suna gidan har dare, kuma Mumy ce ta tsayar dasu domin  fatima ta gaida Abban Elbasheer, Abban nasa na dawowa kuwa mum ta kira Elbasheer din ya dawo gidan, xuwa lkcn kuma duk an watse sai yan uwa na jiki da suka rage, Har parlorn Abban Mum tayi ma fatima iso, Elbasheer na biye da su a baya, fatima ta durkusa kanta a kasa ta gaishe da dogon dattijon bafillatanin dake xaune parlorn cikin sanyin muryarta, ya cire glasses din idonsa ya amsa da fara'a yana mata sannu da xuwa, Elbasheer dai na xaune d'an nesa da su bai kuma yarda ya dago kai bare ya hada ido da iyayen nasa ba, nasiha sosai Abban nasa yyi masu daga shi har ita, daga karshe mum ta daura nata ita ma, duk yanda fatima ta so k'in yarda kwalla ya xubo mata hakan bai yiwu ba, Abba ya mike ya dauko sabon darduma da al-qur'an ya ba mum ta bata, mum ta mika mata, fatima ta karba hannu biyu a hankali tace "Nagode Abba Allah ya kara girma" yace "Ameen, Allah ya sanya albarka ya kauda fitina tsakaninku" kasa cewa komai tayi tana goge idonta, mum ta daga ta, tayi ma Abban sai da safe sannan suka fita, sai a snn Elbasheer ya mike yyi masa sai da safe shi ma sannan ya bi bayansu, har mota mum da kanuwarta da kannin Elbasheer suka rakasu, hawaye kawai fatima take taji kamar kar su bar gidan, bata taba xaton xa su karbeta haka ba a gidan, Elbasheer yyi ma small mum dinsa da mumy sai da safe ya daga ma sisters dinsa hannu sannan ya ja motar suka bar gidan, sun yi nisa sosai ganin kuka take a hankali, yyi murmushi yace "Uhn, to ko in mayar da ke ne gidan?" Ta kallesa muryarta na rawa tace "Ehh" dariya yyi yace "Toh sai ki samu ciki da wuri in mayar dake can har ki haihu" wani kallo tayi masa ta kauda kai, yace "Yeah" suna isa gida ruwan wanka ya fara hada mata a bathroom dinta, sau daya yyi mata magana ta mike a sanyaye ta shiga bathroom din, a can ta cire kayanta snn tayi wanka, ko da ta fito baya dakin, ta fiddo dogon kayan baccinta ta sa sannan ta shige duvet bbu bata lkci kuma bacci ya dauketa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now